Ticker

6/recent/ticker-posts

Mu San Tauhidi 03: Masu Tallalan Magani A Tashar TV

Mafi yawancin masu tallan magunguna na cire aljanu a tashoshin TV irinsu AREWA 24 da TAURARUWA da FARIN WATA da sauransu, kaso 95 daga cikin 100 na masu tallan maganin nan maƙaryata ne, kuma wasun suma mushrikai ne.

 Duk wanda yasan mene ne Tauhidi daya saurari bayanansu zai fahimci maƙaryata ne, wasu kuma shirka kawai suke yiwa ALLAH.

 Domin daga cikinsu akwai masu da'awar suna cire aljani daga inda suke, kamar mai larurar yana wani gari, shima mai cirewar yana wani gari, suna iya cirewa mutum aljanin da ke damaunsu daga nesa basai sunzo inda yake ba, wannan hanyar ta saɓa da koyarwa Alƙur'ani da sunnah, duk mai amfani da wannan hanya shima mushriki ne, domin yana tsafi ne, shi kuma tsafiba ya yiwuwa sai anyuwa aljani bauta.

 Wasu kuma daga cikinsu suna tallan magunguna na sanyi da gyaran jiki ga mata da sauransu suma da yawan waɗannan maƙaryata ne, masu maganin gaskiya basa bin irin waɗannan hanyoyin domin tallata magungunansu

 Kuma idan ka siya magani a gurinsu sau ɗaya sai suyita bibiyarka suce bayan ka gama da wannan saika sayi wancen sannan zaka sami lafiya, haka zasuyita yi maka kawai don su rabaka da kuɗadenka.

 Sannan daga cikinsu akwai masu tallan maganin haihuwa ko mallaka ko wanin hakan wanda, wannan ma ƙarya suke, da yawansu '‘yan damfara ne, kuma sunfi damfarar mata domin mata sukafi bibiyar irin waɗannan mutanen, kuma magungunansu akwai tsada gasu kuma ƙarya suke.

 Don haka muna kira gareku maza da mata ku guji ɗaukar lambar waya na masu tallan magunguna a tashoshin TV kuna kiransu, wasu zasu rabaku da imaninku, wasu kuma kawai kuɗin mutane sukeci amma ƙarya suke.

 Ku rinƙa zuwa islamic chemist idan kunada buƙatar magani, kuje su baku magani eamda yake da asali daga cikin littafin ALLAH, tare da bayanansa, amma ku dai siyan magunguna kai tsaye bakusan dame ake haɗasu ba.

 Musamman maza masu amfani da magunguna na ƙarfin maza, da yawan waɗannan magungunan na ruwa, suna haɗasu me da maganin bature, saisu narkashi su haɗashi a cikin zuma da maganin gargajiya, kai kuma kana ta amfani da magani dagaba ya ya haifar maka da cutar da bazaka iya komai ba.

 Sannan mata masu amfani da magungunan mata na ni'ima suma da yawa suna siyan magani basusan dame aka haɗashi ba, daga ƙarshe wata sai ya jawo mata cancer, ko sanyi ko lalacewa farji, ko tusar gaba ko rikicewar al'ada da sauransu.

ALLAH ka bamu ikon aiki da abin da muka karanta.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments