'Yan bindiga a Anambara sun kashe mata mai ciki da 'ya'yanta guda huɗu ranar Lahadi, 22 ga watan Mayu, 2022. Shiru da aka yi game da al'amarin na iya nuni ga munafurcin masu ikirarin rajin kare 'yancin 'yan'adam.
ME KIKAI MASU NE HARIRA?
✍️ DR. MURTALA UBA (GEOGRAPHY DEPT, BUK)
23 Shawwal 1443H (24/05/2022)
Me ki kai musu ne Harira,
Har ya ja suka ɗauki ranki?
In akwai hujjar kisanki,
Babu laifi gun ɗiyanki.
In su Fatima sun yi laifi,
Me ya yi musu ɗan cikinki?
An yi zalunci tsirara,
An kar ki gami da ɗanki.
Ji suke yi sun ci banza,
Tun da ba gata gare ki.
Babu mai cewa ci-kan-ku,
Tun da ba dangi wajenki.
Wa yakan ce an yi zulmu,
Koko an cuta gare ki?
Na yi mamaki shirunsu,
Kan kisan gillar ga naki.
Da akai jiya mun ji gunji,
Sun ta ɓaɓatu da raki.
Da akai ma irin su mowa,
Mun ji har su kare da doki.
Sun kiran equity da justice,
Ke ko ba justice gare ki.
Kuma an taɓa Al-Aminu,
Mai mutunci shugabanki.
Yo ina justice ga bora,
Wa zai yi tweet a kanki?
Ko irin yin nan a goge,
Sui pretending a naki.
Kar ki damu akwai Ilahu,
Ke kina da Ubangijinki.
In mutane sun ƙi Allah,
Jalla bai watsi ya bar ki.
Ya gani kuma ya ji Jallah,
Zai yi sakayya gare ki.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.