Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Sallar Wanda Mace Ta Wuce Ta Gabansa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu Alaikum Malam Khamis barka da juma'a ya ibada da fatan kana lafiya. Tambaya ta anan shi ne; mene ne hukuncin sallar wanda mace da wuce ta gabansa, shin sallarsa ta ɓaci idan ya sanya sutura? Idan bai sanya sutura ba zai sake sallar ne ko ba zai sake ba ? Na gode sosai

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.

Hukuncin sallar wanda mace ta wuce ta gabansa ya kasu kashi biyu a tsakanin malaman Musulunci, saboda bambancin fahimtar hadisin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam). A cikin Sahih Muslim, akwai hadisin da ke cewa: “Sallah tana yankuwa idan babu sutra a gaban mutum, idan mace baliga, ko jaki, ko baƙin kare suka wuce ta gabansa.”

Dangane da wannan, ga yadda mahangan malaman suke

1. Ra'ayin Mazhabar Hanbaliyya da Wasu Malaman Hadisi: Sallar Ta Ɓaci kuma dole sai an sake. Wannan ita ce maganar wasu daga cikin sahabbai da malamai kamar su Imam Ahmad ibn Hanbal (a wata ruwayar) da kuma malaman zahiriyya. Suna ganin cewa idan mace baliga ta gitta ta tsakanin mai sallah da wurin sujudarsa (idan bashi da sutura), sallar sa ta lalace kuma wajibi ne ya sake ta.

Alƙurdubi Rahimahullah ya ce: " Saboda mace tana fitinar mutum, Jaki Yana kuka, kare yana kai kawo, Saiya jefawa mutum shakku yakama tunani, harsai ya yanke masa sallah ta ɓaci, saboda wadannan al'amura suna kaiwa ga yanke sallar sai aka sanyasu Suna yanke sallah, Almuf-ham lima Ashkala min Talkisul Sahihu Muslim (2/209).

Ibnu rajab rahimahullah bayan ya ambaci irin waccan fassarar ya ce: Mafi kusa da wannan fassara shi ne ace: Lokacinda mai Sallah yashagalta da ganawa da Mahaliccinsa, shi ne lokacinda yafi kusanci da shi yakuma kebanta, Sai aka Umarci mai sallah ya yi taka tsan-tsan wajan gudun kada Shaiɗan yashiga wannan kebewa ta musamman daya yi da Allah, da kusanci na musamman, saboda haka aka shar'anta sanya sitra asallah dan tsoran kada Shaiɗan yashiga, ta kasance Abar kare shaiɗan awannan lokaci, ta hakane kauna da tausasawa za ta shiga da kusanci, domin shaiɗan korarrene daka kusantuwa da inda Allah yake, idan ya nisanci gurin ganawa ta Musamman gamai sallah, Zai zama dole ya yi nisa da yanke rahma da kauna da kusanci da tausasawa.

Wannan shi ne ma'anar kebance wadannan abubuwa uku wajan nesanta daka garesu sune: Mace da Bakin kare da jaki. Mata tagogin shaiɗan ne, idan mace tafita daka gidanta sai shaidan yahade da ita. shaiɗan yasamu damar nesantar Annabi Adam daka gidan rahama da mace.

2. Ra'ayin Jamhurin Malamai (Mafi yawan malamai kamar su Malikiya, Shafi'iyya, da Hanafiyya): Sallar Ba Ta Ɓaci Ba kuma ba zai sake sallar ba: Mafi yawancin malamai (Jamhur) kamar su Imam Malik, Imam Shafi'i, da Imam Abu Hanifah, suna ganin cewa sallar mutum ba ta ɓaci ba, kuma ba zai sake ta ba. Hujjarsu: Sun dogara da hadisin da Nana Aisha (RA) ta fada cewa ta kasance tana kwanciya a gaban Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) alhali yana sallah, kuma idan zai yi sujada sai ya taɓa ƙafafunta ta tatarre su. Wannan ya nuna cewa kasancewar mace a gaban mai sallah ba ya ɓata sallah.

Sun fassara kalmar "yanke sallah" (قطع الصلاة) da ke cikin hadisin da cewa yana nufin rage lada da kuma yanke nutsuwar sallah, ba wai ɓata sallar baki ɗaya ba.

Wucewa ta gaban mai Sallah haramun ne, macece ko namiji ko dabba saboda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce: (Da'ace mai wucewa tagaban mai sallah ya san Abun da zai samu na zunubi da ya tsaya Mai sallar yagama sallar sannan yawuce koda zai kai kwana Arba'in kafin ya idar da sallar) Bukhari (510).

Abubuwan Da Ke Kare Sallah Daga Wannan Matsalar shi ne Sanya Sutura, Don kauce wa shiga cikin wannan saɓani, an shar'anta wa mai sallah sanya Sutura (kamar kishingidawa ga bango, sanya kujera, ko sanda) a gabansa gwargwadon ragowar karshen dabbar hawa, Ma'ana idan kahau dabba ɗan wajan da yake ragowa daka bayanta inkasa sitra kamar wannan marabar ta isar maka daka yankewar sallarka. Idan mace ta wuce ta bayan suturar, wannan ba zai cutar da sallar ba ko kaɗan. Idan mutum yana bin liman ne, suturar liman ita ce suturar mutanen da ke bayansa, don haka wucewar mace ta gaban layuka ba ta ba ta sallar mamu.

WALLAHU TA'ALA A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam   

Post a Comment

0 Comments