Ticker

6/recent/ticker-posts

Abun Ba Sauƙi

  Har na tino:


Wata rana veterinary doctor ya je wurin medical doctor ba shi da lafiya. Da ma kun san akwai jayayya tsakaninsu, kowa yana ga shi ne a gaba.


Sai medical doctor ya tambayi veterinary doctor "Me ke damun ka?"


Sai vet doctor ya ce: "Ka gani ko? Da ni ne aka kawo mini dabba ba ta da lafiya, ba zan tambaye ta ba. Da basirata zan gane."


Ashe medical doctor ya shaqa. Bai ce komai ba.


Bayan ya rubuta magana, sai ya ce: "Idan bai samu sauqi ba bayan kwana uku to a yanka shi." 😅😅🤣

Abun Ba Sauƙi

Post a Comment

0 Comments