Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Miji Ya Yi Tafiya Sama Da Wata Hudu Ba Tare Da Ya Dawo Zuwa Ga Iyalinsa Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Malam dan Allah wani abu ne yake damu na nake neman mafuta mijina matafiyi ne yana tafiya neman abinci yakan yi wata uku sannan ya zo amman kamin wata ukun nakan ji kewarsa tana damu na idan na kira sa na gaya masa sai ya ce min na yi hakuri daga wannan ba wata magana mai dadi da za ta samarmin nutsuwa nanuna masa cewa ni fa maca ce ina da bukatar kulawarsa babu wani wanda Allah ya halattamin na nemi kulawa a gurinsa in bashi ba amman har yanzu ya ki ganewa na ce ya tafi da ni ya ki kuma in ya zo ba ya dadewa dadewarsa kwana biyu wallahi malam na rasa yanda zan yi bana san fadawa cikin wani yana yi na saɓon Allah Dan Allah malam kabani shawara na gode  😭😭😭😭

HUKUNCIN MIJI YA YI TAFIYA SAMA DA WATA HUƊU (4) BA TARE DA YA DAWO ZUWA GA IYALINSA BA

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

wa'alaikumussalam. To yar'uwa kamar yadda malamai sukace; Baya halatta miji yayi tafiya sama da wata huɗu ba tare da ya dawo zuwa ga iyalinsa ba, hakanan koda wani dalili na Shari'a yasa mijin yana gari sai ya kaurace mata da nufin yi mata horo na ladabtarwa to bai halatta ya kaurace mata sama da wata huɗu ba kamar yadda aya ta 226 ta cikin suratul Baƙara ta yi bayani:

لِّـلَّذِيۡنَ يُؤۡلُوۡنَ مِنۡ نِّسَآٮِٕهِمۡ تَرَبُّصُ اَرۡبَعَةِ اَشۡهُرٍۚ فَاِنۡ فَآءُوۡ فَاِنَّ اللّٰهَ غَفُوۡرٌ رَّحِيۡمٌ‏

Ga waɗanda suke yin rantsuwa daga matansu akwai jinkirin wata huɗu. To, idan sun kõma, to, lalle ne Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai.

Sabida haka ýar'uwa mafi yawan malamai sun tafi akan fahimtar cewa: mata na iya hakuri da jima'i tsawon watanni huɗu. Wannan yasa idan miji matafiyi ne matukar baya haura wata huɗu ba tare da ya dawo ga iyalinsa ba, To Shari'a ba ta zarginsa da danne mata hakki na ɓangaren jima'i, illah iyaka idan yana barinsu da yunwa baya wadatar dasu da abinci ruwan sha da sauran abubuwan rayuwa da suke bukata baya nuna kulawarsa garesu to wannan ya wuce iyakar Shari'a.

Sabida haka baiwar Allah tunda dai Allah ya ƙaddara miki miji mai tafiye-tafiye ne akwai bukatar ki sanya hakuri tunda har baya haura watanni huɗu matukar dai yana ciyar daku da kula da lafiyarku har zuwa lokacinda yake dawowa to kina iya hakuri da hakan.

Sannan ki koma zuwa ga Allah kiyi ta rokonsa ta hanyar ambatonsa kiyi ta kai kukanki ga Allah maɗaukakin sarki Sannan ki dinga yiwa mijin Addu'a Allah ya kawo masa wata kofar samu wacce zai dawo mazaunin gida ya dinga harkokinsa a gida maimakon tafiye-tafiyen.

Sannan babu laifi kina iya sanar da manyanku cewa kina bukatarsa a kusa dake in sha Allahu zasu ja hankalinsa akan ya tafi dake kuma wannan shi ne abinda yafi alkhairi matukar dai yana da halinda zai mallaki muhalli ko ya kama hayar muhalli a can garinda yake neman, ko kuma ya dinga kara kwanaki idan ya dawo maimakon kwanaki biyu, idan nan ma ba'a samu matsaya ba kuma ke kina da karfin sha'awar da bazaki iya jure wata uku ko huɗu ba tare da miji ya kusanceki ba, hakanan kwana biyun da yake yi idan ya dawo baya wadatar dake kuwa akwai yiwuwar ki auka halaka to kuna iya zuwa ga alkalin muslunci in sha Allahu zai samar muku da daidaito a tsakaninku domin yana daga manufofin aure shi ne kaucewa aukawa zina. 

Sannan a karshe ina kira ga mazaje musamman matafiya lallai yana dakyau su dinga lura da bukatun iyalinsu ba kuma iya abinci da sauran kayan more rayuwa ba Har da abinda ya shafi jima'i domin suma suna da bukatar jima'in akai-akai kuma banda ku mazajensu Babu wanda aka halattawa ya kusancesu. Idan kai kana ganin kana da mace fiye da ɗaya to ka sani ita miji ɗaya tal take dashi Kuma rashin kiyaye hakkokin mata na jima'i yana kawo barazana ga rayuwarsu da imaninsu, Sannan ku dinga nuna damuwarku akansu maimakon koda yaushe su zasu kiraku kuma ku dinga kiransu kuna debe musu kewa kuna kwantar musu da hankali kai babu laifi ma ku dinga yin SEX CHAT dasu domin debe musu kewa maimakon ku dinga nuna halin ko in kula da bukatarsu gareku Amma SEX CHAT ɗin ya zama da sharadin kai da matar ku keɓance babu wani kusa daku Sannan da sharadin chat din bazai watsu ga wasu wadanda baku ba.

WALLAHU A'ALAM

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments