𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum. Da farko dai ina mai neman afwa a kan tambayar da zan yi ba a kan doka ba, matsala ce ta sa muna neman amsar ne emergency that's why, da fatan za a yi min afuwa a kan hakan da kuma samun amsar tambayarmu nagode.. Tambayar ita ce shin wadda za ta yi layya za ta iya yin lalle (kunshi)? Allah ya kara wa mallam basira na gode.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salamu. Amin na gode. Babu laifin komai idan macen da ta yi nufin yin layya ta sa lalle ko ƙunshi ko ta shafa turare a jikinta, abin da aka hana mai layya shi ne kada ya aske ko ya ɗebe komai a gashin jikinsa, kada ya yanke farcensa, ko wata fata a jikinsa sai abin da ya zamo na lallura ne.
Saboda ya
tabbata daga Ummu Salmata Allah ya ƙara mata yarda cewa:
Lallai Manzon
Allah ﷺ ya ce: "Idan kuka ga jinjirin watan Zhulhijja alhalin ɗayanku ya
yi nufin yin layya, to ya kame daga cire gashinsa da faracensa".
Muslim (1977).
Saboda haka, 'yar uwa babu wani dalili tabbatacce da ya hana macen da ta yi nufin yin layya ta yi ƙunshi ko lalle ko wani abu na kwalliya. Abin da aka hana shi ne cire wani abu na halittar jiki, kamar gashi ko farce (ƙumba), ko fata, kuma wannan hukuncin ya haɗa maza da matan da suka yi nufin yin layya ne.
Sai dai a nan muna kira ga matan da suka yi nufin yin layya da su dakata da yin kitso ko tsefe kai a goman farko na watan zhulhijja, saboda kaucewa zubar da gashi da aka hana wanda ya yi nufin yin layya, domin da kamar wuya a yi kitso ko a tsefe kai a ce gashi bai zuba ba.
Allah Ta'ala ne mafi sanin daidai.
Jamilu Ibrahim, Zaria.
Zauren
Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.