Wani lokacin idan na tina yarinta sai na yi ta dariya🤣
Na Tina ranar da na fara zuwa zance, tin daga sanyi safiya na wanke wata shadda ta na sanya Mata sitati, na wuni Ina goge ta da dutsin guga.😅
Akwai wani ta kalmi sau ciki Mai Kama da kwale kwale, na dauko shi Akwai wani Mai wankin takalmi ya wanke man shi tass🌻
Hula ta kuwa na dade da karbo ta daga wajan wanki.
A ranar wuni na yi Ina shirya Kai na,kai ka rantse da Allah cewa wajan shugaban kasa za ni ko kuma wajan wani Attajiri🙈
Tin da nagama sallar magariba na shira, na dauko shaddar Nan da na wuni Ina gogewa tana she ƙi,😍 na ɗauko hula da takalmi na na kifa🙈
Na nufi gidan su yarinyar da yake lokacin bani da waya 😥 tin akan hanya na dauki hayar wani yaro da zai kiraman ita muka tafi tare da shi😎
Muna Isa kofar gidan su yarinyar na ji gabana ya soma faduwa 😳 yaron ya Shiga domin ya kirawo ta, na tsaya ƙikam a kofar gidan kamar tabarya ko motsin kirki bana iya Don kada Karin guga ta ya karye 🙈
Zuwa can sai ga yaron ya dawo inda nake, yaceman Wai gata Nan zuwa, Nan take na ji wani gumi ya karyoman🥶 kan kace kwabo gumi ya wanke man fuska,🙆 koya na ɗan ji motsi sai inji bugun zuciya na ya karo, zuwa can na ji an danno kofa🙆😳
Yarinyar ta fito ta nufo wajan da nake tsaye , duk tako daya idan tayi da nufin isowa wajena, sai na ji bugun zuciya ta ƙaruwa yake😥 A karon farko kenan Dana fara zuwa zance na ji kamar na she ƙa da gudu🙈🤣
Yarinyar ta ƙaraso ta dubeni, ta ce sannu ,Kaine kake kirana?
Saboda tsabar ruɗewa na ce Mata ba ni ba ne 🙈🙆🙄🚶
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.