Ticker

6/recent/ticker-posts

Maltina Da Madara Peak Basa Kara Jini a Jikin Ɗan'adam - Dr. Sulaiman Gwade

Matashin likita wato Dakta Suleiman Muhammad Gwade yace! dayawa za kaga a kasar hausa a lokacin da aka tabbatar da mutum yana karancin jini, ko tana dauke da juna biyu ko ta Haihu ta zubar da jini dayawa sai kaji ance a bashi maltina da peak milk, a fahimtar mutanen mu zai kara jini. 

Gaskiyar magana babu alaka tsakanin karin jini da Maltina da Peak milk, saboda wake kwara daya yafi Maltina da Peak milk wajen samar da sinadaran kara jini a jikin dan Adam.

Idan kun duba jikin gwamgwanin peak milk za kuga babu sidaran karin jini a ciki  ( not rich in iron) Haka Maltina ma Babu sinadaran kara jini a ciki.

Tambaya anan shine ta Ina Maltina da Peak milk yazama maganin karin jini ?

Amsa: wannan kawai al'adace ta mutanen mu ba tareda sanin abun ba.

Maltina na dauke da sinadaran:

- Calories

- Carbohydrates

- Fat 

- Vitamin

- No Iron


Peak milk na dauke da sinadaran: 

- Fat

- Carbohydrates

- Protein

- Salt

- Vitamin A and D

- No Iron


Jikin dan Adam yana samar da jini da kansa, shi jini yana bukatar sinadaran iron daga abincin da muke amfani.


Daga karshe ina bada shawara garemu kudin da muke kashe wajen Maltina da Peak milk domin kara mana jini, muyi amfani da su wajen siyen abinci masu dauke da iron kamar :


- Wake

- kifi

- Nama

- kwai 

- Kaza

- Fara

- zogole 

- Cashew

- cavage

- salat

- Spinach

- da sauran su.

ALLAH ya kara mana lafiya gabaki daya.

maltina da madara


Post a Comment

0 Comments