𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Game da mai ciki a Ramadan; shin ya kamata ta fara gwada azumin ne taga ko za ta iya koko kawai za ta iya ajiyewa ta ciyar gudun Kada ita ko Ɗan ya wahala? Domin wani lokacin me cikin za ta iya yi amma ba a Jere ba. Wata Kuma za ta iya yi duka ba tare da ta wahala ba. To idan ya kama mutum zai iya yi yana hutawa kwanakin da ta huta ɗin ciyarwa za ta yi koko sai dai ta rama daga baya?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Toh wannan abin da ya fi shi ne seta fara gwadawa intaji
cewa tana shan wahala, wahala wacce tawuce ƙa'ida ta
wuce wuyarda akeji na dabi'a taji dai cewa lallaifa bazata iya ba to shi ne za
ta dena yin azumin kawai tacigaba da ciyarwa amemakon kowanne azumi da tasha,
wannan kuma haka me shayarwa ita ma za tayi, ba kawai saboda kina da ciki ko
kina shayarwa sekiƙi yin azumiba, A'a sekin jaraba kinji
baze yiwuba shi ne seki rika ciyarwa kawai a madadin kowanne azumi
Allah ta'ala ya sa mu dace
Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare
Da Fadakarwa a Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Bvk6LLvY9evDZHXFMZCzeU
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.