Article Citation: Muhammad Musa Yankara (2020). Kare Mutuncin Kai a Rubutattun Waƙoƙin Hausa: Nazari Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Ɗahiru Musa Jahun Bauchi. DEGEL: The Journal of the Faculty of Arts and Islamic Studies, Vol. 18, No. 1. ISSN 0794-9316
KARE
MUTUNCIN KAI A RUBUTATTUN WAƘOƘIN HAUSA: NAZARI CIKIN WASU WAƘOƘIN ALHAJI ƊAHIRU MUSA JAHUN BAUCHI
(O.F.R)
Na
Muhammad
Musa Yankara
Tsakure
Mutunci ya haɗa da sanin darajar mutane har ma da dabbobi, bai taƙaita ga manya ko shugabanni ba. Kowane
cikakken mutum mai hankali yana iya zama mai mutunci a tsakanin mutane. Mutunci
ya ƙunshi ladabi, da biyayya,
da girmamawa, da darajantawa, da tsare mutuncin kai, tare da kare haƙƙin ɗan adam. Haka kuma, dattijantaka, da jin kunya, da yin abu cikin
girma da arziki, da gaisuwa sukan shiga cikin mutunci. Wannan takarda za ta
mayar da hankali ne, a kan halayen kare mutuncin kai a cikin rubutattun waƙoƙin
Hausa na Alhaji Ɗahiru
Musa Jahun Bauchi (O.F.R). A cikin waƙoƙin, Sha’irin ya yi ƙoƙarin
bayyana matakan tarbiyyanta da kyawawan halayen da mutane za su iya amfani da
su wajen kare mutuncin kansu, domin tsira da mutunci wanda ya fi tsira da
dukiya.
Gabatarwa
Masana adabin Hausa, sun yi ittifaƙin cewa rubutattun waƙoƙi a ƙasar Hausa sun samo asali ne daga addinin Musulunci, domin
sakamakon zuwan addinin ne aka sami manyan malamai suka fara rubuta waƙoƙin
da suka shafi addini na Musulunci (Bugaje, 2011). Ire-iren waɗannan waƙoƙi kuwa, cike suke da saƙonni daban-daban waɗanda suka shafi tarbiyyar jama’a, kodai, domin koyar da su ibadu,
ko kuma, domin faɗakar da su da yi masu
wa’azi dangane da abin da ya shafi duniyarsu da lahirarsu. Tsinkayar waɗansu abubuwa da suka shafi tarbiyyantar da mutane, kyawawan
halaye, da kare mutuncin kai a cikin wasu waƙoƙin Alhaji Ɗahiru Musa Jahun Bauchi (OFR), ya sa za a
nazarce su ta hanyar fito da wuraren da yake kira da su, domin samun kariyar
mutunci.
Wane ne Alhaji Ɗahiru Musa Jahun Bauchi (OFR)
An
haifi Alhaji Ɗahiru Musa Jahun a
tsakanin shekarar 1941 zuwa 1942, kusan shekaru 75 ke nan da suka gabata, a
unguwar Jahun da ke cikin garin Bauchi. Alhaji Ɗahiru Musa Jahun ya fara karatun Muhammadiyya a wata makarantar Islamiyya
ta Malam Ladan, a unguwar Kur da ke cikin garin Bauchi. Daga baya aka mayar da
shi makarantar malam Maigari, bayan da ya kai suratul sabbi a makarantarsa, sai
aka cire shi aka kai shi makarantar malam Baƙo inda ya kai suratul tabara. Alhaji Ɗahiru Musa Jahun Bauchi (OFR) ya koma hannun babban yayansa da karatu, inda
cikin shekaru biyu ya sauke Alƙur’ani mai tsarki. Bayan
ya zama matashi, sai ya tafi yawon buɗe ido a garin Gombe inda ya haɗu da
wani malami mai suna malam Murshidi wanda a hannunsa ya ƙara faɗaɗa karatunsa na addini. Dangane da ilimin boko kuwa, an barshi a baya duk da sha’awar da
yake da shi. Sai dai ya koyi haɗa haruffa a wajen abokansa
wanda hakan ya sa ya iya rubutu da karatun Hausa sosai.
Alhaji Ɗahiru Musa Jahun ya faɗa da bakinsa cewa, bai gaji waƙa ba, domin shi jinin sarauta ne, kuma iyayensa ba mawaƙa ba ne, malamai ne. Allah ne ya yi masa
baiwa ta shirya waƙa da kuma sha’war da yake
yi da ita, wanda hakan ya sa ya tsunduma cikin wannan aiki. Ya ce ya zaɓi waƙa fiye da sana’o’in da
yake yi, saboda ya fi ba ta muhimmanci a cikin zuciyarsa, kuma muddin yana da
rai ba zai bar rubuta waƙa
ba.
A halin yanzu,
Alhaji Ɗahiru Musa Jahun Bauchi
(OFR) yana zaune ne a cikin garin Bauchi a Unguwar Jahun layin Liman Muhammadu
Mai Rasuwa, kamar yadda yake faɗa da bakinsa a cikin waƙar ‘Wasu Na Ce Kansu Ya Waye’ a baiti na 77,
79 da 80 da cewa;
To, mai neman garin da nake,
Nan BAUCHI a nan gidanmu yake,
Kuma JAHUN unguwar da nake,
In na zaga in zo in fake,
Jama’a
ba su san ni sosai ba.
Adireshina
ga mai nema,
JAHUN ƙofar Galadima,
Nurul-Islami ke da zama,
Makaranta
ce ta Islama,
Ba
don fahari na zanta ba.
Ni ɗan
MUSA a nan na tsaya,
Ni ƊAHIRU ba sani ga niya,
Nan zan ɗan dakata in tsaya,
Kafin in wuce in ɗan tafiya,
In Allah bai taƙaita
ba.
Ma’anar
Kare Mutuncin Kai
Masana da manazarta sun yi tsokaci daban-daban dangane da ma’anar
mutunci inda wasu suke ganin, Mutunci a nahawu yana da matsayin ɓoyayyen suna, wanda kan tsira daga suna gama-gari ko
sifa, waɗanda a kusan kodayaushe suke nuna hali ko sigar suna ko siffanta,
sannan wasu ɓoyayyun sunan suna
da ɗafa-ƙeya -ci wasu –ta wasu -taka,
sai dai masu ɗafa ƙeya -ci maza ne sauran kuma
mata. Don haka, mutunci da mutuntaka sun tsira daga mutum, mutuntaka ta ƙunshi mutunci da karrama mutane, mutunci kuma
shi ne nagarta ko kamala (Newman, 2000:5 &12).
Har wa yau,
tushen mutunci da mutum ɗaya ne, domin mutunci ya
haɗa da mutuntaka, wato sanin darajar kowane mutum. Sannan kuma
mutunci ya sha bamban da ladabi, domin shi ladabi ɗabi’a ne na girmama manya (Kirk-Greene, 1973:10-11).
Babu shakka
mutunci ya ƙunshi sanin darajar mutane
har ma da dabbobi sannan kuma bai taƙaita
ga manya ko shugabanni ba, kowane cikakken mutum mai hankali (yaro ko babba,
saraki ko talaka) yana iya zama mai mutunci a tsakanin mutane. Mutunci ya ƙunshi ladabi da biyayya da girmamawa da
darajtawa da tsare mutuncin kai, tare kuma da kare haƙƙin wani. Haka kuma,
dattijantaka da jin kunya da yin abu cikin girma da arziki, a wani lokaci hatta
gaisuwa takan shiga cikin mutunci (Newman, 1997:229).
Mutunci shi ne
mutum ya saba wa kansa da kiyaye halaye mafiya kyau da cika. Wato kada ka
aikata wulaƙantaccen abu. Kada ka nuna
halin ƙasƙanci wanda zai rage darajarka ka zama ba ka
da girma wurin ‘yan uwa (Abubakar 1966:21).
Sanin darajar
kai da tsare kai da kuma tsare mutuncin sauran mutane yana daga cikin mutunci,
musamman idan aka daraja su saboda shekarunsu ko iliminsu ko kuma saboda
kasancewar su mutane. Mutunci shi ne mutum ya ji kunyar aikata duk wani abin da
zai zubar masa da darajarsa, sannan kuma kowane mutum ya kare haƙƙoƙin abokin zamansa ko mu’amalarsa, ya tausaya
a lokacin da ya kamata ya tausaya, kuma ya taimaka wa mutane gwargwadon hali a
kan abin da ya kamata ya taimaka, kasancewar mutunci ya ƙunshi bai wa mutane haƙƙinsu, wato shugaba ya
mutunta talakawansa, talakawa su mutunta shugabansu ta hanyar biyayya da yi
musa ɗa’a a rayuwa. Saboda martabar mutunci a
rayuwa ce Hausawa suke cewa:
Mutunci ya fi kuɗi.
Mutunci
riga.
Mutunci
madara (ne).
Ta la’akari da abin da ya gabata, an fahimci cewa mutunci
abu ne mai kyau da kusan kowane mutum yake maraba da shi, domin yana taimaka wa
zaman lafiya ya tabbata, tare da ɗaukaka darajar al’umma kamar yadda tufafi kan
suturta mutum, abinci kan kyautata lafiyar jiki a sami kuzari. Mutunci
yakan ƙarfafi darajar mutum da kuma al’umma
baki ɗaya. Mai mutunci mutum ne mai kunya da ƙwazo da himma wajen dogaro da kai da kauce wa zaman banza ga kishin kai da
na al’ummarsa. Kusan kodayaushe mai mutunci yana kasancewa mai iya bakinsa da
kamewa a tsakaninsa da mutane kamar yadda misalin haka ya zo a waƙar Alhaji Ɗahiru Musa Jahun ta
Tarbiyya II inda a baiti na 103 da 113 yake cewa:
103.
Dama mutunci ne mutun,
In ba
mutunci ba mutun,
Mai
hankali ka riƙe batun,
Ladabi da ɗa’a tarbiya.
113.
Bari nuna kai ɗan wane ne,
Ko
don a ce kai wane ne,
Kowanmu ai ɗan wane ne,
Don kar ka ja mana tankiya.
(Jahun: Waƙar Tarbiyya
II)
Halayen Kare
Mutuncin Kai Daga Bakin Alhaji Ɗahiru Musa Jahun Bauchi (OFR)
Kamar yadda ya
gabata tun daga farko cewa, kare mutuncin kai abu ne wanda ya shafi kunya da
dogaro da kai da kuma kiyaye harshe. Saboda haka, a nan za a kawo yadda
Alhaji Ɗahiru Musa Jahun ya
sarrafa waɗannan halaye a cikin waƙoƙinsa,
domin inganta tarbiyyar al’umma da samar mata da rayuwa mai inganci.
Kunya
Kunya kamar
yadda Yahya da wasu (1992:82) suka bayyana “ta ƙunshi hana harshe yin munanan maganganu
da ƙiya wa gaɓoɓin jikin mutum aikata miyagun ayyuka.
A wata ma’anar
kuma, Ibrahim (2009:62) cewa ta yi, “Kunya na nufin jin nauyi da girmamawa ko
karamcin da ake yi wa na gaba da mutum ko masoyi ko ‘ya’ya ko surukai ko baƙo.
Kunya na nufin
halin ɗa’a da kawaici ko a aikace ko a magance.
Kunya ɗabi’a ce kyakkyawa da kan jawo wa mai ita
daraja da girmamawa a cikin mutane (Garba 2010:20).
Kunya tana matuƙar taka rawa wajen nuna zurfin kiyaye
mutuncin kai da cikar kamala da halayen ƙwarai na mutum, domin siffa ce daga cikin siffofin da ake gane
mutum mai tarbiyya da ita. Musulunci addini ne da ya wajabta yin kunya, domin
kuwa hadisin Annabi (S.A.W) yana nuni da muhimmancin kunya cikin addini inda
yake cewa, “Kunya tana daga cikin imani”.
A game da abin
da ya yi kama da bayanin da ya gabata, Alhaji Ɗahiru Musa Jahun Bauchi ya kawo wani baiti
yana mai yin kira da jin kunya ga mutane da cewa:
49. ‘Yan acaɓa ku inganta halinku,
Mai biɗar arziki bai rashin kunya.
51. Don waɗansunku kan sa a zarge ku,
Ga rashin hankali ga rashin kunya.
53.
Masu tuƙi na mota waɗansun
su,
Kan gwada ba mutunci bare
kunya.
85.
Gyara kaya tuni ne ga matanmu,
Kar a faɗa tafarkin rashin kunya.
(Jahun: Waƙar Gyara
kayanka Bakandamiya).
A nan Sha’irin
yana gargaɗin ‘yan achaɓa da direbobi da su kula
da muhimmancin kunya, domin rashin kunya yake kawo rashin hankali har jama’a
su ƙyamaci mutum. Daman
an ce da wuya a yi ɓarin gari a kwashe duka.
