𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum Malam Khamis ina son yin tsayuwar dare saboda ɗimbin falalar da ta ƙunsa, sai dai a lokuta da yawa, na kan so na tashi amma sai na kasa, to malam khamis ko zaka taimaka min wajan samun damar tsayuwar dare, da shawarwari akan abin da zai taimake ni wajan yin wannan babban aikin?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam
warahmatullahi wabarakatuhu
Sallar dare (wato
Qiyamul Laili) tana daya cikin ibadu mafi girma da daraja a musulunci. Annabi
(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: "Mafi falalar sallah bayan sallar
farilla ita ce sallar dare.
Yin sallar dare
(qiyamul laili) yana da falala mai yawa da Allah Ta'ala ya keɓance shi da su kamar
yadda ayoyin Alqur'ani da ingantattun hadisan Manzon Allah (Sallallahu alaihi
Wasallam) suka tabbatar. Allah Madaukakin Sarki ya yabi mutanen da suke tashi
cikin dare domin yi masa sujada da tsayuwa.
A kowane dare, a
kashi na karshe na dare, Ubangiji yana sauka zuwa saman duniya yadda ya dace da
girmansa. Yana cewa: "Waye zai roke ni na ba shi? Waye zai neme ni gafara
na yafe masa?" Wannan ne ya sa sallar dare ta zama mafi kusa wajen samun amsar
addu'a.
Don samun nasarar
tashi don yin tsayuwar dare (Qiyamul-lail), yana da kyau ka ɗauki matakai a aikace
wajen rage nauyin jiki da kuma shirya zuciya da gangar jiki. Akwai abubuwa da
Malamai suka yi bayanin cewa suna taimakawa wajan samun damar tsayuwar dare, ga
wasu daga ciki:
1. RAGE CIN ABINCI DA
YAWA: Cin abinci mai yawa ko nauyi kafin kwanciya yana haifar da kasala da
nauyin bacci.
2. BACCIN RANA: Yin ɗan baccin mintuna 30
zuwa 45 da rana yana taimakawa wajen kawar da gajiya tare da ba ka kuzarin
tashi da daddare. Hasanul Basary ya wuce wasu mutane a kasuwa da rana, sai
yace: "Waɗannan ba za suyi
bacci ba?" sai aka ce masa "Eh", sai yace: "Ina ganin
darensu ba zai yi kyau ba".
3. KWANA DA WURI: Ka
tabbatar ka kwanta da wuri bayan sallar Isha’i domin samun isasshen hutu.
Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya karhanta bacci kafin Sallar Isha'i da
kuma yin hira bayanta, kamar yadda yazo a Hadisin Muslim mai lamba ta 647, kuma
dalilin da yasa ya karhanta yin hira bayanta saboda hakan zai iya hana mutum
tsayuwar dare.
4. SAKA ƘARARRAWA (ALARM): Ka
saita ƙararrawa (alarm) ko ta wayarka, kuma idan akwai yiwuwa,
ka nemi wani aboki ko matarka ko ɗan'uwa mai himma su riƙa tayar da kai. Allah
yana saukar da rahamarsa ga miji da mata da suke taimaka wa juna wajen tashi
domin yin sallar dare. Idan miji ya tayar da matarsa suka yi sallar raka'a
biyu, ana rubuta su a cikin rukunin maza da mata masu yawan ambaton Allah.
5. NISANTAR ZUNUBAI:
Fudhail bn Iyadh yana cewa: "Idan kaga ba ka iya tsayuwar dare, to ka
tabbatar zunubai ne suka dabaibaye ka".
6. NISANTAR YIN AIKI
MAI WAHALA DA RANA: Nisantar yin aiki mai wahala da rana ko abin da zai kawo
maka fargaba a cikin zuciya, ta hanyar rage burirrika da tunanin abin da ya
wuce.
7. NEMAN TAIMAKON
ALLAH (ADDU'A): Ka roki Allah Ta'ala da ya ba ka ikon tashi don bauta masa da
tsarkakakkiyar niyya. Ka aikata ladubban bacci yayin kwanciya, ta yadda zaka
karanta abin da yazo a cikin Sunnah na addu'o'i da ladubban bacci.
8. FARAWA DA KAƊAN-KAƊAN: Kada ka ɗora wa kanka nauyi
mai yawa. Ka fara da raka'a biyu kawai ko da a kowace rana ne, sannan a hankali
sai ka riƙa ƙarawa.
Idan har ka kiyaye waɗannan, da izinin
Allah za ka dinga tashi sallar dare (Qiyamul-lail). Ina fatan Allah ya datar da
mu gaba ɗaya zuwa wannan ibada
mai girma.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.