Ticker

6/recent/ticker-posts

Ibadun Da Mai Haila za ta Iya Yi Awatan Ramadan

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamou Alaikum wa Rahmatullah! Malam Allah ya kara ilimi mai amfani! shin Malam wanne irin ibadu ne ya kamata mace dake haila ta yi a cikinikin Ramadan ganin ita ba ta azumi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salámu. Kasancewar an hana masu haila yin Sallah da azumi bai dace hakan yasa su zama kasalallu a wannan wata mai alfarma na Ramadan ba. Saboda wannan ba wata ne na wasa da kasala a ibadoji ba. Mata masu haila ba a haramta masu yin zikirin Allah ba, yana da kyau su dage da yin takbiri, da tasbihi, da tahmidi, da tahlili, da istigfari, da sauran duk zikirorin Allah.

Suna da damar sauraron karatun Alƙur'ani, da sauran ilmomi na addini. Amma a game da su karanta Alƙur'ani da kansu kuwa malamai sun yi saɓani, daga cikin malamai akwai masu fahimtar hana mai haila karanta Alƙur'ani, amma a fahimta ta biyu kuma suna da damar karanta Alƙur'ani da ka, ba tare da taɓa Almus'haf ba, wannan fahimtar ta fi zama daidai.

 

Harwayau, masu haila suna da damar yin umurni da kyakkyawa da hani da mummuna, kuma su dage wurin ciyar da masu azumi sadakar abinci gwargwadon iko, d.s.

 

Allah S.W.T ne mafi sanin daidai.

 

Jamilu Ibrahim, Zaria.

 

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa  a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/EPG7wVPlgxRFR4R9CdR8xY

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Post a Comment

0 Comments