Wannan ya sa Hausawa suke ganin duk wanda ya bari mutuncinsa ya salwanta,
to ƙimarsa za ta ragu a idon
jama’a.
Har ila yau
marubucin ya sake bayyana cewa rashin kunya ba ya haifar da ɗa’a mai idanu a cikin al’umma domin shi ke jawo dukkan fitinu inda
yake cewa:
Raya ɗa’a
mu inganta tarbiyya,
Sai
mutunci da yarda da soyayya,
Ba rashin tausayi ba rashin kunya,
Ai shirin farfaɗowa da tarbiya.
71. Tunda an gane cewa rashin kunya,
Shi ka jawo ababen shiga kunya,
‘Yan tsirari masoya rashin kunya,
Ba su ƙaunar
a maido da tarbiya.
(Jahun: Waƙar Yaƙi da Munanan Ɗabi’u).
Kamar yadda
baitocin suka nuna, kunya ita ce mabuɗin alheri saɓanin rashin kunya da ke jawo tsiya da sharri. Sha’irin ya hori
al’umma da su zama masu kunya saboda, matuƙar
ana son wanzuwar zaman lafiya a cikin al’umma sai an kiyaye aikata abubuwan
rashin kunya, domin kunya ƙofa
ce da ke jawo soyayyar mutane da kare mutuncin kai da yin jagoranci ga dukan
alheri.
Alhaji Ɗahiru Musa Jahun Bauchi (OFR) ya kawo wasu
baituka masu kira da kyautata sutura, kasancewar kunya ta haɗa da rufe tsiraici da cewa:
108. Suturar jikinki ta yalwata,
Surar jikinmu ya ɗan ɓata,
Da wuya a ce an kunyata,
In an bi hanyar gaskiya.
109. Suturar jiki ko ko ado,
Mu bi dai shari’a gwargwado,
In ba mu jin kunyar ido,
Ai a ji kunyar tarbiya.
(Jahun: Waƙar Tarbiyya
II)
Lulluɓi na ɗaya daga cikin
kyawawan ɗabi’un da Musulunci ya kawo wanda yake kare
jama’a daga cin zarafi da matsalolin da sukan shiga a sakamakon bayyana
tsiraicinsu. Wannan kyakkyawar ɗabi’a ta fara rauni
tsakanin al’umma musamman mata, domin sun fara watsi da kariyar da Allah maɗaukakin sarki da ya tanadar musu. Wasu mata sun zaɓi su riƙa yawo tamkar tsirara suke
da sunan gayu ko wayewa, wanda mafi yawan abubuwan da suke jawo ɓarna a wannan zamani ya haɗa da bayyanar da tsiraici.
Bayyanar da tsiraici da rashin kunya suna taka muhimmiyar rawa sosai wajen
lalacewar al’umma musammam matasa. Don haka ne Sha’irin
yake gargaɗin jama’a da su riƙa suturce jikinsu da
sutura mai kyau, su ɓoye adonsu don kar a kunyata. Ba wai a cikin addinin
Musulunci kaɗai ba, har a gargajiyar Bahaushe an yi imani da cewa ba mai bayyanar da
tsiraicinsa sai marar tarbiyya. Saboda haka ne ma tun kafin bayyanar Musulunci
Hausawa suke suturce jikinsu da abubuwa daban-daban domin kare mutuncin kansu
da na iyalinsu.
Haka kuma, a cikin waqar Gyara Kayanka yana cewa;
23.
Lakcaran Jami’a ko mu ce tica,
Mun yi fatan a inganta tarbiyya.
24.
Don sifofi ɗabi’un waɗansun ku,
Kan gwada ba su daidai da tarbiyya.
25.
Tun da yara sukan ɗau sifar malam,
Bar fitowa da siffar
rashin kunya.
(Jahun: Waƙar Gyara
kayanka Bakandamiya)
Sha’irin yana
kira ga malaman makarantun Islamiyya da na boko a kan su gyara halayensu, domin
kada yara su kwaikwayi miyagun halaye da ɗabi’u daga gare su
kasantuwar cewa halayen Turawa sun yi tasiri a wurin al’ummar Hausawa ta yadda
suke kwaikwayon dukan ɗabi’u da halayensu. Wannan
ya sa har a fannin ilimi malamai masu koyarwa kan so nuna wayewa ta zamani
ga ɗalibansu, wanda hakan kuwa zubar da mutunci ne. Don haka ma damar
mutum yana son kowa ya ga ƙimarsa
da darajarsa a cikin al’umma dole ne sai ya tsare mutuncinsa ta hanyar kyautata
suturarsa.
