Ticker

6/recent/ticker-posts

Allah Ya Ji Ƙan Ki ‘Mai Gani Daga Zuciya’ Ta Ahmad Usman El-Nafaty

Wannan waƙa ce ta ta’aziyya da addu’ar rahama. Marubucinta shi ne Ahmad Usman El-Nafaty. Ya rubuta ta ranar 10/3/2023.

 

Ɗazu-ɗazu Haleema ta ambata,

Rasuwar da ta girgiza zuciya!

 

Rasuwar da ta sa aka firgice,

Da hawaye har a idaniya.

 

Rasuwar 'yar baiwar zamani,

Ko ko ma in ce zinariya.

 

Wanga suna babba yake garan,

Don ko suna ne na mahaifiya.

 

Wagga 'ya ita ce dai Aisha,

Wacce ba ta gani da idaniya!

 

Duk da ba ta gani da idaniya,

To ganinta yana daga zuciya.

 

Don ko ta iya ƙur'ani ƙwarai,

Rangaɗau maɗaɗau gangariya.

 

Ta mace sanadin aikin ido,

Jumu'ar yau; ɗazu da safiya.

 

Wanda duk ya mace ran jumu'a,

Ba alamar zai shiga hawiya.

 

Na fahimci hakan daga Annabi,

Shugaban dukkan mai gaskiya.

 

Dukkanin zunubanta ka kankare,

Jalla karda ka bar ta da ko ɗaya.

 

Manya-manyan har ma ƙanƙana,

Kankare su ka yo mata yafiya.

 

Rabbi sa ta a janna ta ɗaukaka,

Kar ka bar ta ta zamto shan wuya.

Post a Comment

0 Comments