𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Aslm Dan Allah inada tambaya mene ne hakkin makwabtaka? Me ya kamata ka yi ma makwabcinka ka fita hakkinshi?
HAƘƘOƘIN MAƘWABTAKA
𝐀𝐌𝐒𝐀❗
Wa'alaikumus salam
Warahmatallahi Wabarkatahu
wajibi ne kowane
Musulmi ya san hakkokin makwabcinsa da suke kansa, tare da sanin ladaban zama
da shi, idan ya san hakan, shi zai sa ya zauna da makwabtansa kamar yadda
addini ya tsara.
Malamai sun bayyana
makwabci cewa shi ne wanda in ka ƙidaya gidaje arba'in
daga jikin gidanka hagu da dama gaba da baya.
A tsarin Musulunci
makwabta sun kasu zuwa kashi uku, kowanne da irin hakkokin da ke kansa, akwai
mai hakki ɗaya da mai hakkoki
biyu da kuma mai hakkoki uku.
1. MAKWABCI MUSULMI,
MAKUSANCI (ƊAN'UWA): Shi wannan yana da hakkoki uku, hakkin Musulunci
ga hakkin makwabtaka, ga kuma hakkin 'yanuwantaka, wanda yake tsan-tsan ya ga
ya ɗauke dukkan waɗannan hakkoki.
2. MAKWABCI MUSULMI:
shi wannan yana da hakkoki biyu ne kawai, wato hakkin makwabtaka, sai kuma
hakkin Musulunci.
3. MAKWABCI WANDA BA
MUSULMI BA: shi ma nan yana da hakki ɗaya ne kawai wato hakkin makwabtaka.
Ubangiji mai girma da
ɗaukaka ya fada cikin
littafinSa mai girma, cikin suratul Nisa’i aya ta 36 cewa:
وَاعْبُدُوا
اللَّهَ وَلَا تُشْرِكُوا بِهِ شَيْئًا وَبِالْوَالِدَيْنِ إِحْسَانًا وَبِذِي
الْقُرْبَىٰ وَالْيَتَامَىٰ وَالْمَسَاكِينِ وَالْجَارِ ذِي الْقُرْبَىٰ
وَالْجَارِ الْجُنُبِ وَالصَّاحِبِ بِالْجَنبِ وَابْنِ السَّبِيلِ وَمَا مَلَكَتْ
أَيْمَانُكُمْ إِنَّ اللَّهَ لَا يُحِبُّ مَن كَانَ مُخْتَالًا فَخُورًا
“Kuma ku bauta wa
Allah kuma kada ku haɗa wani da Shi, kuma
ga mahaifa ku yi kyautatãwa, kuma ga ma'abũcin zumunta da marãyu da matalauta,
da maƙwabci ma'abũcin kusanta, da maƙwabci manĩsanci,
da abõki a gẽfe da ɗan hanya, da abin da
hannuwanku na dãma suka mallaka. Lalle ne Allah bã Ya son wanda ya kasance mai
tãƙama,
mai yawan alfahari.
Ayoyi da hadisai sun
karfafa hakkin makwabci a kan makwabcinsa. Jibrilu (AS) bai gushe ba yana yi wa
Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam wasiyya a kan makwabci har sai da ya
yi tsammanin makwabci zai yi tarayya da makwabicnsa a cikin gado. Don haka babu
mai munana wa makwabci ya cutar da shi face la’imi marar son alheri kuma abin
kyama. Mai aikata dukan fasadi a bayan kasa.
Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam yana cewa: “Wallahi bai yi imani ba! Wallahi bai yi
imani ba! Wallahi bai yi imani ba! Aka ce, “Ya Manzon Allah! Sallallahu Alaihi
Wasallam Hakika wannan kuwa ya taɓe kuma ya yi asara, wane ne shi?” Ya ce:
“Wanda makwabcinsa bai kubuta daga bawa’ikahu ba. Suka ce: “Mene ne
bawa’ikahu?” Ya ce: “Sharrinsa.”
Har ila yau, Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce: “Wanda ya kasance ya yi imani da Allah
da Ranar Lahira, to, ya girmama makwabcinsa, kuma wanda ya kasance ya yi imani
da Allah da Ranar Lahira, to, ya girmama bakwabcinsa, kuma wanda ya kasance ya
yi imani da Allah da Ranar Lahira, to ya fadi alheri ko ya yi shiru.” Kuma
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce: “Mumini, shi ne wanda mutane
suka aminta da shi. Musulmi kuma shi ne wanda Musulmi suka kubuta daga
harshensa da hannunsa, mai hijira kuma shi ne wanda ya kauracewa mugun abu. Na
rantse da Wanda raina yake hannunSa, wanda makwabcinsa bai kubuta daga
sharrinsa ba, ba zai shiga Aljanna ba!”
Idan muka yi duba ga
wannan Aya da waɗannan Hadisai za mu
fahimci girman kyautatawa makwabci da girmama shi, domin girmama shi ma yana
nuna cewa mutum ya bayar da gaskiya da Allah da ranar Lahira.
Abin kunya ne gare ka
ya kai Musulmi! A ce ka kwana a koshi, amma makwabcinka ya kwana da yunwa! Abin
kunya ne gare ka a ce ka yi sababbin tufafi amma ka yi rowar tsofaffin
tufafinka ga makwabtanka marasa tufa! Kuma abin kunya ne gare ka a ce kana jin
daɗi da dadadan abinci
da abin sha, amma makwabtanka suna neman kasusuwa da sauran abinci, alhali kana
sane da faɗin Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam: “Kada makwabciya ta raina abin da za ta ba
makwabciyarta ko da kashin hakarkarin akuya ne kuwa.” Kuma ya ce da Abu Zarri
(RA): “Ya Abu Zarri idan kana dafa nama ka yawaita ruwan (romo) don ka ba
makwabtanka.”
Ya kai Musulmi!
Lallai daga cikin hakkokin makwabci a kanka akwai cewa, ka yi masa sallama idan
ka haɗu da shi, kuma ka je
gaida shi idan ba ya da lafiya, kuma ka raka gawarsa idan ya rasu, kuma ka
kasance uba ga ’yan’yansa bayan rasuwarsa kamar yadda shi ya kasance musu a
rayuwarsa. Ka tsaya a gefensa (tare da shi) a cikin kunci da yalwa da tsanani
da wadata. Wata maganar hikima na cewa: “Wanda amfanar da ’yan uwansa ta kubuce
masa, kada ya yarda amfanar da makwabcinsa ta kubuce masa!” Kuma Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce: “Mafi alherin aboki a wurin Allah Maɗaukaki, shi ne wanda
ya fi alheri ga abokinsa, kuma mafi alherin makwabci a wurin Allah Maɗaukaki shi ne wanda ya
fi yin alheri ga makwabcinsa.”
Haram ne a kanka ya
kai Musulmi! Ka rika leka gidan makwabcinka alhali bai sani ba, ko ka ha’ince
shi game da iyalinsa. Duk wanda ya leka gidan makwabcinsa ba tare da izininsa
ba, Allah zai cika idonsa da wutar Jahannama. Kuma haram ne a gare ka rika kashe
kunne domin ka ji abin da yake fada a cikin gidansa ka zama kamar mai leken
asiri da maganarsa da aikinsa ba za su kubuta daga gare ka ba.
Kuma idan ba za ka
iya kyautata wa makwabcinka da dadada masa ba, to ka kame daga cutar da shi,
kada ka cutar da shi ko da da gaisuwa don ya samu ya huta a cikin gidansa. Idan
ya kira ka, ka amsa masa, idan ya nemi shawararka ka ba shi shawara tagari,
idan aka zalunce shi ka taimaka masa, idan shi yake zaluncin ka hana shi. Idan
ya kyautata ka gode masa, idan ya munana ka yi masa afuwa, idan ya aikata
fasadi kada ka karfafa shi a kai, domin da yawa makwabci zai rike wuyan
makwabcinsa a Ranar kiyama ya ce: “Ya Ubangijina! Lallai ne wannan ya rufe min
kofarsa, ya ki yi min nasiha, ya gan ni ina aikata sharri bai hana ni ba.” Wani
mutum ya ce, “Ya Manzon Allah! Sallallahu Alaihi Wasallam Lallai ana ambaton
yawan Sallar wance da azuminta, sai dai tana cutar da makwabcinta.” Sai ya ce:
“Tana cikin wuta!” Sai ya ce: “Ya Manzon Allah! Sallallahu Alaihi Wasallam
Lallai wance ana cewa tana da karancin Sallah da azumi, amma tana yawan sadaka…
kuma ba ta cutar da makwabtanta.” Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam
ya ce: “Tana cikin Aljanna.”
Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce: “Abubuwa huɗu suna daga cikin sa’ada: mace tagari
da gida yalwatacce da makwabci nagari da abin hawa mai lafiya. Kuma abubuwa huɗu suna cikin shakawa
(taɓewa da rashin sa’a):
mugun makwabci da muguwar mace da mugun abin hawa da kuntataccen gida.”
Yana daga cikin
hakkokin makwabtaka a kyautata masa ta kowanne hali, kamar aika masa da abin da
ka dafa, bashi shawarwari da za su amfane shi, a kansa ko iyalansa, ko
'ya'yansa, tsawatarwa 'ya'yansa a kan abin da aka ga zai cuce su, domin
kyautatawa makwabci yana kai mutum zuwa Aljanna.
Wani mutum ya je
wajen Manzon_Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yace:"Ya Ma'aikin Allah
shiryar da ni a bisa wani aiki, idan na tabbata a kansa zan shiga Aljanna, sai
yace: "Ya Ma'aikin Allah ta ya ya zan san ni mai kyautatawa ne? Sai ya ce:
Tambayi makwabtanka idan suka ce kai mai kayutatawa ne to shi ne, amma idan
suka ce kai ba mai kayuatatawa ba ne, to ba shi ba ne".
Wannan Hadisi yana
nuna mana cewa idan mutum yana son ya san matsayinsa, to ya tambayi makotansa
sune shaidarsa a kan shi mai kyautatawa ne ko a'a, don haka wajibi ne mu zamo
masu kyautata musu don mu samu kyakkyawar shaidar cewa mu masu kyautatawa ne, don
in muka zamo masu kyautatawa, to mun kama hanyar zuwa Aljanna.
Ibn Umar ya kasance
yana da makwabci Bayahude, idan ya yanka akuya sai ya ce: ku kai wa makwabcina
Bayahude wannan (Abu Dawud da Tirmizi).
Har ila yau, kiyaye
mutuncinsa (Makwabci) dana iyalinsa da dukiyarsa suna daga cikin kyautatawa,
domin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam yace: "Mutum ya yi zina da mataye
goma shi ya fi sauki a gare shi da yin zina da matar makwabcinsa, mutum ya yi sata
a gidaje goma shi ya fi sauki a gare shi da ya yi sata a gidan
makwabcinsa" (Ahmad).
Ya zo cikin sunani
Abu Dawud daga Aba Huraira Allah ya kara yarda a gare shi ya ce: "wani
mutum ya zo wajen Ma'aikin Allah ya kawo karar makwabcinsa, sai ya ce da shi,
ka je ka yi hakuri, sai ya sake zuwa na biyu ko na uku, sai Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce: jeka ka ɗebo kayanka ka zuba a kan hanya, sai ya je ya
sanya duk lokacin da mutane suka zo wucewa sai suka tambaye shi bisa halin da
yake ciki, sai ya basu labarin irin cutar da makwabcinsa yake yi masa Sai suka
rinka la'antar makwabcin, sai makwabcin ya zo gare shi ya ce: ya ɗan uwana mayar da
kayanka gidanka ba zaka kara ganin wani abu na rashin kyautatawa ba daga gareni
har abada".
Ya bayin Allah! “Lallai
ne Allah Yana umarni da adalci da kyautatawa da ba ma’abucin zumunta
(hakkinsa), kuma Yana hani daga alfasha da abin ki da zalunci, Yana yi muku
wa’azi tsammaninku za ku yi tunani.” Don haka ku tuna Allah Mai girma da ɗaukaka, sai Ya tuna
da ku, kuma ku gode maSa a bisa ni’imominSa, sai Ya kara muku. Kuma ambaton
Allah ne mafi girma. Kuma Allah Yana sanin abin da kuke aikatawa.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.