Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Matar Aure Da Ta Yi Zina Har Ta Samu Ciki

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu alaikum Malam khamis barka da Safiya da fatan ka tashi lafiya. Malam Khamis mace ce mai aure ta yi zina dawani a lokacin sai ciki ya shiga, shin ya halatta ta zubar cikin ko za ta kyale shi, idan ta kyale cikin shin za ta baiwa mijinta labari ko ba zata bashi ba? Idan ta haihu shin yaron na mijin aure ne ko na wanda ya yi zinar da ita? Na gode Allah ba da ikon amsawa.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumussalam warahmatullahi wabarakatuh.

Babu makawa abun da kin aikata na zina kina matar aure yana cikin manyan laifuka, koda zina zunubi ce maigirma ita kaɗai to girman zunubin nakaruwa idan aka ce mai aure ta yi zina, shiyasa ma hukuncin mazinacin da bai taɓa aure ba shi ne bulala 100, wanda kuma yake da aure ko yataɓa aure shi ne ajefeshi harsai ya mutu.

Allah Yana cewa

وَلَا تَقۡرَبُوا۟ ٱلزِّنَىٰۤۖ إِنَّهُۥ كَانَ فَـٰحِشَةࣰ وَسَاۤءَ سَبِیلࣰا

Kuma kar ku kusanci zina, haƙiƙa ita alfasha ce, kuma mummunar hanya ce. (Surah Al-Israa’i: 32).

Hakika kin tafka babban kuskure. Domin zina tana cikin Kaba'irori wato zunubai mafiya girman laifi awajen Allah. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Ya ce: "Bayan yin shirka da Allah, babu wani zunubi mafi girman laifi kamar maniyyin da namiji ya sanyashi a cikin mahaifar matar da ba ta halatta gareshi ba".

Imamuz zahaby ya kawo a cikin littafinsa Alkaba'ir cewar duk Wanda ya yi zina da matar aure za a yi musu azaba (da shi da ita) Rabin azabar wannan al'umma.

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya ce: “duk matar da ta shigo ma wasu mutane ɗan wani wanda ba cikinsu yake ba, to ita ba komai bace Awajen Allah. Kuma (Allah) ba zai shigar da ita aljannarsa ba… “ (Nisa’iy hadisi na 3481, Abu Dawud Hadisi na 2263).

Duk macen da ta yi zina alhalin tana da aure haƙiƙa ta ci amanar mijinta kuma tabbas sai Allah ya bi ma sa haƙƙinsa a ranar alƙiyamah matuƙar be yafe mata ba. Saboda haka ki nemi yafiya a wajen mijinki cikin salo ba tareda ya gane abin da kika aikata ba.

kinga anan gayawa mijin naki cewa kinyi zina yayafe miki wannan babu shakka maslaha ne, to amma kuma bakida tabbacin cewa mijin zai hakura yayafe miki kuma yaci gaba da zama dake bayan kin gaya masa, kekanki zaki riƙa tunanin infa kika gaya masa kinyi zina ze iya cewa ya sake ki, wanda sakin shikuma ɓarna ce, bayan sakin kuma waɗanda basu san kinyi wannan zinan ba duk sesun sani musamman iyayenki kuma mutuncinki zai zube kinga wannan duk ɓarna ce, sannan kuma kin tonama kanki asiri bayan Allah ya rufa miki.

Dan haka malamai suka ce wacce tasamu kanta a cikin irin wannan halin to kawai taroƙi mijin yayafe mata dukkan laifukan da ta yi masa waɗanda ta sani da wanda ba ta saniba, amma karta kuskura ta gaya mishi cewa ga abin da ta yi saboda karta buɗe ƙofar waɗancan ɓarnace ɓarnacenda za su iya biyo baya.

Haramun ne mace ta zubar da ciki koda kuwa na zina ne. Zina babban zunubi ce, kuma zubar da cikin zai zama ƙarin wani babban zunubin na daban (kamar kisan kai). Saboda haka, dole ne ta bar cikin har ta haife shi, kuma jaririn bashi da laifin komai na abin da mahaifiyarsa ta aikata.

A Shari'ar Musulunci, idan mace mai aure ta samu ciki ta hanyar zina har ta haihu, yaron na mijin aure ne, ba na mazinacin ba. Wannan ya dace da sanannen hadisin Manzon Allah (ﷺ) inda ya ce

"الْوَلَدُ لِلْفِرَاشِ وَلِلْعَاهِرِ الْحَجَرُ"

("Ɗa na mai shimfida ne [mijin aure], shi kuma mazinaci bashi da komai sai jifa").

Muddin mijin yana saduwa dake a wannan lokacin, to yaron yana karkashin nasabar mijin ne. Sai dai idan shi mijin da kansa ya musanta cikin ta hanyar rantsuwar LI'ANI a gaban alkali (idan ya gano gaskiyar lamarin).

An tambayi SHAIK BIN BAAZ dangane da matar datake da aure saita samu ciki ta hanyar zina, shin ya halatta ta zubda cikin ɗan? ko za ta kyaleshi, idan ta kyale cikin shin za ta baiwa mijinta labari ko ba zata bashi ba? sannan mene ne yake wajibi a kan mijin a wannan halin?

Sai ya amsa dacewa: Bai halatta agareta ta zubda wannan cikin ba, abun da yake wajibi akanta shi ne tuba zuwa ga Allah maɗaukakin sarki, da kuma kin bayyana al'amarin, ɗan da ta haifa kuma za a jinginawa mijinta ma'ana ɗansane, saboda faɗin Annabi sallahu Alaihi wasallam (Ɗa na mai aure ne mazinaci kuma uƙuba ce kawai tasa) Ma'ana wanda ya yi zina baida hakkin ajingina ɗan gareshi, shi kawai uƙubar zinarce a kansa. Fatawa bin bãaz (21/205). Da wannan majalisar fatawa ta kasar saudiyyah ta yi fatawa akai.

Tare da girman laifin da kika aikata da muninsa a al'ada da kuma hankali, babu wanda zai shiga tsakanin Allah da bawansa, Allah yana farin ciki da tuban bawa kuma yana karɓar tuban, Allah maɗaukakin sarki Ya ce

قُلْ يَا عِبَادِيَ الَّذِينَ أَسْرَفُوا عَلَىٰ أَنفُسِهِمْ لَا تَقْنَطُوا مِن رَّحْمَةِ اللَّهِ ۚ إِنَّ اللَّهَ يَغْفِرُ الذُّنُوبَ جَمِيعًا ۚ إِنَّهُ هُوَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ

Ka ce: ''Yã bãyĩNa waɗanda suka yi ɓarna a kan rãyukansu! Kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah. Lalle Allah na gãfarta zunubai gabã ɗaya. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.' (Suratul Zumar Aya ta 53).

Ibnu kasir rahimahullah Ya ce: Wannan aya tana kirane ga dukkan masu saɓo su tuba su koma zuwa ga Allah, tana kuma ba da labarin Allah yana gafarta zunubai baki ɗaya ga duk wanda ya tuba yadawo daka aikata laifukan, komai irin yawansu da girmansu koda sunkai yawan kumfar kogi, matukar an yi tuba na gaskiya Allah yana gafarta su.

Saboda haka kiyi nadama ki koma ga Allah cikin gaggawa, ki yanke kowace irin alaka da wancan mazinacin, ki kyautata wa mijinki kuma ki roki Allah ya asirta ki a duniya da lahira.

WALLAHU TA'ALA A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

 ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam   

Post a Comment

0 Comments