Ticker

6/recent/ticker-posts

Falala Da Fa’idar Yin Aure

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaiku Mal. Khamis Ina maka fatan Alkhairi 🙌🏽 Ubangiji Allah ya saka maka da Alkhairi irin kokari da kake yi da jama'a, Allah ya kara maka lafiya da nisan kwana mai Albarka.👏🏼 Mal. Khamis ina da tambaya ina so sanin falalar da fa'idan yin Aure Bisa Alkur'ani Da Sunnah.?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Walaikum sallam warahmatahi wabarkatahu;

Aure yana da falala da alkhairai masu yawa a musulunci da kuma rayuwar ɗan adam ta yau da kullum. Shari'ar musulunci ta kwadaitar da yin aure domin yana kawo albarka, tsari, da kuma lada mai yawa ga ma'aurata waɗanda suka yi shi a matsayin Sunnar Ma'aiki (Sallallahu Alaihi Wa Sallam), kuma suka kiyaye dokokin shi.

Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya kwaɗaitar da al'ummarsa akan suyi aure. Ya ce: "Ku auri Mafi soyuwa agareku cikin mata kuma masu haihuwa, domin dayawanku zanyi alfahari ranar alkiyama" kuma ya ce: "aure sunna-ta ne, duk wanda ba ya kwaɗayin sunnah-ta, to ba ya tare dani".

An ruwaito Daga cikin manyan ɗaliban Abdullahi ɗan Abbas wato Abdullahi bn Jubairi Ya ce Abdullahi ɗan Abbas ya tambaye shi shin kayi aure? Sai ya ce bai yi ba, sai ya ce masa kayi aure domin mafi alherin wannan al'umma yana da aure. Wato yana nufin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) da manyan sahabbansa duk suna da aure don haka idan so kake kabi sunnar su to kayi aure.

An karɓo hadisi daga Abdullahi ɗan Mas'ud (Allah Ya kara masa yarda), Manzon Allah (Sallallahu Alaihin Wasallam) Ya ce, ya ku taron matasa duk wanda ya samu iko daga cikin ku, toh yayi aure domin shi ne yafi taimakawa wajan rintse gani kuma shi ne yafi taimakawa wajan kare farji daga aikata zina, wanda bai samu iko ba toh na umarce shi da yin azumi domin azumi garkuwace gare shi. Bukhary da Muslim ne suka ruwaito shi. Bukhari 5065.Muslim 1400.

Allah Ya faɗa a cikin Suratun Nisaa, inda Ya ce;

...فَانْكِحُوۡا مَا طَابَ لَـكُمۡ مِّنَ النِّسَآءِ مَثۡنٰى وَثُلٰثَ وَرُبٰعَ ۚ فَاِنۡ خِفۡتُمۡ اَلَّا تَعۡدِلُوۡا فَوَاحِدَةً اَوۡ مَا مَلَـكَتۡ اَيۡمَانُكُمۡ ؕ ذٰ لِكَ اَدۡنٰٓى اَلَّا تَعُوۡلُوۡا ؕ‏

...ku auri abin da ya yi muku daɗi daga mata; biyu-biyu, da uku-uku, da huɗu-huɗu. Sa'an nan idan kun ji tsoron ba za ku yi adalci ba, to, (ku auri) guda ko kuwa abin da hannayenku na dama suka mallaka. Wannan shi ne mafi kusantar zama ba ku wuce haddi ba. (Surah: An-Nisaa, Ayat: 3).

وَمِنۡ اٰيٰتِهٖۤ اَنۡ خَلَقَ لَكُمۡ مِّنۡ اَنۡفُسِكُمۡ اَزۡوَاجًا لِّتَسۡكُنُوۡۤا اِلَيۡهَا وَجَعَلَ بَيۡنَكُمۡ مَّوَدَّةً وَّرَحۡمَةً ؕ اِنَّ فِىۡ ذٰ لِكَ لَاٰيٰتٍ لِّقَوۡمٍ يَّتَفَكَّرُوۡنَ‏

"Kuma akwai daga ayoyinsa, Ya halitta muku matan aure daga kanku, domin ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku. Lalle a cikin wancan akwai ayoyi ga mutane masu yin tunani. (Surah: Ar-Room, Ayat: 21).

وَلَقَدۡ اَرۡسَلۡنَا رُسُلًا مِّنۡ قَبۡلِكَ وَ جَعَلۡنَا لَهُمۡ اَزۡوَاجًا وَّذُرِّيَّةً ؕ وَمَا كَانَ لِرَسُوۡلٍ اَنۡ يَّاۡتِىَ بِاٰيَةٍ اِلَّا بِاِذۡنِ اللّٰهِ ؕ لِكُلِّ اَجَلٍ كِتَابٌ‏

"Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun aika waɗansu manzanni, daga gabaninka, kuma Muka sanya matan aure a gare su da zuriyya, kuma ba ya kasancwa ga wani Manzo ya zo da wata aya, sai da iznin Allah. Ga kowane ajali akwai littafi. (Surah: Ar-Ra'd, Ayat: 38).

Manzon Allah (Sallallahu Alaihin Wasallam) Ya ce; "Wanda yayi aure, hakika ya kammala rabin Addinin sa, toh ya ji tsoron Allah a sauran rabin" Watau ibadar da aka halicce ka don kayi ta, idan kayi aure, Allah Subhanahu Wa Ta'ala Ya ba ka rabin ta Ƙyauta.

Manzon Allah (Sallallahu Alaihin Wasallam) Ya ce hakika idan ɗayan ku ya ga wata mace sai ta kayatar da shi toh ya tafi wajan iyalin sa, hakika yin hakan zai mayar da abin da ya ji a zuciyar sa. Muslim ne ya ruwaito shi (hasanun sahihun).

Daga Abdullahi ɗan Amr RA ya ce : Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya ce: Duniya wani jin daɗi ce, amma mafi alherin jin daɗinta shi ne auren mace ta gari. Muslim 1467.

Abu zarrin RA ya ruwaito, Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya ce: Idan kuka sadu (jima'i) da iyalanku za a baku lada, sai sahabbai suka ce, yaya ɗayanmu zai biya sha'awar sa kuma a bashi lada? Sai ya ce ku bani labari, idan yayi zina ba za a rubuta masa alhakki ba? Sai suka kwarai, sai ya ce to haka za a bashi lada idan ya kwanta da iyalansa. Muslim 1006. Abu Dauda 1286.

Abdullahi ɗan Masud yana cewa Da zai zama saura kwana ɗaya duniya ta tashi, zan so ace nayi aure a wannan lokacin (Musannnaf Ibn abi Shaibah 3/454 ).

Ibn Abbas R.A, sahabin Annabi (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) Ya ce "Ku yi aure, domin kwana guda da aure shi ne mafi alheri daga ibadar shekara dubu". Waɗannan hadisan akwai su cikin Buguyatul Muslimina.

Fa’idodin da suke cikin aure ba za su Kididdigu ba amma ga wasu kaɗan daga ciki za mu lissafo kamar haka;

1. Yin aure biyayya ne ga Umurnin Allah da Manzon Allah (Sallallahu Alaihin Wasallam).

2. Yin aure yana sanya Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) farin ciki a ranar lahira. Ya ce “Ku yi aure ku hayayyafa domin ni zan yi ma sauran al’ummomi alfahari da ku a ranar Alkiyamah”.

3. Ta dalilin aure za ka samu wanda zai fito ta jikin ka, har ya girma yana kalmar Shahada!!

4. Ta dalilin aure ne za ka samu zuriyar da za su yi maka addu’a bayan rasuwar ka wannan yana daga cikin ayyukan da ladan su ba zai yanke ba har abada.

5. Yin aure ya kan zama dalilin runtsewar idanun mutum daga kalle kallen haramun, sannan ya kare masa al’aurar sa daga Zina.

6. Ta dalilin aure ne za ka samu damar taimaka ma ƴar uwar ka Musulma, ka aure ta, ka kiyaye ta kenan daga Zina.

7. Ta dalilin aure ne za ka samu cikar Addinin ka, da ninkawar ladan ka fiye da wanda ba su da aure.

8. Ta dalilin aure ne za ka samu ladan ciyar da Matar ka, da daukar nauyin ta, da ladan samar mata da Mazaunin da za ta rayu.

9. Ta dalilin aure ne za ka samu damar Qara yawan Musulman duniya ta hanyar haihuwar da za ka samu.

10. Ta dalilin aure ne za ka samu damar karkatar da himmar ka daga kan nemen biyan bukatar ka ta hanyar haram izuwa ga hanyar halal. Da kuma samun ladan saduwa da iyalan ka.

11. Za ka samu lada mai girma sosai idan har Allah Ya azurta ka da ƴaya mata guda biyu, kuma kayi hakuri da su ka kyautata musu, ka kyautata tarbiyyar su, su za su zama garkuwar ka daga shiga wuta.

12. Idan har ƴayan ka guda biyu suka rasu, kuma kayi hakuri, toh Allah zai shigar da kai Aljannah saboda wannan.

13. Ta dalilin aure za ka samu Qaruwar mutuncin ka da darajar ka a cikin al’ummah, ka shiga sahun mutanen da za su iya jagorantar lamuran rayuwar al’ummah.

14. Ta dalilin aure ne zaka samu taimakon Allah cikin lamarin ka. Kamar yadda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) Yake cewa: mutum uku, hakki ne akan Allah ya taimake su. wanda zai yi aure don nufin kame mutuncin sa. bawa wanda yake neman ‘yancin sa saboda ya samu daidaituwa (a cikin addini). mujahidi (mai yakin daukaka addinin Allah).

Muna tunatar da matasa da ƴan mata da suke da ikon yin aure, lallai a je ayi aure, a rage burin duniya. Kullum rayuwa tafiya take yi mutuwa zuwa yake yi babu notice, ku dubi duk waɗannan garaɓasar amma ban da Tuzurai da Gwagware Mata da Maza, su ba za su samu ba. Fatan mu duk masu niyyar Aure irin mu Allah Ya Mana jagoranci, Ya hore mana daga falalar Sa Ameen.

Ya Allah ga bayin Ka suna son Ɗabbaka umarnin Manzon Ka (Sallallahu Alaihin Wasallam) Ya Allah, wanda ba Shi da kuɗin yin Aure Ya Allah Ka ba shi, irin mu kenan, wanda kuma yake da shi amma bai samu halin yi ba Ya Allah Ka ba shi Ikon yi. Ya Allah Ka sa mu Auri masu Taqwa da kwantar mana da hankalin mu a duk lokacin da muke cikin wani hali sannan su zama hanyar shigar mu Aljannah Ameen Ya Yayyu Ya Qayyum.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments