Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsokacin Wasu Fitattun Mutane Game Da "Diwanin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Diwanin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (na Prof. S.A. Yakasai da Abu-Ubaida Sani) ya yi dacen samon sanya albarka daga wasu fitattun mutane. Ga abubuwan da suke cewa:

An yi sa’a an haɗa waƙoƙin tun ALA yana raye… Dr. Bukar Usman, M.IoD, D.Litt, OON

MUƘADDIMA

Farfesa Sa’adiya Omar
Darakta, Cibiyar Nazarin Hausa
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato

Godiya ta tabbata ga Allah (Subhanahu Wata’ala) wanda ya halicci ilimi. Tsira da amincinsa su tabbata ga Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi wa Sallam) wanda ya wajabta neman ilimi a kan dukkan Musulmi maza da mata. Na yi matuƙar farin ciki da aka nemi na yi muƙaddima a wannan littafi mai suna DIWANIN WAƘOƘIN AMINU LADAN ABUBAKAR (ALA), littafin da Farfesa Salisu Ahmad Yakasai da Abu-Ubaida Sani suka rubuta a kan ɗaya daga cikin shahararrun mawaƙan Hausa na wannan zamani.

Haƙiƙa irin wannan aikin haɗin-guiwa tsakanin malami da ɗalibi, wata sabuwar hanya ce ta taskacewa da kuma adana waɗannan waƙoƙi domin kada su salwanta. Abin lura a nan shi ne irin tagomashin da waɗannan waƙoƙi na zamani suke da shi, wajen isar da saƙonni ta siga daban-daban domin inganta rayuwar al’umma. Bugu da ƙari, wannan Diwani ya zo da bayani mai zurfi game da rayuwar Aminu ALA, wato tarihin ya fito da bayanai dangane da ƙimarsa a cikin al’umma da yanayin da ya samar da waƙoƙi da kuma mutanen da aka yi waƙoƙin domin su.

Wani ƙari da aka samu kuma a wannan Diwani shi ne na tattara waƙoƙin a bisa jigogin da suka dace. Wato kama daga jigon ilimantarwa da wa’azantarwa da faɗakarwa zuwa na siyasa da soyayya da sarauta da kuma na yabo da jinjina. Sauran sun haɗa da jigogi na ganin dama da na talla da na aure da na ta’aziyya da ɗaukaka da kuma na zagin kasuwa. Dukkan waɗannan abubuwa sun zama shaidar da za a tabbatar da cewa wannan aiki na marubutan haɗaka, wata gudummawa ce ga ci gaban nazari a fagen adabi, musamman ma fannin waƙoƙin Hausa na zamani.

 

JINJINA

Alhaji Aminu Ado Bayero
Mai Martaba Sarkin Kano

Muna godiya ga Allah mai kowa mai komai da ya nuna mana fitowar wannan muhimmin littafi da aka rubuta a kan waƙoƙin fasihi, gwani, rumbun hikima wato Alhaji Aminu Ladan Abubakar (ALA). Haƙiƙa ALA wani babban jigo ne kuma jagora a fagen adabin Hausa na zamani, domin shi ne fitila mafi haske a cikin fitilun da ke haskaka wannan sabon jigo na waƙoƙin Hausa na zamani.

ALA ya yi amfani da ɗimbin basirar da Allah ya yi masa wajen ɗabbaƙa sabon salo a waƙar Hausa ta yadda tilas ya ja hankalin masana da manazarta adabin Hausa.

Diwani wata taska ce ta adana ayyukan fasaha da suka danganci waƙa, da zube, da wasan kwaikwayo, da sauran ayyukan adabi. Muna maraba da wannan diwani na waƙoƙin Alhaji Aminu Ladan Abubakar, da fatan littafin zai amfanar a fagen bincike da nazari ga malamai da kuma ma’abuta sha’awar waƙoƙin Hausa.

Marubutan wannan littafi wato Prof. Salisu Ahmad Yakasai da ɗalibinsa Abu-Ubaida Sani, haƙiƙa sun yi tsinkaye da hangen nesa wajen yin wannan gagarumin aiki domin ƙara fito da wannan sabon fanni na adabi da taskace waƙoƙin ALA domin amfaninmu baki ɗaya. Allah Ya albarkaci wannan littafi, ameen.

 

ALLAH SAN BARKA

Ado Ahmad Gidan Dabino, MON
Tsohon Shugaban Ƙungiyar Marubuta ta Nijeriya, ANA
Reshen Jahar Kano

Samar da littattafai a kan waƙoƙin fasihan mawaƙan Hausa na Arewacin Nijeriya babban abin jin daɗi da kuma alfahari ne, saboda ana adanawa da killace ire-iren waɗannan ayyuka domin gudun ɓacewarsu wata rana. Diwanin waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA), na tabbata zai zama abin so ga jama’a musamman masu son waƙoƙinsa da kuma manazarta.

 

TSOKACI

Alhaji Kabir Assada
Babban Edita, Mujallar Muryar Arewa

Littafin Diwanin Waƙoƙin Amini Ladan Abubakar (ALA), wani kundi ne da ya zamo ɗaya-tamkar-da-goma idan ana maganar taskace tarihin mawaƙan Hausa na wannan zamani da kuma ayyukansu. Mawallafan littafin sun nuna ƙwarewa da naƙaltar sanin ƙabli da ba'adin wannan fage na adabi, musamman idan aka yi la'akari da tsari da zubin littafin.

 

GOYON BAYA

Hajiya Fati Nijar
Mawaƙiyar Hausa

Waƙa tana taka muhimmiyar rawa wajen haɓaka harshe da kuma bunƙasa al'adun al'umma. Samuwar DIWANIN WAƘOƘIN AMINU LADAN ABUBAKAR (ALA), tanadi ne na kare wannan aiki na adabi daga salwanta. Marubuta littafin sun nuna ƙwarewa cikin hikima.

 

YABAWA

Malam Sulaiman Salisu Muhammad
(Mai Bazazzagiya)

Yau Farfesa Salisu Yakasai,
Sani Ubaida kun yi aiki sosai,
Gun Diwanin nan na ALAN Waƙa.

 Wannan aiki Allah sa albarka,
Babbar gona ce ciki ga shuka,
Kwanyar ALA ga ta nan fa ta waƙa.

 Don adabi ALA yana raya shi,
Har al’ada ba a bin sa fa bashi,
To haka harshen walwala gun waƙa.

Diwanin Aminu Ladan Abubakar (ALA)


 


Post a Comment

0 Comments