Ticker

6/recent/ticker-posts

2.3.2 Zule-Zuleyya - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 83)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

2.3.2 Zule-Zuleyya

Wannan ma wasan tashe nna yara mazaYana tafiya da waƙa, sannan akan buƙaci kayan wasa yayin gudanar da shi. Kimanin yara biyar ne zuwa sama da haka suke gudanar da wannan wasa. Kamar sauran mafi yawan wasannin tashe, an fi gudanar da shi da dare.

2.3.2.1 Kayan Wasa

i. Sakaina

ii. Wuƙa ko wani abu mai kaifi

iii. Igiya

iv. Kayan fenti iri-iri

v. Sanduna biyu gajeru

2.3.2.2 Yadda Ake Wasa

Yara za su nemi sakaina, sannan su yi amfani da wuƙa ko wnai abu mai kaifi su gyara ta daidai faɗin fuskar mutum. Sai kuma su yi huje-huje a  jikinta daidai wurin da hanci da idanu da baki za su fito. Daga nan za su bi jikin sakainar su yi mata fenti iri-iri. Sukan yi amfani da abubuwa kamar bula da bayan tukunya da farar ƙasa da makamantansu. Bayan an kammala tsaf, za a ɗaura igiya ko lilo ko wani zare mai kauri a gefe da gefen wannan sakaina, sannan a ɗaura a fuskar ɗaya daga cikin ‘yan wasa. Wanda aka ɗaura wa sakainar shi ake kira Zule. Sannan zai nemi sanduna guda biyu gajeru.

Masu wasa za su ɗunguma zuwa wurin tashe. Yayin da suka iso wurin da za su gudanar da wannan tashe, Zule zai sunkuya ya riƙa dogara sandunansa a ƙasa. Zai kasance tamkar wata dabba ce mai ƙafa huɗu. Ga kuma fuskar da aka yi masa da sakaina. Ɗaya daga cikin yara zai sa waƙa, saura kuwa za su riƙa amsawa. Ga yadda waƙar take:

Bayarwa: Iya ku ɓoye ‘ya’yanku ga abin mafarki,

Amshi: Ga Zule ya shigo.

 

Bayarwa: Zule-zuleyya mai idon sakaina,

Amshi: Ga Zule ya shigo.

 

 

Bayarwa: Kura ta leƙa ta ga babu dama,

Amshi: Ga Zule ya shigo.

 

Bayarwa: Damisa ta leƙa ta ga babu dama,

Amshi: Ga Zule ya shigo.

 

Bayarwa: Ɓauna ta leƙa ta ga babu dama,

Amshi: Ga Zule ya shigo.

 

Bayarwa: Gwanki ya leƙa ya ga babu dama,

Amshi: Ga Zule ya shigo.

 

Bayarwa: Zaki ya leƙa ya ga babu dama,

Amshi: Ga Zule ya shigo.

 

Bayarwa: Giwa ta leƙa ta ga babu dama,

Amshi: Ga Zule ya shigo.

Yayin da ake wannan waƙa, Zule zai ci gaba da dogara sandanunasa yana tafiya a sunkuye, tamkar dai dabbar da ake zancenta cikin wannan waƙa. Yara da dama sukan tsorata idan suka gani. Wasu har sai an ɓoye su.

2.3.2.3 Tsokaci

Duk da ƙananan yara na tsorata yayin da suka ga Zule, wasan ya kasance mai nishaɗantarwa ga masu kallo (manya). Sannan waƙar wasan na ɗauke da sunayen dabbobin dawa kamar yadda Hausawa ke kiransu. Wannan kamar ilmantarwa ce tare da kundance sunayen dabbobin daji. Bayan haka, wasan na nuna gaba ma da gabanta ko a cikin dabbobi.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments