An ƙirƙiri wannan shafi ne domin ɗalibai da masana da manazarta Hausa da ke makarantu daban-daban. Za ku iya amfani da wurin rubuta tsokaci (comment) da ke ƙasa domin duba tattaunawar da ta gaba ko tura sabon saƙo.
Manufar wannan kafa ita ce samar da haɗin kai da zamowa farfajiyar ƙaruwa da juna musamman ta hanyar turo tambayoyi, amsa tambayoyi, turo muhimman bayanai da suka shafi karatun Hausa da ilimummumukan zamani da zamantakewa, da makamantansu.
Za ku iya turo tambayoyi ko ku amsa tambayoyi da aka turo.
Mun gode.
Na ji daɗin ganin wannan zaure. Allah ya ƙara ɗaukaka harshen Hausa. Amin.
ReplyDeleteTunani mai kyau.
ReplyDeleteAllah ya albarkacin wannan dandali
Wannan dandali zai taimaka matuƙa wajen tattauna muhimman abubuwa da za su ciyar da harshen Hausa gaba. Allah Ya saka maka da alheri, amin.
ReplyDeleteDa kyau! Wai kare ya ga rawar kura.
ReplyDeleteMadalla da wannan dandali mai albarka. Allah ya sa mu amfana.
To madallah
ReplyDeleteMaasha Allah.
ReplyDeleteMuna maraba da wannan dandali mai albarka wanda zai jagoranci wayar da kan ɗalibai da malamai da ma sauran masu nazari wajen warware zare da Abawa dangane da abin da ya shige wa al'umma duhu game da Harshenmu kuma abin Alfaharinmu don ganin ya ci gaba da ƙanshin ɗan goma. Allah Ya ƙaro basira kuma Ya yi mana jagora baki ɗaya. Amin.