Dogaro da Kai
Masu iya magana
suna cewa "Dogaro da kai jari". Wannan yana nufin himma ko ƙwazo cikin al’amura don kai wa ga cim ma buri
da buƙata, da kuma tashi daga
ragwanci da karayar zuciya da danƙwafewa
a wuri ɗaya (Yankara 2018). Tarbiyyantar da jama’a
dangane da dogaro da kai abu ne muhimmi da ke nuna ƙololuwar kare mutuncin kai, domin yana rage
zaman banza da sace-sace ga matasa da shaye-shaye wanda hakan ya sa
Alhaji Ɗahiru Musa Jahun a cikin
waqoqinsa yake cewa:
103. Komai kake nema kuwa,
Yi ta ƙoƙari zai samuwa,
Mai gaskiya bai damuwa,
Kai
dai ka zam mai tarbiya.
104.
Hanyan abinci a sunkuya,
Ka
biɗe ta ko ta cikin ƙaya,
Ko
da anai maka dariya,
Kai
dai ka nemi halaliya.
(Jahun:
Waƙar Tarbiyya III)
Zance na haqiqa shi ne, wannan Sha’irin yana qoqarin
nunawa mutane tarbiyya da kare mutuncin kai ne ta hanyar nuna muhimmancin neman
na kai da yin hani ga zama cima-zaune. Neman na kai yana tare da wahalhalun da
dole sai an jure an shanye su, don duk wanda aka ga ya zage damtse wajen neman
na shi, to mutane na yi masa hukunci da mutum mai tarbiyya da kamun kai, wanda
ba ya qwallafa rai ga na wani. Haka kuma ba zai takura wa sauran jama’a ba,
domin na wani bai rufe masa idanu ba.
Dubi wani
misalin da Sha’irin yake cewa;
5. Ya kamata da kanmu mu dogara,
Duk wuya mu ɗamartu mu zabura,
Mui shiri sosai mu yi ɗammara,
Nuna
kishi sai mun dogara,
Mu
da kanmu mutan Najeriya.
(Jahun:
Waƙar Yaƙi da Rashin Ɗa’a MAMSER)
Sha’irin yana nuni da cewa kishin ƙasa bai taɓa yiwu wa sai al’umma ta dogara da kanta. Dogara da kai ɗin
nan kuwa ya haɗa da muhimmantar da sana’o’i da inganta su da kuma kyautata su. Muhimmantar
da sana’a da yin gaskiya abin alfahari ne ga duk wani mutumin kirki a ƙasar Hausa. Mutum yakan yi mutunci a idon abokan mu’amalarsa kuma, nuna
halin kirki ga ɗaiɗaikun mutanen gari yana taimaka wa zaman gaskiya da
amana. Haka
kuma, adalci yakan ɗore a kowane al’amari,
sannan ƙasa takan ginu ta ɗore a kan gaskiya.
Kowace sana’a ta neman halas tana da ƙima da daraja, kuma ana son a kyautata ta. Bahaushe bai yarda da zaman
banza ba. Mutum ya zama raggo, kasalalle ba shi da muhalli a cikin rayuwar
Hausawa. A kullum kiran da suke yi wa junansu na a tashi tsaye ne a sami abin
yi, a dogara da kai, ba sai an jira wani ya yi wa mutum hidima ba (Yahaya da
wasu, 2006).
Don muhimmantar da neman halas da dogaro da kai,
Alhaji Ɗahiru ya nuna hatta Musulunci ya yi umurni da
hakan inda yake cewa:
15.
Tuni addini ma na kira,
Cewa
mai rai ya yi ɗammara,
Ya ga kansa da kansa ya dogara,
Abu
ne daga Allah ƙaddara,
Shan daɗi ko kuma shan wuya.
16. In dai ba ya zama dole ba,
Bai
kyautu ka ƙallafa ranka ba,
Ga
mutane don roƙonsu ba,
Nemi
‘yar sana’arka ka jarraba,
Ko ta
yiwu buƙata ta biya.
17.
