Shin Gaskiyane Wai Babu Kyau Aske Gashi Ko Farce Ranar Juma'a?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Shin Gaskiyane Wai Babu Kyau Aske Gashi Ko Farce Ranar Juma'a?

    الحمد لله.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Babu Wani Abu daya tabbata daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam na iyakance wata rana cikin ranaku daba'a tsafta a cikinta, (Aske gashi ko aske ƙumba, ko gashin hammata ko yanke farce) Babu a cikin ayyukansa ko furucinsa Sallallahu Alaihi wasallam.

    Imam Hafiz Assakawy Allah yajikansa da Rahma a cikin Mauzu'u Ƙassul Azafir ya ce: " Yanda Ake yanke farce ko ayyana wata rana kebantacciya ta yanke farce bai tabbata daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ba.

    Yazo a cikin Almaƙasidul Husnah shafi na (422) duk Abun da Aka ruwaito akan haka, Hadisai na ƙirƙira da karya marasa Asali.

    Kamar yanda ibnu Hajar Rahimahullahu yafada a cikin fat-hul baari (5/359) Ya ce: Sanadan Hadisan Basu ingantaba.

    Duk wanda yakesan komawa yasamu cikakkun bayanai yakoma ya duba littafin "Talkeesul Habeer (2/170) dakuma Silsila Za'ifah na Albany hadisi mai lamba ta (1112, 1816, 3229,).

    An samo Al'adar Yanke farce kowacce juma'a daka wajan wasu daka cikin Shababbai data bi'ai.

    Baihaƙy ya ruwaito da Sanadinsa a cikin " Sunanul Kubrah (3/244) daka Nafi'u, Abdullahi bin Umar yakasance yana Yanke farcensa yana kuma rage gashin bakinsa akowacce Juma'a".

    Ibnu Abu Shaibah ya ruwaito a cikin " Al-Musannaf (3/197) daka Muhammad Bin Ibrahim Attamimy ya ce: Wanda ya yanke farcensa ranar Juma'a, yai Wankan Juma'a hakika ya cika Juma'a.

    Ibnu Hajar yaruwaito a cikin Fat-hul baary (5/359) Wanda yai wanka ranar Juma'a, yai Asuwaki ya yanke farcensa hakika yasamu cikakken ladan juma'a.)..

    Saboda Abun da Aka ruwaito daka wasu cikin sahabbai databi'ai suna yanke farce ranar Juma'a, Malaman Shafi'iyyah da Hanabila sukace: Mustahabbine yanke farce Duk ranar Juma'a.

    Imamun Nawawi Allah yajikansa ya ce: Shafi'i da Dalibansa sun nassanta Mustahabbancin yanke farce ranar juma'a, da kuma Ɗaukar hakan Amtsayin wata Alama ta Juma'a.

    Almaj-mu'u (1/340)..

    An Tambayi Imamu Ahamd ya ce: Sunnah ne yanke farce ranar Juma'a kafin zawali, da kuma ranar Alhamis, yana kuma bayar da zaɓi, Wannan shi ne Abun da yafi dacewa, Sunnah ne duk lokacinda Mutum ya buƙaci yankewa.

    Abun da Muslim ya ruwaito daka hadisin Anas Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya iyakance Mana lokaci na (Rage gashin baki, da yanke farce, da cire gashin Hammata da aske gashin ƙumba, kada Mubari yawuce kwana Arba'in )

    Ƙurduby ya ce: An Ambaci kwana arba'in ne dan iyakance Mafi tsawon lokacine, Bawai iyakancewa ne ta dole sai yakai kwana Arba'in ba. wannan baya hana Askewa ko yankewa duk Juma'a juma'a, Abun da yake abun lura a cikin haka shi ne buƙatuwa.

    Nawawi ya ce: Zaɓi shi ne dukkan waɗannan ana kulawa da Buƙata.

    Sharhin Muhazzab.

    Wannan baya hana yi kowacce juma'a, domin tsafta a cikinta Shar'antacciyace.

    Fat-Hul baari (10/346).

    Allamah Bahuty Al-Hambli rahimahullahu ya ce: Rage gashin baki ko yanke farce, ko cire gashin hammata, (Ranar juma'a, yakasance kafin sallah) wasu sukace: Ranar Alhamis, Wasu kuma Sukace: Mutum yanada Zaɓi duk lokacin da buƙata takama sai ya Aske.

    Kash-shaful Ƙina'i (1/76)

    Saboda Haka kowacce rana Ya halatta kayanke farce ko ka yi aski, ko ka yi kaciya Babu wani haramci a cikin Haka.

    WALLAHU A'ALAMU.

    Tambaya da Amsa Abisa fahimtar magabata Nakwarai.

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/BSA30hdZD7V3WSJF8WVwUj

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.