Hukuncin Kwalliyar Da Mata Ke Yi A Lokacin Bikin Aure

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Malam Dan Allah mene hukuncin kwalliyar da mata suke yi a yanzu, su canza kala, da su eye lashes da ake sa wa da attach, in za a yi biki, kuma mene hukuncin wanda suka maida ita sana'a, dan amarya in za a yi mata akwai wadda ake yi dubu hamsin, akwai wadda ta fi ta, shin kuɗin ya kamata su ci, kuma sun ci halak?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salamu, kwalliya a lokacin biki za a iya kasa shi zuwa gida biyu, wato akwai kwalliya halastacciya da haramtacciya:

    1. Duk wata kwalliya da ba ta saɓa wa shari'a ba babu laifi idan an yi ta a lokacin biki, misali shafa abin da ba zai jirkita haƙiƙanin halittar Allah ba ga mata, kuma ba zai cutar ba, kamar gazal ko jambaki ko foda ko ƙunshi, da makamantansu, ko kuma ƙarin gashi na roba ko na zare a fahimtar wasu malamai, duk waɗannan babu laifi idan an yi su. Haka nan kuma ya zama kwalliya ce da babu nuna tsiraici, babu cakuɗuwa tsakanin maza da mata.

    2. Kwalliyar da ta saɓa wa shari'a kuwa haramun ne a yi ta, a lokacin biki ne ko ba lokacin biki ba, kamar shafa abubuwan da ko bayan an wanke su halittar mutum ba za ta koma asalin yadda take ba, misali man da ke ƙara hasken fata da ƙarin gashin ɗan'adam a kan gashi na asalin kan mutum ko yin wushirya, ko tsattsaga jiki (kwale), duk waɗannan jirkita halittar Allah ne, kuma jirkita halittar Allah haramun ne kamar yadda nassoshin shari'a suka tanadar. Haka nan ɗinka matsattsun tufafi ana nuna tsiraici da sunan kwalliya, duka waɗannan haramun ne.

    Game da masu yin sana'ar yin kwalliyar kuwa, su ma za a yi masu hukunci ne ta lura da kasa kwalliya kashi biyun can da aka yi. Wato kenan matuƙar kwalliyar da suke yi a matsayin sana'a ba wadda ta saɓa wa shari'a ba ce, to ya zama sana'a ce halastacciya. Amma kuwa idan kwalliyar da ta saɓa wa shari'a suke yi wa mutane da sunan sana'a, to wannan sana'a ta zama haramtacciya.

    Allah ne mafi sani.

    Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/IƘUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.