Ticker

6/recent/ticker-posts

Lemu Shege! (Waƙar Daɓe)

Ina Lumu shege,

Mai malmala ga munta.

 

Kare baƙin bahwade,

Ya hana mu walwala.

 

Mata ku yo aniya,

Bana Lumu ƙwace yakai.

 

Ta masussuki yab biya,

Yat ta da gindi tsaye.

 

Wanga ɗan baƙin mugu,

Ya hana mu walwala.

 

Kare baƙin bahwade,

Mai malmala ga munta,

Ba za ya gwaa hwashe ba.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments