𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum, malam. Muna godiya sosai da irin gudunmawar da kuke bayarwa ga addinin Allah. Muna da tambaya game da mijina wanda yake fama da matsalar saurin kawowa yayin jima'i, haka kuma azzakarinsa ba ya tashi sosai, kuma bayayinsa suna da kauri sosai. Mun yi ƙoƙari da yawa, mun yi amfani da shawarwarin da kuka ba mu a baya game da irin wannan matsala, amma har yanzu abin ya gagara. Muna neman wani taimako ko shawara daga gare ku, ko Allah Ya sa mu dace.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Matsalar saurin
kawowa da raunin azzakari daga cikin matsalolin da suke damun maza da yawa a
rayuwar aure, kuma tana iya zama da tushe daban-daban. A shari'ar Musulunci, an
yarda da neman magani ga kowace cuta, kamar yadda Manzon Allah (Sallallahu
Alaihi Wasallam) ya ce:
إِنَّ
اللَّهَ عَزَّ وَجَلَّ أَنْزَلَ الدَّوَاءَ وَأَنْزَلَ الدَّاءَ وَجَعَلَ لِكُلِّ
دَاءٍ دَوَاءً فَتَدَاوَوْا وَلَا تَدَاوَوْا بِحَرَامٍ
(Sunan Abi Dawud)
"Lalle Allah
Madaukakin Sarki Ya saukar da magani kuma Ya saukar da cuta, kuma Ya sanya wa
kowace cuta magani. Don haka ku nemi magani, amma kada ku nemi magani da
haramun."
Fahimtar Tushen
Matsala
Malamai sun bayyana
cewa matsalar saurin kawowa tana zuwa ta ɓangarori da dama. Wasu maza suna samun rauni
a jikinsu saboda yawan cin abinci mai ƙiba, mai yawan
sukari, ko kuma rashin motsa jiki. Wasu kuma, musamman a farkon aure, suna da ƙarfi sosai, amma
bayan ɗan lokaci sai suka
koma kan yanayin halittarsu ta asali. Akwai kuma wanda matsalar ta kasance ta
gado, wato halittarsa haka take a fannin jima'i . Don haka, kafin a fara
magani, ya kamata a fahimci tushen matsalar.
Magunguna Da
Shawarwari Na Shari'a
1. Motsa Jiki Da
Horar Da Jiki
Ya kamata mijinki ya
koya wasanni da motsa jiki na yau da kullum, musamman waɗanda ke ƙarfafa jiki kamar
motsa ƙafafu da ciki. Hakan zai taimaka masa ya sami ƙarfi da kuzari. Har
ila yau, ya koya dabarun saduwa da mace kafin jima'i, ta yadda matar za ta
gamsu kafin saduwa, kuma ko ya kawo dawuri, buƙatarta ta biya.
2. Yawaitar Jima'i
Wani shawarwari da
malamai ke bayarwa shi ne yawaitar yin jima'i. Idan mutum ya saba yin jima'i a
kullum, jikinsa zai saba da hakan, kuma matsalar saurin kawowa na iya raguwa.
Misali, idan ya sadu da matarsa da dare, sannan ya ƙara da asuba, kuma ya
ci gaba da hakan na tsawon sati biyu, zai iya samun gyara.
3. Magunguna Na
Halitta
Akwai wasu magunguna
na halitta waɗanda suka zo a cikin
littattafan likitancin gargajiya na Musulunci, kuma wasu malamai sun ba da
shawarar su. Daga cikinsu akwai:
Mazaƙutar raƙumi: a soya ta da man
jikinta, ba tare da an saka wani mai ba, sannan ya ci ta.
Furen dabino da garin
chitta: a nika su, a zuba su cikin ruwan zuma, ya rika sha.
Man jirjir: ya sha
cokali ɗaya da safe kafin ya
karya, da kuma da magariba. Wannan na iya ba shi ƙarfi da kauri.
Duk da haka, dole ne
a tuna cewa waɗannan magunguna ba su
da tabbaci a cikin Alkur'ani ko Sunnah, kuma shawarar da aka ba su ita ce ta
wasu malaman gargajiya. Mafi aminci shi ne a koma ga likitoci na zamani waɗanda suka ƙware a fannin lafiyar
jima'i, tare da neman magungunan da suka halatta kuma ba su da illa.
Abubuwan Da Ya Kamata
Ku Kauce Masa
1. Kauce wa
magungunan da ba a san tushensu ba ko kuma waɗanda ke ƙunshe da abubuwan
haramun.
2. Kada ku je wurin
bokaye ko masu duba don neman magani, domin wannan yana ɓata aqida kuma yana
kawo cutarwa mafi girma fiye da amfani. An yi kashedi game da masu duba da ke
yin maganganun gaibu da ba su da tushe .
3. Kada ku yi amfani
da ruqyah ta hanyar rubuta Alkur'ani a takarda sannan a nitsar da ruwa a sha
domin wannan ba shi da tushe a Sunnah, kamar yadda Sheikh Al-Albani ya faɗa . Hanyar ruqyah da
aka amince da ita ita ce karatun Alkur'ani da addu'o'in da suka zo daga Annabi.
Shawarwari Na Ƙarshe
1. Ku koma ga likita
na kwararre a fannin lafiyar jima'i don bincikar tushen matsalar.
2. Ku dage da ruqyah
shari'ah ta hanyar karatun Alkur'ani da addu'o'in Annabi.
3. Ku ci gaba da
kyautatawa a tsakanin ku, ku kiyaye soyayya da fahimtar juna.
4. Ku yi istigfari da
addu'a da yawa, ku roƙi Allah Ya warkar da mijinki.
WALLAHU A'ALAM (Allah
ne Mafi Sanin gaskiya).
Ina roƙon Allah Ya warkar da
mijinki, Ya ba shi ƙarfi da kuzari, kuma Ya sanya zaman aure cikin ni'ima da
kwanciyar hankali. Idan kuna da ƙarin tambaya, to,
muna maraba da ku a kowane lokaci.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.