𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Matata tana aiki kuma tana samun albashi, amma kullum wulaƙanci nake sha a hannunta domin karayar tattali da ya same ni. In dai ban kawo cefane ba, to ba ni da abinci ko wurin kwana. Ko dai kawai in sake ta ne?
MATATA TANA WULAƘANTA NI SABODA INA CIKIN
MAWUYACIN HALI NA RASHIN KUƊI
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa
Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
Abin da kake ciki yana da
matukar ciwo da tashin hankali. Ba daidai ba ne mace ta riƙa wulaƙanta
mijinta saboda yana cikin mawuyacin hali na rashin kuɗi.
Aure jarrabawa ce da ake buƙatar
haƙuri da taimakon juna daga ɓangarorin
biyu. Duk da cewa halin da kake ciki yana da zafi sosai, saki ba shine mafita
ta farko ba. Dukiyar matarka nata ce, amma kuma hakkin ta ne ka ciyar da ita.
A ƙa’ida
ko da mace tana da arziƙi,
haƙƙin ciyarwa da tufatarwa da
samar da mazauni da bayar da magani a lokacin rashin lafiya da sauransu
makamantansu a kan mijinta ne su ke, ba a kan ta ba. Wannan shi ya bai wa
namiji matsayinsa na mai kulawa da iya yin saiti ga iyalinsa har da matarsa.
Allaah Ta’aala ya ce:
الرِّجَالُ
قَوَّامُونَ عَلَى النِّسَاءِ بِمَا فَضَّلَ اللَّهُ بَعْضَهُمْ عَلَى بَعْضٍ
وَبِمَا أَنْفَقُوا مِنْ أَمْوَالِهِمْ
Mazaje ne masu tsayuwa a kan
mata domin abin da Allah ya fifita sashensu a kan sashe da shi, da kuma abin da
mazan suke kashewa na dukiyoyinsu. (Surah An-Nisaa’: 34).
Don haka, idan miji ba zai
iya ɗaukar
nauyin iyalinsa ba, bai halatta tun farko ma ya yi aure ba. Annabi (Sallal
Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
«يَا
مَعْشَرَ الشَّبَابِ مَنِ اسْتَطَاعَ مِنْكُمُ البَاءَةَ فَلْيَتَزَوَّجْ، وَمَنْ
لَمْ يَسْتَطِعْ فَعَلَيْهِ بِالصَّوْمِ فَإِنَّهُ لَهُ وِجَاءٌ»
Ya ku taron matasa! A
cikinku duk wanda yake da ikon ‘BAA’AH’ to ya yi aure, kuma duk wanda ba shi da
iko sai ya kama yin azumi, domin shi kariya ne a gare shi. (Sahih Al-Bukhaariy:
5065; Sahih Muslim: 1400).
Ma’anar ‘AL-BAA’AH’ kamar
yadda malamai suka nuna ita ce: Ƙarfi
ko ikon saduwa da mace, ko kuma ƙarfin
ɗaukar
nauyin ɗawainiyar
auren.
Don haka shari’a ba ta bai
wa namiji daman kwanciya ya jira wai matarsa ce za ta riƙa ciyar da shi ba.
Ita kuma mace da ta samu
arziƙi sama da mijinta, ya zama haƙƙi a kanta ta kula da yin
sadaka da alheri ga jama’a
musamman talakawa daga cikin makusantanta. Saboda maganar Allaah (Subhaanahu Wa
Ta’aala) da ya ce:
وَفِي
أَمْوَالِهِمْ حَقٌّ لِلسَّائِلِ وَالْمَحْرُوم
Kuma a cikin dukiyoyinsu
akwai haƙƙi ga mai tambaya da wanda ya
kame. (Surah Az-Zaariyaat: 19).
Kuma mafi girma daga cikin
waɗanda
suke da wannan haƙƙin
samun sadakar mace akwai mijinta, saboda maganar da Annabi (Sallal Laahu Alaihi
Wa Alihi Wa Sallam) ya gaya wa Zainab matar Abdullaah Bn Mas’ud (Radiyal Laahu Anhumaa)
cewa:
«صَدَقَ
ابْنُ مَسْعُودٍ، زَوْجُكِ وَوَلَدُكِ أَحَقُّ مَنْ تَصَدَّقْتِ بِهِ عَلَيْهِمْ»
Gaskiya Ibn Mas’ud ya gaya
miki: Mijinki da ’ya’yanki suka fi cancantar samun sadakar dukiyarki. (Sahih
Al-Bukhaariy: 1462).
Wannan ɗin
kuma shi ya fi mata lada, saboda abin da ya zo a cikin wata riwaya na hadisin
da ya gabata, lokacin da su Zainab ɗin
suka tambayi Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) a kan bayar da
sadaka ga mazajen aurensu, sai ya ce:
«نَعَمْ،
لَهُمَا أَجْرَانِ: أَجْرُ الْقَرَابَةِ، وَأَجْرُ الصَّدَقَةِ
»
Na’am, suna da lada biyu:
Ladan zumunci da ladan sadaka. (Sunan An-Nasaa’iy: 2583, kuma Al-Albaaniy ya
sahhaha shi).
Don haka dai maganar ba ta
kai na saki ba a tsakaninku, in sha Allahu. Kawar da kai za ka yi daga
dukiyarta, ka tashi ka jajirce wurin nema daga falalar Allah. Ita kuma ta
taimaka maka, ko da da sadaka ne. Allaah ya ƙara
mana fahimta.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.