𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum warahmatullah. Allah ya sakawa da malam da alkhairi. Dan Allah ina neman bayani game da shafa wani mai da yake fito da gemu. Kamar Amfani da MINOXIDIL
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumus salam warahmatullahi wabarakatuhu,
Shafa man da ke fito da gemu kamar Minoxidil halal ne, babu laifi a amfani da shi, bisa fatawar malamai da dama kamar Ibn Baz, Ibn Uthaimin da Lajnatud
Da'ima. matuƙar abinda yake amfani da shi baya ƙunshe da wani abu na haram kuma baya cutar da lafiyarsa.
Minoxidil wani magani ne da ake amfani da shi wajen taimakawa gashi ya yi girma,
kuma wasu mutane suna amfani da shi domin taimakawa gemu ya fito. Saboda haka,
amfani dashi ba haramun bane kai tsaye, amma hukuncinsa yana danganta da
amincinsa ga lafiyar mutum da kuma abubuwan da aka haɗa shi da su. Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:
وَلَا تُلْقُوا بِأَيْدِيكُمْ إِلَى التَّهْلُكَةِ
"Kada ku jefa kanku cikin halaka da hannuwanku." (Suratul Baƙara ayata 195).
Haka kuma Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya ce:
«لَا ضَرَرَ وَلَا ضِرَارَ»
"Babu cutarwa, kuma babu rama cutarwa da cutarwa." (Sunan Ibn
Majah, Hadisi na 2340).
Wannan yana nuna cewa duk wani abu da zai cutar da lafiyar mutum bai
halatta ya ci gaba da amfani dashi ba. Ya kamata a sani cewa Minoxidil na iya
taimakawa wasu mutane wajen ƙara yawan gashin gemu, amma ba kowa yake samun sakamako
iri ɗaya ba, sannan amfani da shi a gemu ba shi ne amfanin da aka fi amincewa da shi a hukumance ba. Yana iya haifar da
kaikayi, bushewar fata, ja ko kumburi, jiri ko bugun zuciya da sauri a wasu
mutane.
Saboda haka, yana da kyau mutum ya nemi shawarar likita kafin ya fara
amfani dashi, musamman idan yana da matsalar zuciya ko hawan jini. A taƙaice, neman hanyar da
zata taimaka gemu ya fito ba laifi bane a Musulunci, amma dole ne a kiyaye
lafiyar jiki da guje wa duk wani abu mai cutarwa.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.