Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Masu Aljanun Da Suke Bayar Da Magani

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Mene ne hukuncin masu aljanun da suke bayar da magani?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Mu’amala a tsakanin mutane da aljanu abu ne da ya daɗe a tarihi, kuma yawanci ba ya haifar wa mutanen da suka shiga cikinsa wani alheri. Domin abu ne mawuyaci wani aljani ya yarda ya haɗa-kai ko baki ko gwiwa da wani ɗan Adam a kan wata buƙatarsa, in ba shi ɗan Adam ɗin ya bayar da wani taimako ko hanun-jari mai tsoka ga wannan aljanin ba. Wanda kuma a ƙarshe zai janyo cutuwa ko asara ko lalacewa ga shi kansa wannan mutumin ko danginsa ko kuma wasu daga cikin yan uwansa mutane. Shiyasa malaman Sunnah suka yi tsawa a kan a nisanci irin wannan ƙullin zumuncin, domin neman a tsira da imani.

Magani iri biyu ne: Akwai wanda ake samun sa ta hanyar jarrabawa ko gwadawa daga wurin masana harkar lafiya, ko dai a gargajiyance a wurin masana harkar ko kuma a zamanance a asibitoci. Akwai kuma wanda ake samun sa ta hanyar karanta wasu Ayoyin Alƙur’ani ko wasu Addu’o’i Ingantattu, tare da amfani da wasu saiwoyi ko ganyayyaki ko yin ƙaho, irin yadda suka tabbata daga Annabin Rahama (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam). Wannan irin maganin kasidin ne, kuma shi ake samu ta wurin malamai masana addini, kuma masu Imani da tsarkin zuci da kyautata ayyuka a cikin alumma.

Neman magani daga waɗannan wuraren biyu ya halatta, matuƙar dai ana tare da aƙidar cewa: Waraka dukkanta a hanun Allaah Maɗaukakin Sarki ta ke. Kuma matuƙar ana yin maganin ne tare da ƙanƙan-da-kai da neman waraka daga Allaah Mahaliccin dukkan komai. Sannan kuma matuƙar ba a tabbatar da cewa akwai wata matsala mai cutarwa da aka cusa ko aka gauraya a cikin wannan maganin da aka karɓo daga wurinsu (malaman) ba.

Amfani da ganye ko itatuwa masu tsarki da kuma turare mai daɗi (kamar miski ko ūd) domin yin ruƙya ko turarena muhalli halal ne, muddin an dogara ga Allah kuma an yi da Alkur'ani. Idan an haɗa da surkukuwa, buƙatar miyagun abu, ko ambaton sunayen aljanu, to amfani da su ya bace kuma ya haramta.

Akwai kuma waɗansu malaman da ba irin waɗannan malaman na Allaah ba. Su ne kamar bokaye ko masu duba ko malaman istikhaara ko yin addu’a, waɗanda su ma ake kiran su da suna malamai. Amma kuma ayyukansu ba kyawawa abin yabo ba ne, sakamakon abin da suke yi na yin ta’ammali da rauhanai ko aljanu mutane ɓoye. Yawancin waɗannan suna samun maganin da suke bayarwa ga masu zuwa wurinsu ne ta hanyoyin yardar da shaiɗanun aljanu, kamar ta biya musu buƙatun da suka nema daga wurinsu na ayyukan saɓo da shirka da kafirci.

Hanya ta gari wajen maganin aljanu ita ce Ruƙya ta shari'a ta hanyar Alkur'ani da ingantattun addu'o'i, ba ta hanyar masu duba da bokan da ke ikirarin amfani da aljanu ba.

A karantarwar Sahihin Addininmu na Musulunci dai ba a yarda a tafi wurin irin waɗannan mutanen don neman magani ko wata buƙata irin wannan ba. Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

مَنْ أَتَي عَرَّافًا فَسَأَلَهُ عَنْ شَيْءٍ لَمْ تُقْبَلْ لَهُ صَلَاةُ أَرْبَعِينَ لَيْلَة

Duk wanda ya tafi wurin mai duba kuma ya tambaye shi a kan wani abu, to kuwa ba za a karɓi Sallolinsa na kwana arba’in ba!

(Muslim (5714) da Ahmad (16638) suka fitar da shi).

Watau kenan duk wanda ya tafi domin tambaya kawai, to ya yi asarar ladan sallolinsa guda ɗari biyu, watau: (5x40=200)!!

Wannan kuwa ba ƙaramar asara ba ce, in da mutane suna fahimta. Allaah ya ƙara mana fahimta.

Sannan kuma Manzon Allaah (Sallal Laahu ’Alaihi wa Aalihi wa Sallam) ya ce:

مَنْ أَتَى عَرَّافًا أَوْ كَاهِنًا فَصَدَّقَهُ بِمَا يَقُولُ فَقَدْ كَفَرَ بِمَا أُنْزِلَ عَلَى مُحَمَّدٍ

Duk wanda ya tafi wurin mai duba ko boka kuma ya gaskata shi a kan abin da yake faɗi, to haƙiƙa! Ya kafirce wa abin da aka saukar wa Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) (Ahmad da Al-Haakim ya riwaito shi, kuma As-Shaikh Al-Albaaniy ya inganta shi a cikin Sahih Al-Jaami: 5939).

A ƙaidar shariar musulunci kuwa duk wanda ya kafirce wa abin da aka saukar wa Annabi Muhammad (Sallal Laahu Alaihi wa Aalihi wa Sallam) bayan kuwa yana musulmi, to ya yi ridda kenan.

Idan wannan ne hukuncin wanda ya je wurin irin waɗannan mutanen, to ina kuma ga su kansu mutanen?!!

Allaah ya kiyashe mu, ya tsare mu daga hanyoyin hallaka.

Don haka, wajibi ne musulmi a duk inda yake ya nisanci duk abin da zai janyo masa naƙasa ko tawaya a cikin addininsa da imaninsa, balle kuma abin da zai iya lalata shi, ya ruguza shi. Allaah ya taimake mu.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments