Wai me ya sa ake jarrabar mata a gidan aure?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Asssalamu Alaikum Malam. Wai me ya sa ake jarrabar mata a gidan aure?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Babu shakka Aure shi ne mafi girman ibada da Allah S.W.T ya karrama macce da ita, kuma Allah ya yi mata kwallia da shi a tsakan-kanin tsarekunta. Lallai daraja mai tsada irin wannan bazai yiwu Shaiɗan ya zurawa mata ido a kanta ba. Domin Riwaya Ta Tabbata Cewa Sahabiyya Asma'u Bint Yazeed (R.a) Taje Wajen Shugaba alhalin yana tsakiyar sahabbansa. Sai ta ce: Haƙiƙa Allah ya aikoka ne zuwa Maza da Mata, mun bika munyi imani dakai, Amma mu mata muna da rauni, muke gadin gida, mune ma'ajiyar sha'awar maza, muyi rainon 'ya'yansu Sannan su kuma maza an ƙara fifitasu da sallar Juma'a, Jam'i, Sallar Gawa da kuma fita jihadi, shin zamu samu lada irin nasu ya Manzon Allah? sai Annabi ya waiga wa sahabbansa ya ce dasu: "shin kun taba jin wata mace da takai wannan iya kyakkyawar tambaya a kan addininta?" sai sukace: "wallahi bamuyi zaton mace na samun shiriya irin wannan ba. sai shugabanmu ya juyo gareta yana mai cewa: "Asma'u ki koma ki sanar da matan da ke bayanki cewa: duk wacce ta kyautata zamantakewarta da mujinta, kuma take faranta masa don samun yardarsa, kuma ta bishi cikin umarninsa, haƙiƙa za ta samu duk irin ladan da maza ke samu" sai Asma'u Bint Yazeed ta juya cikin farin ciki sai hailala takeyi tana yin kabbara saboda wannan bushara data samu wajen Annabi Muhammad .

    Yanzu 'Yar Uwa Kina Zaton Shaiɗan Zai ƙyaleki da ibada 1 tak da a ƙarƙashinta za ki samu wannan romon???

    lallai a cigaba da haƙuri gami da JURIYA A cikin zamantakewar auredon bawa shaiɗan kunya da kuma samun Yardar Allah.

    Don kin yi imani, hakan ba shi ne yake nuna cewa shikenan Allah buwayi bazai jarabceki ba, dole akwai ranar da zai jarabceki domin ya bayyanar da imanin ki gareshi"

    ALLAH BUWAYI YA CE:

    "Ashe, mutãne sun yi zaton a barsu su ce: "Mun yi ĩmãni," alhãli kuwa bã zã a fitine su ba?" al-`ankaboot 2

    Yaa Allah ka jarabcemu daidai yadda imanin mu zai iya ɗauka, Ameen.

    WALLAHU A'ALAM

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/Fb6ƙgYPXfEeHb8CD1SWAkK

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.