Kar ka yarda zaman banzan gari,
Ko
ko ɓata garin jama’ar wuri,
Sai baƙin aiki ba swa fari,
Sai
yawan ce ba su da ko ɗari,
Don
nuna macewar zuciya.
18.
Sana’o’i sun wuce ƙirguwa,
Wanda
za ka yi domin ƙaruwa,
In har ka yi ne ta ƙi
samuwa,
Nan in ka nemi gudummuwa,
Babu laifi ɗan Najeriya.
(Jahun: Waƙar Yaƙi da Rashin Ɗa’a MAMSER)
Marubucin
wannan waƙa ya bayyana dukan ɗabi’u da halayen masu zaman banza. Ya bayyana su da cewa rashin
abin yi na kawo macewar zuciya har mutum ya zama maroƙi, ko ya zama lalatacce mai burin lalata
wasu. Idan kuwa har al’umma na son tsira da mutumci, to, lallai sai an kawar da
lalaci an haɗa kai wuri ɗaya, kowa ya ga ya samu ‘yar sana’a, don kuwa sana’o’i suna da
matuƙar yawa. Wato mutum ya
tsaya ya nemi na kansa, domin biyan dukan buƙatarsa kar ya zama ci-ma-zaune a cikin al’umma. Kuma ko a wurin
neman ma, to dole sai an kiyaye da haram da halal, ko abin da zai zubar da
mutunci a idon sauran jama’a. Duk da yake Bahaushe yana sane da fifikon darajar
da Allah ya yi wa mutane ta fuskokin rayuwa, kuma kusan kowa yana martaba kansa
da sana’arsa, kasancewar ba su gamsu da zaman banza ba. Don haka mutumin da duk
yake da ingantacciyar sana’a kuma ya riƙe
ta da muhimmanci yakan yi daraja da ƙima
daidai gwargwado a idon mutane.
Kiyaye Harshe
Bunza (2013) a
cikin wata maƙala da ya gabatar ya fara
da karin maganar da yake cewa, baki abin magana! Duk da irin fa’idar da ke ga
bakin mutum, adabin Bahaushe sai da ya yi horo da kame shi. Ba shakka, baki abu
ne muhimmi. Da baki ne mutum ke bayyana kansa a san shi a san cinikinsa. Duk
mutumin da yake da baki, ya fi sauƙin
mu’amala da mutane a fahimce shi. Hasali ma, duk yawancin mu’amalar mutane ta
cinikayya da neman ilimi da addini da siyasa da neman abinci da sauransu ta
baki ake yin su a sauƙaƙe. Mai baki ake sanyawa gaba domin isar da saƙon al’umma na kyautata tarbiyyar jama’a da
kuma kyautata musu. Duk da irin wannan fa’idar ta baki, sai da aka shigo cikin
adabi domin jan kunnen jama’a don su san yadda za su yi amfani da bakinsu a
wajen maganganunsu na yau da gobe.
Harshe
wani ɓangare ne da yake tabbatar da
mutuntakar ɗan’Adam, kuma da shi
ne ɗan’Adam kan fahimci manufar abokin zancensa. Har wa yau, harshe ne
maƙunsar tunanin ɗan’Adam, kuma rayuwa ba ta kammala idan babu shi. Saboda haka, duk
inda mutum biyu ko fiye da haka suka haɗu za a same su suna
zantawa da juna (Pinker, 2007:3&419). Allah ya yi wa mutum baiwar harshe
saboda ya cin ma muradin rayuwarsa. Kuma nagarta da ƙeta fitattun ɗabi’un ɗan’Adam ne, kuma mutum ya
sami gagarumar nasara a rayuwarsa, musamman yadda zamantakewarsa da danginsa da
sauran jama’ar gari take gudana (Aristotle, 2002:468).
Masu hikimar
magana suna cewa "abin da ya taɓa hanci, to, saƙon kan isa zuwa idanuwa". Alhaji Ɗahiru Musa Jahun yana cewa:
38. Jita-jitan da ba ta da alheri,
Daina yaɗa ta domin gudun sharri,
Kame baki a kan ayyukan sirri,
Don gudun yaɗa ƙarya abin kunya.
(Jahun: Waƙar Yaƙi da Munanan Ɗabi’u)
Falsafar da
take cikin wannan baiti ita ce, mutum ya zama mai kiyaye harshensa ta hanyar
barin abin da bai dame shi ba. Da kuma guje wa yaɗa ƙarya da jita-jita wanda yake zubar da ƙimar mutum da wargaza masa tarbiyya.
A wani wuri
kuma Alhaji Ɗahiru Musa Jahun saƙo yake ba mahajjata dangane da kame baki da
cewa:
16. Daina sharri, surutu yawan musu,
Ko ƙarairai
a nan ko a can Hajji.
17. Bar shiga kantuna ko yawan yawo,
Don raɗa, jita-jita kuna Hajji.
(Jahun: Waƙar Bankwana
da Alhazan Bauchi)
Halayyar wasu
mutane ita ce, ɗaukar maganar wani a kai
ta zuwa ga wani. Wannan halayya tana ɓata tarbiyya da rusa
zamantakewa, kuma Sha’irin ya tabbatar har a cikin ayyukan ibada ana yin irin
wannan hali. Don haka sai ya kwaɓi al’umma da su guje
wa ƙarya da raɗa da yaɗa jita-jita a wurin sauke
faralin da ya hau kansu na addini. Ƙarshe
kuma sai ya naɗe bayanin sa da nuna wa jama’a cewa ɗaukar gulmace-gulmace da yawo da tsegumi na jefa ƙasa cikin halin ruɗani da zullumi. Saboda haka matuƙar ba yaƙar
wannan aka yi ba, al’umma ba za ta samu zaman lafiya ba. Ga abin da yake cewa:
37. Shirin gyara kaya tana gangami,
A bar ƙulle-ƙulle da ɗaukan ɗumi[1],
A kan
jita-jita da tsaigungumi[2],
Na
jawo ma juna zaman zullumi[3],
Ta ƙarya da sharri da gardandami[4],
Mu
himmatu don sanya takunkumi[5],
A kan ‘yan ta’adda da ke shan tsumi[6],
Suna kashe juna ana tsegumi,
A ƙarshe su bar mu da
sallallami,
Kamar shugabanni suna rurrumi[7],
Ku
amsa kiran gwamnatin malami,
Mu sa
ma wa kanmu zaman lafiya.
(Jahun:
Waƙar Tarbiya da Zaman Lafiya).
Wannan baiti ya tattaro abubuwa masu yawa dangane da
illar rashin kame baki da kiyaye harshe. Sha’irin ya nuna wannan ɗabi’a
tana haifar wa da ƙasa zullumi da
zaman ɗar-ɗar[8] a tsakanin mutane. Saboda muhimmanci
kame baki da kiyaye harshe ya sa a rayuwa ya sa gargajiyar Bahaushe ta
tsani ƙarya da tsegumi da gulma da yi da mutane,
kasancewar suna kawo tarnaƙi wajen kyautata
tarbiyya. Maimakon haka, Bahaushe tun a zaman gargajiya ya yi amanna da tsare
mutumcinsa da faɗin abin da in an je an dawo zai ce shi ne kuma ba ya jin tsoro ko kunyar
maimaitawa.
Wannan shi ya sa Alhaji Ɗahiru Musa Jahun yake tunatar da manya cewa:
8.
Jama’a in za ku yarda da ni,
Da sai in faɗi a nawa gani,
Magana
mai kyau da mai muni,
Manya ku ad da ji da gani,
Ku jiye ku gane wa ‘yan yara.
(Jahun: Waƙar Ranar
Yara)
Hikimar da take
cikin wannan baiti ita ce, kame baki musamman ga manya wajen faɗin miyagun maganganu da suka shafi batsa da rashin kunya a gaban
yara, domin zuciyar yaro kamar mayen ƙarfe
(kura) ce da take naɗe abu cikin ƙanƙanin
lokaci. Hakan ya sa har karin magana masu alaƙa da kame baki suka bayyana a zantukan
Hausawa kamar:
Baki
ke yanka wuya
Shegen mutum, bakinsa
Ga bakin wawa akan ji magana
Halshen
mutum, zakinsa
In ka
ga baki da tsawo na mai gardama ne
Maganar
duniya iyawa ce, in ka ji ta kama bakinka
Kurum
ta raba ka da kowa.
Kammalawa
Wannan maƙala ta yi ƙoƙari wajen tattaro bayanai masu ba da haske
kan hanyoyin kare mutuncin kai, domin inganta tarbiyyar al’umma a cikin wasu
rubutattun Waƙoƙin Alhaji Ɗahiru Musa Jahun Bauchi
(OFR). Abubuwan da aka samu sun haɗa da kunya da dogaro da kai da kuma kiyaye
harshe ko kame baki. Wannan kuwa wani yunƙuri
ne na nuna muhimmancin waƙoƙin Hausa wajen kyautata tarbiyyar al’umma da wanzar da zaman lafiya da kawo
ci gaban ƙasa.
Manazarta
Adamawa, A. (2007). Sirrin Kamalah. Bauchi: Adamawa
Media Link.
Adamu, A. U. (2000). “Tarbiyyar Bahaushe, Mutumin Kirki and Hausa
Prose Fiction: Towards an Analytical Framework”. A Seminar Paper Presented in
the Department of English and European Languages. Kano: Bayero University.
Ahmad, I. (2003). Lessons For Every Sensible Person.
Madina Munawwara: Alrasheed Printers.
Ainu, H. A. (2013). ‘Sauye-sauyen Zamani A Cikin Rubutattun Waƙoƙin
Hausa: Misali Daga Jigon Madahu’. Cikin: Ɗunɗaye Journal of Hausa
studies, Vol. 1, No. 6. Sokoto: Department of Nigerian Languages, Usmanu Ɗanfodiyo University.
Amfani, A. H. (2011). “Hausa da Hausawa: Jiya da Yau da Gobe”. One
Day Symposium. Zaria: Ahmadu Bello University.
Amin, M. L. (2002). “The Hausa Metaphysical worldview:
A Paremiological Exposition”. Ph.D Dessertation. Zaria: Department of Nigerian
and African Languages, Ahmadu Bello University.
Bugaje,
H.M. (ND). ‘Hankali da Lura: Matsayinsu da Muhimmancinsu a Rayuwar Hausawa’. Muƙalar da aka gabatar a taron ƙara
wa juna sani. Zariya: Sashen Harsuna da Al’adun Afirka, Jami’ar Ahmadu Bello.
Bugaje,
H. M. (2011). “Wa’azi A Rubutattun Waƙoƙin Mata Na Ƙarni Na Ashirin”. Kundin Digiri Na Biyu.
Zaria: Sashen Harsunan Nijeriya da Afrika. Jami’ar Ahmadu Bello.
Bugaje, H. M. (2013). “Tarbiyya da Zamantakewar
Hausawa: Jiya da Yau”. In: Excerpts of International Conference On (Taɓarɓarewar Al’adun Hausawa)
The Deterioration of Hausa Culture Organized by Katsina State History and Culture Bureau in
Collaboration with Umaru Musa ‘Yar’adua University, Katsina.
Bunza, A.M. (2002). Yaƙi Da Rashin Tarbiya,
Lalaci, Cin Hanci Da Karɓar Rashawa Cikin Waƙoƙin Alhaji Muhammadu Sambo
Wali Basakkwace. Lagos: Ibrash Islamic Publications Centre Ltd.
CNHN, (2006). Ƙamusun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press.
Ɗangambo,
A. (1974). ‘Nazari Kan Nagari Nakowa’. In: Harsunan Nijeriya, Vol.
1 No. IV. Kano: Department of Nigerian Languages Bayero
University.
Xangambo, A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da
muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kano: Triumph Publishing Company
Limited.
Yankara, M. M. (2018). "Tarken Tarbiyya A Cikin Wasu Waƙoƙin
Alhaji Dahiru Musa Jahun Bauchi (OFR)". Kundin Digiri Na Biyu. Sakkwato:
Sashen Harsunan Najeriya. Jami'ar Usmanu Danfodiyo.
[1] Kalma ce ta Sakkwatanci wadda ke nufin
surutu ko magana
[2] Jam’i ne na tsegumi wato ƙorafe-ƙorafe
[3] Zaman zullumi na nufin zaman fargaba
[4] Jam’i ne na kalmar gardama, wato maganganun da ba su da
amfani
[5] Asalinsa abin da ake rufe bakin dabba
ne don kar ta yi ɓarna. Yanzu ana
amfani da kalmar a matsayin hana walwala ko kuma watayawa
[6] Tsumi na nufin magani na garkuwa don tsari ko abokan gaba
[7] Nau’i ne na barci da ake yi idan an yi aiki an gaji, sai
a ɗan kwanta zuwa wani lokaci taƙaitacce
[8] Daidai da ma’anar ɗuri na 36
The official website of the DEGEL Jounal is https://www.degeljournal.com

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.