Ticker

6/recent/ticker-posts

Ladubban Yin Addu'a

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, yayana barka da dare, don Allah tambayata ita ce: a koya min yadda bawa zai yi addu'a, nagode.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salamu, Allah maɗaukakin Sarki yana son a roƙe shi, kuma yakan yi fushi da wanda ba ya roƙon shi, kuma shi ya ce ku roƙe ni zan amsa maku, kamar yadda aya ta 60 ta suratu Gáfir ta yi bayani. Addu'a tana da matsayi mai girma a addinin Musulunci, har ma ta kai ga Annabi ﷺ ya ce: Addu'a ita ce ibada". Abu Dáwud 1479, Ibn Majah 3828.

Daga cikin ladubban da bawa ya kamata ya kiyaye su domin addu'arsa ta sami saurin karɓuwa a wurin Allah sun haɗa da:

1. Mai addu'a ya zama mai kaɗaita Allah a bautarsa, ya kiyaye shirka da sauran saɓon Allah, ya zamo mai ɗa'a ga Allah.

2. Ya zamo mai tsarkake niyyarsa a addu'ar da yake yi, yana yi ne don Allah.

3. A wajen yin addu'ar ya roƙi Allah ta hanyar yin tawassuli da sunayen Allah kyawawa.

4. Ya zamo mai yabo da jinjina ga Allah da duk abin da Allah ya cancanci a yi masa hakan. Saboda ya tabbata wani mutum ya zo ya yi sallah a lokacin Annabi ﷺ yana zaune, da wannan mutum ya idar da sallah, sai ya roƙi Allah da cewa Allah ya yi masa gafara da rahama, sai Manzon Allah ﷺ ya ce masa: "Kai mai sallah ka yi gaggawa, idan ka yi sallah, to ka zauna ka yabi Allah da abin da ya cancance shi, ka yi mini salati, sannan sai ka yi addu'a". Tirmizhiy 3476.

5. Yi wa Manzon Allah ﷺ salati kafin fara addu'a kamar yadda ya gabata a hadisi na sama.

6. Fuskantar alƙibla yayin addu'a, saboda ya tabbata Annabi ﷺ ya fuskanci alƙibla ya yi addu'a a lokacin da ya fuskanci rundunar mushirikai su dubu ɗaya (1000) a ranar yaƙin Badar, shi kuma da Sahabbansa su ɗari uku da sha tara (319), ya fuskanci alƙibla ya ɗaga hannayensa ya roƙi Allah ya cika masa alƙawarin da ya yi masa, kamar yadda Muslim ya ruwaito a hadisi mai lamba ta 1763.

7. Daga hannaye a lokacin addu'a. Saboda sahabi Salmanu ya ruwaito cewa Annabi ﷺ ya ce: "Lallai Ubangijinku SWT Mai kunya ne, kuma Mai girma ne, yana jin kunyar bawansa idan ya ɗaga hannayensa zuwa gare shi ya kuma dawo da su ba komai". Abu Dáwud 1488.

8. Yin yaƙini a kan cewa Allah zai amsa maka addu'arka, kamar yadda hadisi mai lamba 3479 a Tirmizhiy ya tabbatar, wato ka riƙa jin tabbacin cewa lallai Allah zai karɓi addu'arka.

9. Naci da yawaita yin addu'ar a kai a kai.

10. Yin ƙanƙan da kai a cikin al'amura.

11. Cin abinci ta hanyar halal, da sanya tufafi ta halal, da nisantar haram ta kowace hanya.

Saboda Abu Hurairata ya ruwaito cewa Annabi ﷺ ya ce: "Ya ku mutane lallai Allah mai tsarki ne, ba ya karɓa sai mai tsarki, lallai Allah ya umurci Muminai da abin da ya umurci Manzanni, sai ya ce: "Ya ku Manzanni, ku ci daga tsarkaka, ku yi aiki na ƙwarai...), sannan kuma ya ce: "Ya ku waɗanda suka yi imani ku ci daga tsarkaka na abin da muka azurta ku)...".

Muslim 1015.

Wannan na nuni a kan cewa cin halal da shan halal, da sanya tufafin halal, dalilai ne da suke sa a karɓi addu'ar bawa.

Allah ya sa mu dace, amin. Kuma duk bawan da yake kiyaye waɗannan abubuwa da iznin Allah Allah zai riƙa karɓar addu'arsa.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Zauren Tambaya Da Amsa Abisa Alkur'ani Da Sunnah. Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments