Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wanda Ya Sha Ruwa Yana Zaton Rana Ta Faɗi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum mallam,

nine nake azumi sai gari ya yi lullumi sai na sha ruwa daga baya sai rana tahasko to ya azumina?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh.

Wannan mas'ala ce da Malamai suka yi saɓani a kai inda wasun su ke ganin cewa ramuwa ta zamo lazimci wanda haka ta faru da shi, sannan wani ɓangare na Mallamai ke da fahimtar ramako bai lazimce shi ba. Amma a gaskiya idan akwai sakaci ko gangaci toh ya zamo lazimi rama azumi, amma idan kuwa da gaske yana zaton rana ta faɗi ne, ya sha ruwa, toh babu komai a kan sa.

Mu sani hukuncin musulunci ana gina shi ne a kan yaƙini da tabbas ko kuma mafi rinjayen zato, amma ba zallan zato ba.

Toh wannan daga irin abin da ya ambata, zai rama wannan azumi duba da cewa akwai wani abu na sakaci, haka kuma shari'a bata saka lullumi a matsayin ma'auni ba na karya azumi, cewa tayi idan rana ta faɗi.

(.. ثُمَّ أَتِمُّوا۟ ٱلصِّیَامَ إِلَى ٱلَّیۡلِۚ... )

[Surah Al-Baqarah 187]

 

Dalili na gaba shi ne bai tambayi ‘yan uwan sa masu azumi ba masana lokaci kafin ya karya azumin sa.

 

Dalili na gaba a yau ana da lokutan ɓullowar rana da faɗuwar ta, har ma da na alfijir, babu abin da zai hana ya duba a masallacin su ko a wayar sa, hakan zai sa ko da rana tayi lullumi, sai ya duba lokaci, kafin ya karya azumin sa. Sannan wannan ma, ita ce ɗaya daga cikin fatawowin Amirul miminina, Umar Ɗan Khattab.

 

Dalili na gaba da yasa muka ce zai rama azumin nan, don kuwa bai gina karya azumin na sa a kan mantuwa, tilasci ko kuskure ba, ballantana duba da hakan ace babu komai a kan sa. A'a kawai rana tayi lullumi, ya sha ruwa babu hujja a cikin haka. Amma da ace ya karya azumin sa duba da ɗaya daga cikin abinda muka ambata, shi ke nan, babu wata ramuwa a kan sa

1731 - «إن الله تعالى تجاوز لي عن أمتي الخطأ والنسيان وما استكرهوا عليه» .

(صحيح) [حم هـ] عن أبي ذر [طب ك] عن ابن عباس [طب] عن ثوبان. المشكاة 6293، الإرواء: 82، الروض 404: حب، الضياء

Haka ma ko da jahilci ne ya karya azumin, toh sai ya rama saboda hadisin Annabi sallallahu alaihi wa sallama da yace, sun kashe shi, me hana su tambaya da basu sani ba

4362 - 1515  قتلوه قتلهم الله ألا سألوا إذا لم يعلموا فإنما شفاء العي السؤال؟ إنما كان يكفيه أن يتيمم.

(صحيح) [د] عن جابر. الإرواء 105، صحيح أبي داود 363

 

Amma kawai da ganin lullumi sai ka karya azumi, ma'ana da ganin ƙurji sai ka caɓa masa wuƙa? Haba.

 

WALLAHU TA'AALA A'ALAM.

 Amsawa

 Malam Aliyu Abubakar Masanawa

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Fadakarwa  a Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BpO6i5KwGBm8IcVtlhBr0j

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments