Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Ina Da Laifi, Idan Na ƙi Yarda Mijina Ya Sadu Da ni A lokacin Da Nike Cikin Jinin Haila?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Idan mace tana cikin yin jinin al'ada sai mijinta ya nemi ya sadu da ita a haka amma taƙi yarda, shin ko yin hakan laifi ne a gareta kuma ta saɓawa mijinta?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Gaba ɗaya Malaman muslunci sun yi ittifaƙi a kan cewa bai halatta ba miji ya sadu da matarsa a lokacin da ta ke cikin jinin al'ada. Sun kafa hujja ne da faɗin Aʟʟāн(ﷻ) a cikin suratul baƙarat inda ya ke cewa:

"فاعتزلوا النساء في المحيض ولا تقربوهن حتي يطهرن، فإذا تطهرن فأتوهن من حيث أمركم الله"

(البقرة/الآية222)

MA'ANA:

Ku nisanci matayenku kada ku kusance su (da nufin yin jima'i da su) har sai sun yi tsarki (ɗaukewar jini) idan sukayi tsarki (wankan tsarki) to ku zo musu ta inda Allαн(ﷻ) ya umarce ku (farjinsu):

A saboda haka ko da miji ya nemi ya sadu da mace a lokacin haila to bai halatta ta bashi haɗin kai ba, domin kuwaMαnzon Allαн(ﷺ) ya ce:

لا طاعة لمخلوق في معصية الخالق

MA'ANA

Ba a yin biyayya ga wani abin halitta cikin saɓawa mahalicci.

Anan idan mace ta saɓawa miji ba ta da wani laifi, kuma lada ma Ubangiji zai ba ta. Domin dukkan irin alaƙar da ke tsakaninka da wani mutum ko da waye shi, to idan ya umarceka da saɓon Allah ba za ka yi masa biyayya ba ko da kuwa mahaifa ne, kuma inda za su ce sun tsine wa mutum to tsinuwar ba za ta yi tasiri a kansa ba sai dai ma Aʟʟāн(ﷻ) ya ƙara masa albarka. Domin haƙƙin Aʟʟāн(ﷻ) a kan bayinsa yana sama da haƙƙin duk wani ma'abocin haƙƙi daga cikin halittu.

шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ

 Mυѕтαρнα Uѕмαи

 08032531505

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/DIcJIƘrWyLP0oBOMSnDi5P

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments