Ticker

6/recent/ticker-posts

Wadanda Suke Ihu Da Timuwa A Kasa Idan An Yi Musu Mutuwa

TAMBAYA (67)

Menene hukuncin wanda yake ihu da timuwa a kasa saboda an yi masa mutusa ?

AMSA

Ba mu da abin fada face abinda Annabi SAW yace a lokacin da dan sa (Ibrahim) ya rasu; "Haqiqa ido yayi wahaye, zuciya ta quntata, ba ma da abin fada face abinda zai farantawa Ubangiji. Muna baqin cikin rashinka ya Ibrahim"

Bukhari 1303 da Muslim 2315

Da kuma abinda Abu Dardaa ya fada; "me nake gani yayinda mutane suke qoshi da abinci amman kuma suna tsananin jin yunwar ilimi"

Da kuma abinda Ayyub as-Sakhtiyaani ya fada; "Haqiqa idan labarin mutuwar Ahlus Sunnah ya riskeni, sai naji kamar wata gaba ce a cikin gabobin jikina ta fadi"

Abu Nu'aym al-Hilya Vol. 3 page 9

Da kuma abinda Imam Ibn al-Qayyim ya fada a cikin Miftaah Daar us Sa'aadah, a page 74 yace; "Kyakkyawar rayuwa ita ce kusantar malamai, saboda idan babu su to mutane zasu koma ne tamkar shanu a garke ko fiye da haka"

Wallahu ta'ala a'alam

Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta, astaghfiruka wa'atubi ilayk

Amsawa;

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments