Ticker

6/recent/ticker-posts

Bayani Game Da Hukuncin Wanda Ya Yi Sallah Ba Zuwa Ga Alkibla Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Meye hukuncin mutumin da ya yi sallah, sai bayan ya gama sannan ya fahimci cewa wannan sallah da ya yi ba Alƙibla ya fuskanta ba?

BAYANI GAME DA HUKUNCIN WANDA YA YI SALLAH BA ZUWA GA ALƘIBLA BA

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Yana daga cikin sharadin sallah mutum ya fuskanci Alƙibla matukar ba wata matsala aka samu ba wadda za ta hanashi hakan, inhar ko mutum yaki fuskantar Alƙibla alhalin yana da dama toh sallarsa ba tacciya ce, sabida Allah ya ce

قَدْ نَرَىٰ تَقَلُّبَ وَجْهِكَ فِي السَّمَاءِ ۖ فَلَنُوَلِّيَنَّكَ قِبْلَةً تَرْضَاهَا ۚ فَوَلِّ وَجْهَكَ شَطْرَ الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ ۚ وَحَيْثُ مَا كُنْتُمْ فَوَلُّوا وُجُوهَكُمْ شَطْرَهُ ۗ وَإِنَّ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ لَيَعْلَمُونَ أَنَّهُ الْحَقُّ مِنْ رَبِّهِمْ ۗ وَمَا اللَّهُ بِغَافِلٍ عَمَّا يَعْمَلُونَ

Lalle ne, Muna ganin jujjũyawar fuskarka a cikin sama. To, lalle ne, Mu jũyar da kai ga Alƙibla wadda kake yarda da ita. Sai ka jũyar da fuskarka wajen Masallaci Tsararre, kuma inda duk kuka kasance, to, ku jũyar da fuskõkinku jiharsa. Kuma lalle ne waɗanda aka bai wa Littafi, haƙĩƙa su, suna sanin lalle ne, shĩ ne gaskiya, daga Ubangijinka. Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga abin da suke aikatawa. (Baƙara 144).

Da umarnin da annabi (Sallallahu alaihi wasallam) ya yi ya ce “Sannan ka fuskanci alƘibla kayi kabbara) Bukhari 6667.

Maluman sun tafi akan cewa wanda ya yi sallah ba zuwa ga Alƙibla ba da gangan ko a halin mantuwa zai sake, sabida bai cika sharadinta ba.

An tambayi maluman ‘Lajnatudda’imah’ kan hukuncin matafiyi da ya isa gari, ya yi sallah ba zuwa ga alƙibla ba, kuma bai tambaya ba, baiyi bincike ba, suka ba da amsar cewa zai sake wannan sallar, sabida rashin bincike da baiyi ba, ko kokari wurin gano alƙiblar, (Lajnatudda’imah Majmu’ah ta biyu 5/294).

Dan haka, ya wajaba akan wanda ya yi sallah ba zuwa ga Alƙibla ba yana mai mantuwa ya sake sallansa, amma in ya rasa gane Alƙibla sabida rashin wanda zai tambaya, ko kuma wasu dalilai, toh mafi yawan Malamai suna akan ba zai sake ba. kuma hakan shi ne daidai…….

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments