Ticker

6/recent/ticker-posts

Falalar Salatin Manzon Allah (SAW)

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh. Dan Allah malam ina so ka bayyanamin nassi da ya kawo falalar salatin manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) a ranar Juma'a

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam Warahmatullahi Wabarakatuh.

Ɗan'uwa tunda Allah da kansa ya ce yana salati ga manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) kasan ba karamar falala ce a cikin sa ba. Allah سبحانه وتعالى Ya ce

 إِنَّ اللَّهَ وَمَلَائِكَتَهُ يُصَلُّونَ عَلَى النَّبِيِّ ۖ يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا صَلُّوا عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا تَسْلِيمًا

Lallai Allah da Mala'ikunsa suna yi wa Annabi salati. Ya ku waɗanda kuka yi imani Ku yi masa salati, kuma ku yi masa sallama cikakkiya. (Suratul Ahzab).

Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya ce

مَنْ صَلَّى عَلَيَّ وَاحِدَةً صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ عَشْرًا

Duk wanda ya yi min salati sau ɗaya, Allah zai yi masa salati sau goma. (Sahih Muslim).

Haka nan Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya ce

مَنْ صَلَّى عَلَيَّ صَلَاةً وَاحِدَةً صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ بِهَا عَشْرَ صَلَوَاتٍ، وَحُطَّتْ عَنْهُ عَشْرُ خَطِيئَاتٍ، وَرُفِعَتْ لَهُ عَشْرُ دَرَجَاتٍ

Duk wanda ya yi min salati sau ɗaya, Allah zai yi masa salati sau goma saboda ita, a kankare masa zunubansa goma, kuma a ɗaga masa darajarsa sau goma. (Sunan An-Nasa'i).

Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya ce

إِنَّ مِنْ أَفْضَلِ أَيَّامِكُمْ يَوْمَ الْجُمُعَةِ، فَأَكْثِرُوا عَلَيَّ مِنَ الصَّلَاةِ فِيهِ، فَإِنَّ صَلَاتَكُمْ مَعْرُوضَةٌ عَلَيَّ

Lallai daga cikin mafi alherin kwanukanku akwai ranar Juma'a. Saboda haka ku yawaita yi min salati a cikinta, domin ana gaba tar min da salatinku a gareni. (Sunan Abu Dawud).

Sannan Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya ce

أَكْثِرُوا عَلَيَّ مِنَ الصَّلَاةِ يَوْمَ الْجُمُعَةِ وَلَيْلَةَ الْجُمُعَةِ

Ku yawaita yi min salati a ranar Juma'a da daren Juma'a.

Saboda haka ya kamata Musulmi ya yawaita salati ga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) a ranar Juma'a da darenta, domin Allah ﷻ Ya yi umarni da yin salati gare shi, kuma Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya bayyana falalarsa a hadisai da dama.

Allah ne mafi sani.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam   

Post a Comment

0 Comments