Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Wajibi Ne Mace Ta Tayar Da Iƙama Idan Za Ta Yi Sallah?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum warahamatullahi. Malam mace za ta yi sallah toh sai aka ce ba lallai ba ne sai ta ta da iƙama kawai Allahu akbar zatace sai tafara karatun sallah? Wai shin wannan ya halatta ko dole sai ta ta da wannan iƙama?

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

وعليكم السلام ورحمة الله.

ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ،

Anyi tambaya ga kwamitin bada fatawa na kasar Saudiyyah cewa shin an wajabta ma mace a shari'ah ta yi iƙaamah idan tana jagorantar wasu mata a sallah? Sai suka amsa da cewa: ba a wajabtawa mata yin iƙaamah ba a sallah ko da mace na sallah ita kaɗai ko mace daya tana jagorancin wasu mata a jam'i, kamar yadda ba a shar'anta musu yin kiran sallah ba. (Fataawa al-Lajnah al-Daa’imah, 6/84).

An tambayi Shaykh Ibn Baaz (rahimahullah) cewa "Shin ya halatta ga mace ta yi Kiran sallah da Iƙaamah a sallah ko bai halatta ba??" Sai Shaykh ya amsa cewa: ba a shar'anta Wa mata yin kiran sallah ko Iƙaamah ba, amma wannan ga maza ne. Da kiran sallah da Iƙaamah babu dayansu da aka shar'anta ga mata, Kawai za su yi sallarsu ne babu kiran sallah babu iƙaamah. (Majmu'ul Fataawa wa Maƙaalaat Mutanawwi’ah, 10/356)

والله أعلم،

 

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBƙfaiPwf28l

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments