𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Idan ma’aurata suka samu saɓani wajen fahimtar Musulunci; ɗaya daga cikinsu ya taso ne a Yammacin duniya, ɗayan kuma a Gabas, kuma kullum suna yawan saɓani da rigima har ba sa iya cimma matsaya ɗaya, yaushe ne ake ɗaukar ṭalaƙ (saki) a matsayin mafita?
Shin ya zama laifi mace ta
nemi saki? Shin za a hukunta ta a Ranar Alƙiyama
saboda neman saki? Shin Al’arshin
Allah (Arsh na Ar-Rahman) yana girgiza idan aka nemi saki? Wannan shi ne abin
da wani miji ɗan Gabas yake gaya wa wata mata da ta
taso a Yammacin duniya.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Godiya ta tabbata ga Allah,
tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzon Allah ﷺ.
Mace tana iya neman saki
idan akwai ingantaccen dalili na Shari’a. Hadisin da yake cewa saki yana sa
Al’arshin Allah ya girgiza ƙirƙirarren hadisi ne na ƙarya.
Sakin mace Musulma daga
mijinta lamari ne da Allah ba Ya so, kuma ba abin yabo ba ne. Wannan kuwa
saboda matsalolin da ka iya biyo bayan saki da kuma munanan abubuwan da za su
iya faruwa sakamakonsa.
Amma idan akwai wata matsala
a rayuwar aure tsakanin miji da mata, sakamakon wani aibi ko wasu aibu da ke
tattare da ɗaya daga cikinsu ko dukkansu, kamar
matsalolin addini, mummunan hali, rashin lafiya, ko wani aibi kamar rashin
haihuwa, ko makamancin waɗannan, to saboda rahamar
Allah, neman saki ya halatta. A irin wannan yana yin, babu laifi ko haramci a
cikin neman saki.
Abin da aka haramta shi ne
mace ta nemi saki daga mijinta ba tare da wani ingantaccen dalili na Shari’a
ba. An yi gargaɗi mai tsanani game da neman
saki ba tare da ingantaccen dalili ba. An ruwaito daga Annabi (SAW) cewa: “Idan mace ta nemi
mijinta ya sake ta ba tare da wani dalili ba, to an haramta mata ƙamshin Aljanna.” Imam At-Tirmidhi ne ya
ruwaito hadisin, kuma ya ce hadisin hasan ne. (Sunan At-Tirmidhi, 1187.)
Hadisin da ake cewa: “Ku yi
aure, kada ku yi saki, domin lalle saki yana sa Al’arshin Allah ya girgiza.”
Hadisi ne ƙirƙirarre kuma mai rauni (da’if). (Al-Jami‘ as-Saghir, 2429.)
Allah ne Mafi sani.
Amsawa: Shaikh Muhammad
Saleh Al-Munajjid (Hafizahullah) Fassara: Usmannoor Rijiyar Lemo.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.