Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Ya Halasta A Auri Mai Shan Taɓa Sigari?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum wa Rahmatullah! Malam Allah ya kara ma tsawon rayuwa mai Albarka! Tambaya ta ita cé: shin meye hukuncin auren mutumin da ke shan Taɓa domin an cé idan zakuyi aure, ku sama ma 'ya'yanku uba na gari? Na gode Assalamou Alaikum.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam. 'yar uwa shan Taɓa sigari ba shi da kyau a addinin Musulunci, kuma laifi ne daga cikin laifuka, saboda Taɓa sigari tana cutarwa, Shari'a kuma ta haramta mutum ya cutar da kansa da gangan. Sai dai duk da haka a aƙidar Ahlussunnah Waljamá'a, zunubin shan Taɓa ba ya fitar da shi cikin Musulunci, amma kuma bai yi wa kansa adalci ba. Saboda haka ya halasta a aure shi idan ba a sami wanda ya fi shi nagarta ba.

Allah Ta'ala ne mafi sanin daidai.

Jamilu Ibrahim, Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfƙds

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments