Ticker

6/recent/ticker-posts

Salo Asirin Waƙa na Farfesa Abdullahi Bayero Yahya [02 - Babi Na Ɗaya]

Salo Asirin Waƙa
Salo Asirin Waƙa

Salo Asirin Waƙa

BABI NA ƊAYA

Mawaƙi Da Waƙa

Mawaƙi

Ya dace tun da farko manazarci ya san ko wane ne mawaƙi da kuma waƙa ita kanta kamin a yi bayani kan maƙasudin wannan littafi.

Shi dai mawaƙi a ƙasar Hausa mutum ne wanda mutane ke yi masa kallo ta fuskoki da dama: ko dai su ce yana da azanci ko mace ne da maza ba su faɗa da shi kan abin da ya ce musu, ko kuma su ce yana da fasaha da ilmi. Idan suka ce mace ne to mai kiɗa da waƙa ne a yayin da marubucin waƙa suke yi wa ɗaukar malami, wato mai ilmi mai fasaha.[1]

Wannan kallo da Hausawa kan yi wa mawaƙi ya tusgo ne a sakamakon kasancewarsu musulmi da kuma fahimtar da suka yi wa matsayin sabgar mawaƙi da shi kansa a Musulunci. Ba ƙudurin wannan littafi ba ne ya nuta cikin wannan magana domin masana a fagen ilmin addini ne ke da wannan gona.[2]

Waƙoƙin da al’umma ke ji kuma ta lamunta da lafazinsu, ba ta ji mawaƙi ya saɓa ta fuskar harshenta (ta yadda za ta kasa gane ma’ana da sauri) da al’adunta da addininta ba, su ne ke cikin filin da mutane ke saurin fahimta nan da nan ba da wahala ba. Misali:

 1. In za ka faɗi faɗi gaskiya
Kome taka ja maka ka biya

2. Haka ne editanmu na Gaskiya

 Wadda ta fi dubun zinariya

 

3. Sai mu gode Allah shi ɗaya

 Don shi ne Sarkin gaskiya

 

4. Ya mallaki dukkan talikai

 Na kwari da tudu da samaniya

 

5. Da mutum aljan da mala’ika

 Dabbar sarari da ta maliya

 

 

6. Mulki iko daula duka

 Na ga Sarki Allah shi ɗaya

 

7. Shi yake ba wanda ya so duka

 Ya sarautu a lardin duniya

 

8. Shi yake karɓe ta ga taliki

 Don ya ɗanɗani wahalar duniya

 (Sa’adu Zungur: Arewa Jumhuriya Ko Mulukiya)

 

Duk da yake Sa’adu Zungur ya saɓa wa ƙa’idar harshen Hausa ta sanya kalmar ‘da’ tsakankanin jerin sunayen da aka rattaba (kalmomi masu gicciyen rubutu a baiti na 5 da na 6), wannan bai hana wa masu saurare su fahimci manufarsa ba. Wata ƙa’ida da Zungur ya karya ita ce sauya kalmar ‘sarauta’, ya kawo lamirin ‘ta’, (bt 8) kurum. A ganin mawaƙin tun da a baya kaɗan ya ambaci aikatau na sarauta, wato ‘sarautu’, ba lalle ne tababa ta shigo kan manufarsa don ya yi amfani da lamirin sunan ba.

Ga kuma wani misali:

16. Ban da kowa birnin ga baicin ka

Ba ni bin kowa sai da yardakka

Wanda dut yac ce za shi soke ka

Yanzu in ya ga ni sai ya lele ka

 Ya sani fuskata takobi ta

 (Haliru Wurno: Sarkin Musulmi Abubakar III, Safiya Da Gaskiya Taka Aiki)

A wannan baiti mawaƙin ya yi amfani da kalmomi a muhallin da Hausawa ba su amfani da su da kuma inda suke amfani da su, amma shi da abin da yake nufi. A duk wuraren nan biyu Hausawa sun fahimce shi ba da wata matsala ba.

A wuri na farko Haliru ya yi amfani da kalmar ‘lele’, wadda Hausawa ke jinginawa ga nuna tsananin ƙauna da tattali zuwa ga ɗa ko ɗiya daga mahaifi ko mahaifiya. To amma shi Haliru ba wannan yake nufi ba. Manufarsa ita ce ‘mutum ya kwanta wa wanda a da can sukar sa yake yi, mutum ya ayyana tsoro da taushi da girmamawa da ladabi da biyayya ga wanda a da can yake ci wa mutunci’.

A wuri na biyu kuwa Haliru ya ce fuskarsa takobi ce. Haƙiƙa Hausawa sun san da irin wannan fasahar magana. To amma idan suka yi la’akari da abin da Haliru yake gabatar musu, wato waƙa, za su fahimci cewa shi harshensa wanda ke cikin bakinsa wanda yake waƙa da shi, shi yake nufi. Wato harshen Haliru takobi ne ga mai sukar Sarkin Musulmi Abubakar III. Abin nufi shi ne, sukar da Haliru zai yi da harshensa zuwa ga mai sukar Sarkin Musulmi Abubakar III, ta fi kaifi da gauni da zafi. Take wannan suka daga Haliru za ta fille kan duk mai sukar Sarkin Musulmi, ta fitar masa da rai, wato ta fille shi, ko ta yi sanadin a fille shi, ko ta tabbatar wa jama’a cewa wannan mutum ba ya cikin jama’ar Musulmi da Sarkin Musulmi ke shugabanta, hasili ta kafirta shi.

Duk waɗannan misalai suna cikin filin da mawaƙi ya yi tarayya da sauran mutane. Suna iya fahimtar sa kai tsaye ba tare da wata matsala ta harshe ba. Mawaƙi bai tafi can kan iyakar duniyar harshe ba, bai hau kan bangon duniyar harshe ba.

Idan mawaƙi ya kai a kan bangon duniyar harshe ko kuma kusa da shi, to nan kam sai sauran mutane sun yi kamar suna yi kafin su fahimce shi sosai da sosai. Misali:

1. Kai ka isa1 da isa2rka kai ne mai isa3

Ka isa4d da masu isa5 isa6 in sun isa7

(Mu’azu Haɗeja: Halayen Mutane)

 

A wannan baiti mawaƙi ya fito daga da‘irar da ya yi tarayya da sauran mutane, ya koma cikin da’irarsa ta ‘gwanin na gwanaye’. Da’irar da yake nuna ikonsa a kan harshe, ya ja kalma ko kalmomi yadda yake so. A baitin nan Mu’azu Haɗeja ya ja kalmar ‘isa’ tamkar yana jan alewa. Ya yi amfani da ita har sau bakwai tattare da ma’anoni mabambanta (salon dibilwa ke nan). Ga yadda watakila manazarci zai fassara kowace kalmar ‘isa’ a jere:

1. isa – yin abin da aka so ba da la’akari da ko akwai abin da

 ko wanda zai hana ba.

2. isa – iko.

3. isa – cikakken iko.

4. isa – kai wani zuwa ga wani abu.

5. isa – samun iko.

6. isa – kai wa zuwa ga wani matsayi.

7. isa - ikon da mai cikakken iko ya yarda da shi don ganin

 damarsa.

 

A taƙaice, Mu’azu Haɗeja yana ƙoƙarin bayyana ƙarfin ikon Allah Maɗaukaki, tare kuma da yin addu’a. A maganar yau-da-kullum watakila ga abin da zai ce:

Ya Allah kai ka yin abin da kake so babu mai tare ka saboda

 kai ne mai cikakken iko, ka kai waɗannan da ka yarje wa

 su kai ga matsayin ɗaukaka.

Irin wannan zaren tunani ya ginu ne a kan abubuwa guda uku: na ɗaya shi ne ilmin Tauhidi; na biyu shi ne sanin kalmar da ke iya sarrafuwa; sannan na uku shi ne amfani da salon dibilwa wanda da shi ne mawaƙi ya tsallaka daga filin da ya yi tarayya da sauran mutane zuwa cikin filin da shi ne kurum ke iya zuwa gare shi a duniyar harshe.

Haka shi ma Haliru Wurno ya yi amfani da ilmin Tauhidi don ya tsallaka ya shiga da’irar bangon duniyar harshe. A nan ne ya bayyana siffar Allah Maɗaukaki ta alƘadimu la auwala lahu[3], ya ce:

15. Azal1 yake tun azal2 yake ko azal3 ma

Ga Allah ba azal4 don babu kowa

(A.H. Wurno: Wa’azi)

 

Kalmar ‘azal’ ita ce Haliru ya yi rawarsa da ita, ya ba ta wata ma’ana daban. Manufar Haliru a nan ita ce ya kawar da ƙumshiyar lokaci daga tunanin mai saurare gaba ɗaya don gane siffar nan ta Allah Maɗaukaki, wato al-Ƙadimu la auwala lahu. Yadda za a iya fassara wannan baiti a jumlace da kalmomi biyu ko uku, watakila shi ne: Allah ne Azal don ya gabaci komi da kowa. Lura da cewa Haliru bai kawo kalmar ‘komi’ ba saboda kalmar ‘kowa’ ta isar mata. Kowa mai rayuwa ne saboda komi, idan kuwa aka kawo ‘kowa’ to lalle ‘komi’ ya wanzu don shi ne ‘kowa’ zai ci ya rayu. A wata fuska ana iya cewa Haliru ya kawo kalmar ‘kowa’ domin waɗanda ke cikin ƙumshiyar (misali, ɗan Adam) sun fi ɗaukaka bisa ga na cikin ‘komi’.

Kalmar ‘azal2’ ta cikin ɗangon farko sokakkiya ce wadda ‘azal’ ta uku da ta huɗu da kuma yankin jimlar /don babu kowa/ suka soke. A ƙarshe dai kalmar azal ta farko ita ce kurum wanzajjiya.

Mu’azu Haɗeja da Haliru Wurno waɗanda marubuta waƙoƙi ne sun yi amfani da salon dibilwa suka hau kan ƙereriyar bangon duniyar harshe. To su ma mawaƙan baka sukan hau ƙereriyar. Dubi wannan misali:

Fadawa ku bugan in buge ku

Mui ta faɗammu gidan duniya

Kun san ba a faɗa lahira

Ko don ku ka zuwa lahira

Narambaɗa ba ya zuwa lahira

Zama ya san ɗauke mai akai

Ko ya zo dawowa yakai

 (Ibrahim Narambaɗa: Toya Matsafa sadauki na Abdu/Baban Isa baban Buwai/[4]

 

Ba za a ce Narambaɗa yana inkarin tafiya lahira (mutuwa, a taƙaice) ba. Haka kuma ba za a ce Narambaɗa ya furta waɗannan ɗiya ba tare da wata ma’ana ba. To amma mece ce ma’anar? Marubucin wannan littafi yana ganin furucin Narambaɗa bai rasa nasaba da zamanin da mawaƙin ya tsara waƙar. Watakila Narambaɗa bai daɗe da zuwa wani gidan rediyo ba, musamman Gidan Rediyo na Kaduna. A shekarun da Narambaɗa ya rayu, rediyo da fayafayen naɗiyar magana na garmaho ba su daɗe da bayyana a ƙasar Hausa ba. Haka kuma Kaduna da wuraren naɗiyar magana wurare ne masu nisa ga Narambaɗa. Wannan sabuwar hikima ta ƙirƙiren zamani mai ban ta’ajibi ce ga Hausawa. To shi kuma Narambaɗa wata hikima da ya hango cikin wannan ƙirƙiren zamani ita ce, da zarar aka naɗi muryarsa ko ta duk wani mutum, to za a ji muryarsa har abada ko bayan ya mutu, kamar dai yana a gabanmu da ransa yana rera waƙarsa. A nan ke nan ko Narambaɗa /ya zo (lahira) dawowa yakai/!!!

A irin wannan tattaki kan ƙereriyar bangon harshe ne mawaƙi kan tuntsure ya afka cikin amfani da harshe ta hanyar da ta saɓa wa al’adun Hausawa. Misali shi ne waƙar da Abubakar Kassu Zurmi ya yi wa Na Gidan Duwa in da yake faɗin cewa wannan gwarzo ya je lahira amma saboda ba a tauri a can sai aka bar shi ya dawo duniya! Yadda Kassu ya bayyana wannan lamari ko kusa bai saɓuwa ga Hausawa domin ya saɓa wa addininsu.

 Ta amfani da wasu salailai kamar dibilwa (wanda aka gani a sama) da luguden sautuka (ƙarangiya) da kuma kacici-kacici, mawaƙi yana iya ƙulla magana mai ma’ana ba tare da wata matsala ba. Dubi yadda Garba Gwandu ya yaba Sarkin Yaƙin Gwandu, Abubakar Koko, cikin kirari da zuga:

Garba sinadari abin haɗa manyan gadaje

Zaki zaburo ka kai zama gun mazaje

Gwarzgarzaya ragargajgabrin gwaraje

 Alhaji Garba ɗan bani mulki ƙi garaje

(Alhaji Garba Gwandu: Yabon Sarkin Yaƙin Gwandu Abubakar Koko)

 

 Sautin /z/ = /j/ shi ne Garba Gwandu ya yi lugudensa da shi a ɗango na biyu, a yayin da a ɗango na uku ya lugudi sautin /z/ = /j/ da na /g/ da kuma na /r/. Mallakar da mawaƙin ya yi ma harshe ce ta ba shi damar harhaɗa kalmomi masu makamantan sautuka har ya ta da maganganu masu tsari da ma’ana. Lalubo waɗannan kalmomi daga duniyar harshe ba mawuyacin abu ba ne a wurinsa.

Mawaƙi mai iya dagula hankalin mai saurare ko karatu ne ta wasa da ma’anonin kalmomi waɗanda kowa ya san su, amma ya riƙe ɗaya daga cikinsu. Wato ta amfani da salon kacici-kacici sai ya bar kowa cikin zuzzurfan tunani kan ko me yake nufi.

A wani lokaci mawaƙi kan yi amfani da wannan salo na amfani da kacici-kacici sannan shi da kansa ya yi bayanin abin da yake nufi. Aƙilu Aliyu ya yi haka inda yake cewa:

1. Ƙulun ƙulufit abu dunƙule

 Ƙalau na ƙale ƙalubale

 

2. Ka cinci ka-ci miye abin

 Da ke yaɗo kuma dunƙule

 

3. Ya watsu ya barbazu tattare

 Da rassa ga shi a mulmule

 

4. Kadan ka ture zuciya

 Da ilmu ake ƙalubale

(Alhaji Aƙilu Aliyu: Waƙar Ƙalubale)

 

A baiti na ɗaya ne Aƙilu Aliyu ya fara siffanta mana abin da yake son mu gane. Ya ce wani abu ne wanda a cure (dunƙule) yake. A kuma baiti na biyu sai ya ƙara siffa ɗaya don ƙarin bayani, wato shi wannan abu bayan zamansa dunƙule, to kuma yana yin yabanya (yaɗo). Ko kuwa har yanzu ba mu gane ko mene ne ba? Don ya ba mu amsar wannan tambaya sai mawaƙin ya ƙara shigar da mu duhu ya ce wannan abu da ke dunƙule amma yake yaɗo, shi ne kuma ke watsuwa ya bazu sannan kuma ya yi rassa da yawa amma ya kasance a mulmule. Wannan amsa ita ce baiti na uku yake ɗauke da ita. A baiti na huɗu ne Aƙilu Aliyu ya fito fili ya faɗa mana cewa ai wannan abu dai shi ne ilmi.

Da wannan bayani ne za a iya gane cewa siffofin nan sun dace da ilmi. Ilmi ne kurum dukiyar da mai ita zai iya ya ɗiba ya ba wani amma kuma ba ta ragu ba. Shi ne kurum zai yi rassa (wato ɗaliban mai ilmi) su bazu cikin duniya amma kuma shi yana nan da haibarsa.

To amma a wani lokaci mawaƙi yakan sa bayaninsa a mala, su kuma manazarta ko masu saurare su yi ta shafar ƙwalluwar kansu don su gano wannan bayani. Dubi wannan waƙa mai baitoci shidda kacal:

1. Ina da garibi wa ka son in sanas sasa

Biɗah hankali ba za shi sa wa ka sama sa

Bale tafiya ko kai gudu ba ka cimma sa

Ku gai min da sab’in nunu deli ku ce masa

 Akwai ni da tsuntsu ko fa ya san kama tasa

 

2. Idan bai sani ba shi zo shi tambayi aƙili

Shi zage zuwa can tambaya inda kamili

Mutum shi yi biɗa da’ ahiri har ga awwali

Idan fa ya gane na sani ya yi hankali

 Ga tsarassa duk ba za ta samun kama tasa

 

3. Ana dafuwatai ammanin ba shi yin miya

A ci shi da nau’o’i akan ci shi shi ɗaya

Akan yi kamatai wane kaka tambaya

Misalin jikinai haɗɗalas da suhuliya

 Akwai shi ga daji har gida ana sama sa

 

4. Akwai shi ga dutsi mai biɗatai shikan fake

Ga icce shi hau kul ya zamo ba shi yin sake

Akwai shi ga ramu har tudu har cikin haki

Kurum ba jini ga jikinsa ba shi da fiffike

 Kurum babu gashi ko guda ga jiki nasa

 

5. Shina da ciki ai babu hanji shina da bai

Akaifa ƙashi har jijiya ba su zam garai

Kurum ba idanu ba wuya gunsa babu kai

Kurum babu nama babu rai kuma dai da rai

 Zama ba shi motsi gun jiki ya isam masa

 

6. Asuta da halbi ba shi sawak ka sama sa

Idan kay yi jifa kom matso taka far masa

Idan ka ganai ka zaburammai ka tsar masa

Idan kaf fake wai don shi haike ka kamma sa

 Waɗanga ba sun sa mai biɗatai shi sa masa

(Wazirin Sakkwato Muhammadu Buhari: Ina Da Garibi)

 

Mene ne ko kuma wane tsuntsun ne Waziri Buhari ke nufi? Marubucin wannan littafi har yanzu bai samu amsa mai gamsarwa ba, tun kuwa fiye da shekaru goma sha biyar ne ta shiga hannunsa.

Wasu suna da ra’ayin cewa iska marubucin waƙar ke nufi, wasu suka ce ai inwa ake nufi. Wasu ma cewa suka yi ai duniya ce Waziri Buhari ke nufi, a yayin da wasu suka ce zuciya ce, zuciya mai guri ba zuciya tsoka ba. Waɗannan ra’ayoyi watakila za su karɓu ta yin la’akari da sanin zuhudu da sufanci, musamman ganin cewa Waziri Buhari mallami ne kuma malizimcin zuhudu da sufanci.

To amma Sambo Waliyyi Giɗaɗawa yana da ra’ayin cewa abin da Waziri Buhari ke nufi shi ne ƙwai. Ya kafa hujjarsa da cewa watakila shi Waziri Buhari ya samu tasirin wasu littattafan faslsafar Larabci, domin a cikin irinsu ne shi kansa Sambo Waliyyi Giɗaɗawa ya ce ya taɓa cin karo da wani baiti wanda ya yi kama da tunanin da ke cikin wani ɓangare na wannan waƙa. Baitin Larabcin yana cewa:

Wa yu’kalu maɗbukhan lazizaan wa taratan

 Wa yuukalu mashwiyyan idha halla fil lahabi[5]

 

Ma’ana: Kuma wani lokaci akan ci shi dafaffe zad daɗi,

 Kana akan ci shi soyayye lokacin da mai ya nashe shi

 

Mawaƙi Yana Ɗaukar Kalmomi Da Rai

Mawaƙi mai jin kalmomi ne ta amfani da kunnuwansa da zuciyarsa da jikinsa da kuma ɗanɗanonsa. Haka kuma yana ganin kalmomi idan ya kalli abubuwa da abin da suke yi, har ya kawo kalmomin domin su ƙawata ko su munana ko su daɗanta, da dai makamancin haka. Yana iya ya jinjina kalmomi ya gane masu nauyi ko ‘yan lahe-lahe, ya gano masu gauni da kaifi da waɗanda suka dallashe. Yana iya gane kalmomi masu zurfin ciki, waɗanda ba tasiri guda ko ma’ana guda sukan kawo ga mutum ba. Shi ke jinjina kalmomi ya gano masu laushi ko kaushi, da masu ƙarfi da garɗi da daɗi, kai har ma da masu ɗaci ko bauri. Sannan ta fuskar ƙararsu yana iya gano masu amo da marasa amon. Misali, yayin da Haliru Wurno ya so ya kawo hoton yadda motarsa ta faɗi tare da shi ciki, ga yadda ya ce:

3. Da tab birkita taw wakita taƙ ƙara zubewa

Da tam mazaya tak karkata tak koma jicewa

Da taw wantsala tam mulmula niƙ ƙara ɗimewa

Da nif firgita nit tsorata kaina ka kaɗawa

Malakul mautu ga sannan nika hange da isowa

 

4. Ina kwance tana nan bisa taro bisa kanmu

Da manyansu da yaransu da kyar sunka cire mu

Gani na haka can kwance kamar za ta kashe mu

Duhu nata ƙaruffanta kujeri ka jice mu

Da saura na ka sha ma’u dalilinka fitowa

 

5. Na zabura na jirkita na koma ɗimewa

Ban gane gabas yamma bale dama arewa

Ji kaina ka ta motsi katarata ka kaɗawa

Idona ka hawaye ciki ƙalbi ka bugawa

Ganin na aza guri cike raina ka tunawa

 (Alƙali Haliru Wurno: Babban Bajini Bello Ƙanena)

 

A waɗannan baitoci Haliru ya yi amfani da salon amfani da kalmomi masu kaifin ma’ana da masu zurfin ma’ana domin ya ƙirƙiro salon zayyana wanda kuma da shi ne ya cusa mana hoton haɗarin da motarsa ta yi da shi ciki. Haka kuma kasancewar kalmomin nan kusa da juna a tsarin waƙar takan sa mai saurare ya ji irin yadda abubuwa suka auku da sauri kamar da ƙiftawar ijiya, abin da kuma shi ne ke aukuwa a yayin haɗarin mota. Kalmomin ‘birkita’ da ‘wakita’ da ‘zubewa’ da ‘mazaya’ da ‘karkata’ da ‘jicewa’ da ‘wantsala’ da kuma ‘mulmula’, duk su suka bayyana hanzarin wannan mota. Tashin hankalin da Haliru ya shiga ciki ya fito cikin kalmomin ‘ɗimewa’ da ‘firgita’ da ‘tsorata’ da ‘kaɗawa’ da kuma hangen mala’ikin mutuwa kusa da mawaƙin a baiti na 3, da kuma gaba ɗayan na 4 zuwa na 5, waɗanda suka haɗa da taron da ‘yan ba da ɗoki suka yi a kan Haliru. Rinchaɓin da ya auku ga Haliru da ƙarafan motarsa, salon zayyana ne mai kaifin ma’ana. Shi yana kwance a ƙasa bai iya taɓuka kome, ita kuwa motarsa tana a kansa sannan su kuma masu ƙoƙarin ceto shi suna a kan motar da shi kansa Halirun. Nauyi bisa nauyi!

Wannan ɗabi’a ta mawaƙi ita ta tilasta shi zama mafaraucin kalmomi. Idan ya farauto su to a can cikin ƙwaƙwalwarsa da zuciyarsa zai dinga ƙalailaice su ta hanyoyin da aka ambata ɗazu. Sai dai fa idan waƙa ta zo masa, ba kiran su ko tono su zai yi ba. Zuwa suke yi cikin tsarin da ya dace da haliyyar da yake ciki ko ya sa kansa ciki.

 Mawaƙi Maƙerin Maganganun Hikima Ne

Maganganun hikima na daga abubuwan da al’umma ta gada. Wannan gadon yana daga cikin al’adun al’umma. Waɗannan al’adu sun haɗa da tatsuniya (gatana) da kacici-kacici da gagara-gwari da salon magana da karin magana da ishara da dai sauransu. To wai shin wane ne ya ƙirƙiro waɗannan maganganun hikima a Hausa? Cikin rukunonin Hausawa wane rukuni ne ya ƙirƙiro su? Ko kuwa shin wane rukuni cikin rukunonin da suka ƙirƙiro maganganun hikima ake ganin shi ne a kan gaba?

Amsoshin waɗannan tambayoyi a mala suke a nan. Sai dai ba za a kasa iya cewa idan ba mawaƙa ne a kan gaba ba, to kuwa ba za su zamo a baya ba. A nan za a dubi mawaƙa a matsayin rukuni daga rukunonin da ke ƙirƙiro karin magana da sauransu.

Mawaƙi kan yi amfani da karin magana a matsayin salo. Salo kuwa hanyarsa ce ta isar da saƙonsa ga mai karatu ko sauraren waƙarsa. Akwai hanyoyi aƙalla guda uku da mawaƙi kan saka karin magana cikin waƙa ko bayan kawo shi kamar yadda Hausawa ke faɗar sa. Waɗannan kuwa su ne faɗaɗa karin magana da gutsure karin magana da kuma ƙirƙiro sabon karin magana. Yakan bi waɗannan hanyoyi saboda dalilai da dama, kamar ƙarin bayani da yin ishara da fitowa da saƙo a sarari da nuna gwaninta da cika wasu ƙa’idojin waƙa kamar yawan gaɓoɓi, da kuma kambama magana.

a) Faɗaɗa Karin Magana

Idan za a yi wa mutum nasiha da cewa ya kalli ko ya yi la’akari da haɗarin da ya auku ga wasu mutane a da, muddin dai a maganar yau-da-kullum ce a ke yi masa nasihar, to ana iya cewa: Wane ka dai ji abin da masu fasahar magana suka ce, in ka ga gemun ɗan’uwanka ya kama da wuta to shafa ma naka ruwa, ko kuwa? To amma shi mawaƙi ga yadda ya faɗi wannan karin magana da wannan manufa:

122.Sai ku hango gemun ɗan’uwa

 Da ya kama wuta da gaganiya

 

123.Don ku nemi ruwa ku yi yayyafi

 Kada ku ma naku ya sha wuya

 (Sa’adu Zungur: Arewa Jumhuriya Ko Mulukiya)

 

A nan Sa’adu Zungur ya yi amfani da karin maganar, amma fa ya sake masa kama ta hanyar bayyana mana yadda aka yi gemun ya kama da wuta, wato ‘‘da gaganiya’’. Ma’ana, ko dai shi ɗan’uwan ne ya yi gaganiya, ya kasance da rashin natsuwa, ko kuma gemun ne ya kama da wuta balbalbal, babu ƙauƙautawa. Haka kuma Sa’adu Zungur ya ci gaba da ƙara sake wa karin maganar kama da cewa mu nemo ruwa kamar na hadari masu yawa mu yi yayyafi kan namu gemu. Ya ƙara da cewa idan aka yi haka to namu gemun ba zai halaka ba.

Abin lura a nan shi ne, Sa’adu ya warwatsa wannan karin magana a cikin baitoci biyu. Wato sai ka tsittsinto kalmomin sannan ka iya tayar da karin maganar. Wannan kuwa manuniya ce ga cewa mawaƙi kan lallanƙwasa ko daddatsa karin magana. Yana iya lanƙwasa ko ya datsa ko ya gutsure ko ya faɗaɗa karin magana. Dubi yadda wani mawaƙi shi ko ya kawo wannan karin magana:

In ka ga gemun ɗan’uwanka cikin wuta

 Nemo ruwa ka zuba ma naka shaɓe-shaɓe

 (Alƙali Bello Giɗaɗawa: Hannunka Mai Sanda)

 

Alƙali Bello shi ma a nan amfani ya yi da salon kambamawa, kamar Sa’adu Zungur, domin ya ƙara fitowa da muhimmancin saƙonsa zuwa ga jama’a. Wannan saƙo shi ne, kare gemunka daga kamawa da wuta. Ya ce cikin wuta ba ‘ya kama da wuta’ ba kamar yadda karin maganar yake a maganar yau-da-kullum. Zuba ruwa za ka yi ba ‘shafa’ su za ka yi ba, kuma don gemun ya yi shaɓe-shaɓe ba ya kasance da ruwa sama-sama ba.

Alƙali Haliru Wurno a wata waƙarsa da ya kira ‘‘ Ko Ba Ka Raƙumi Ka San Cau’’, cewa ya yi:

Ji kai in ka ganai yashe

 Kutumbun ba shi tserewa

 

Jinin kai na gami da wuya

 Da sun rabu ba su komowa

Tumun dare ba ni zaɓen ka

 Tsaya in sake ɗaukowa

Ana iya shafa kan mussa

 Na jibda ba ka farawa

 

Ana iya kama ɗan buku

 Mijirya ba ka damƙowa

 

Fura aka kwankwaɗa amma

 Kunu kam sai da kurɓawa

Mutum in ya biɗo canji

 Abinai an na renawa

(Alƙali Haliru Wurno: Ko Ba Ka Raƙumi Ka San Cau)

Ga wasu ƙarin misalai:

(i)

 Giwa du’ abin da tah haifa

Ai an shedi bai zama taffa

Domin ya wuce shiga kwalfa

(Alhaji Garba Gwandu: Yabon Bajini Ya Zama Tilas, Waƙar Makaman Gwandu Balarabe)

 

(ii)

Inda Waziri nij ji swan giwa bai ɓacewa

Bai da awan na raƙumi ko a wajen taɓawa

Giwa du’ abin da tah haihwa bai ɗimewa

 Duka daji gidansu birni ab bai shigowa

 (Alhaji Garba Gwandu: Yabon Sarkin Yaƙin Gwandu Abubakar Koko)

 

(iii)

Alu namijin zuma mai wuyac cima

Kowah hi ka harbi shi sha kainai

 (Alhaji Musa Ɗanƙwairo: Shirya Kayan Faɗa)

 

(iv)

Ƙarya ce sukai

Wanda duk ka hwaɗin za ya yi ba ya yin kome

 (Ibrahim Narambaɗa:Amadun Bubakar Gwarzon Yari/ Dodo Na Alƙali)

 

b) Gutsure Karin Magana

Mawaƙi kan yi amfani da karin magana ta hanyar gutsure shi. Zai ambaci muhimman kalmomin da karin maganar ya ƙunsa, ya bar saura don mai saurare ko karatu ya cike su. Waɗannan muhimmam ƙumshiyoyin tunani ko kalmomi kan iya kasancewa ɗaya ko biyu ko uku, gwargwadon yadda karin maganar ba zai shige duhu ba. Misali, Hausawa kan ce ‘‘Dila sarkin dibara’’ ga mutumin da aka ga wayonsa ya faifaye. To domin mai saurare ya tuna da wannan karin magana ga abin da mawaƙi ya ce:

Na yi gabas wajen yanyawa

 Kila dibaratai ta ishe ni

 (Alƙali Haliru Wurno: Gudale)

 

c) Ƙirƙiro Karin Magana

 

A zamansa na mai mulkin harshe kuma maƙerin maganganun hikima, mawaƙi lalle yakan ƙera wa jama’arsa karuruwan magana. Wato mawaƙi kan faɗaɗa rumbun karin magana a tsawon zamani, ya ƙirƙiro sabbin karuruwan magana. Dubi wannan:

Mota idan ta ƙiya kura akai da ita

 In mas’ala ta yi tsauri sai a sake wata

 (Alƙali Bello Giɗaɗawa: Zuwa ga ‘Yan’uwa Maasu Tunani...)

 

Tabbas ɗango na farko a wannan baiti sabon karin magana ne. Hausawa sun kasance a duniya tun zamanin zamunna. To amma ba su san abin da ake kira ‘mota’ ba sai a ƙarni na ishirin bayan da Turawan mulkin mallaka suka ci ƙasar Hausa. Haka kuma faɗaɗa ma’anonin kalmar ‘kura’ su haɗa da katakon ɗaukar kaya mai tayoyi huɗu, bai auku a harshen Hausa ba sai a cikin ƙarnin. Sabnoda haka, mota idan ta ƙiya kura akai da ita, magana ce wadda ta zo ga Hausawa a wannan baiti cikin ƙirar karin magana kuma sabon karin magana a lokacin da aka yi waƙar da wannan baiti yake ciki.

Haka nan kuma a wata waƙa Alƙali Bello Giɗaɗawa ya ce:

Bari son ka rena ƙafarka don motad daɓe

 In ka ga an koro ka nemi wuri laɓe

 (Alƙali Bello Giɗaɗawa: Hannunka Mai Sanda)

 

Bayanin da ya gabata game da karin maganar /mota idan ta ƙiya kura akai da ita/ ya wadatar ga /bari son ka rena ƙafarka don motad daɓe/.

Shi ma mawaƙin baka ba ɗan tashi ka rama ne ba:

Ni Amadu Gwanna Ɗakingari

Haƙon bisa bai kama kumare

 

Jirgin sama ba a sa mai sanke

Ko an sa mai ana ɗebewa

 

Zama kusa maganin mai tcince

 

Manguro karuwa’ icce ta

Ga ta baƙa ɗiya jajjaye

 

In na tuna goro Gwanja za ni

Na tuna R.K, Ɗakingari

Malam Anaruwa wan Jaɓɓi

 

Muhammadu ɗan su Sarkin Gobir

Yaka na Saudi ‘yar mallammai

Sanyin ruwa ba shi kama bado

 (Amadu Gwamna Ɗakingari: Yabon Abubakar Ruwa Ɗakingari (R.K.))

 

Jirgin sama sabon abu ne cikin al’adun Hausawa saboda, da farko dai, ba Hausawa ne suka ƙirƙiro shi ba. Hasili kamar yadda mota ta zo masa cikin ƙarni na ishirin, shi ma a lokacin ne ya zo kuma daga baya. Ita ma ɗabi’ar sanya sanke a kan hanyar mota ga dukkan alamu an fara ta ne a ƙasar Hausa saboda yadda ruwan sama ke ɓata hanyar mota[6].

Ke nan a wannan baiti shi ma Amadu Gwamna Ɗakingari ya ƙirƙiro sabon karin magana ko kuma aƙalla ya taskace sabon karin magana.

Ga wani misali:

 

Tarago mai jan kaya

Jirgin bisa mai yat tcela’ uway yaya

Kana gaba rigimakka na biya dab baya

Ɗan Sanda

(Abubakar Kassu Zurmi: Mamman ɗan Sale/Tayin Kura kare ba ya son goyo nai)

Ta yin nazari kan irin rurin da jirgin sama ke yi ne Kassu Zurmi ya lura da abubuwa biyu. Na ɗaya babu wani abu da Bahaushe ya ƙirƙiro kuma babu wata dabba a ƙasar Hausa da ke ruri irin na jirgin sama. Hadari na ruwan sama kurum ke haka, shi kuwa yin Allah ne. Na biyu, Kassu ya lura da cewa sai jirgi ya wuce sannan zai ji wannan ruri. Sai bayan da jirgin sama ya shigo cikin duniyar tunanin Hausawa sannan suka lura da waɗannan abubuwa, kuma sanin haka ya ba Kassu Zurmi damar ƙirƙiro wannan karin magana.

 Mawaƙi Mallamin Al’umma Ne

Babu ja-in-ja cikin iƙirarin da ke cewa mawaƙi mallamin al’umma ne tun bayan da Musulunci ya zo ƙasar Hausa. Mun ga yadda waƙoƙin Wali Ɗanmasani, da ma wasu kamin sa, suka yi ƙoƙarin bayyana wa Hausawa sira (tarihin Manzo s.w.s.). To balle a ƙarni na 18 da 19 da Allah ya albarkaci ƙasar Hausa da malamai kamar Shehu Usmanu ɗan Fodiyo da Malam Muhammadu na Birnin Gwari da Malam Shi’itu ɗan Abdurra’ufu[7] da ƙanen Shehu, wato Mallam Abdullahi ɗan Fodiyo da ɗansa Muhammadu Bello da ‘yarsa Asma’u da tarin magoya bayansa. Duk waɗannan sun rubuta waƙoƙi domin su ilmantar da al’ummarsu addinin Musulunci da fannonin ilmi waɗanda ke da alaƙa da shi. Waƙoƙi kamar waƙar ‘Tabban Haƙiƙan’ da ta ‘Lalura’ na Shehu da waƙar ‘Tsarin Mulki irin na Musulunci’ da ta ‘Wa’azu’ na Abdullahi duk misalai ne da ke tabbatar da cewa mawaƙi mallamin al’umma ne. Wannan lamari ya ci gaba har zuwa ƙarni na 20 da wannan na 21 da muke ciki. Ta fuskar marubuta waƙoƙi ke nan.

Zaman mawaƙi mallamin al’ummar Hausawa bai tsaya ga marubuta waƙoƙi ba kuma bai fara gare su ba. Mawaƙan baka su ma mallaman wannan al’umma ne. Hasili sun riga takwarorinsu marubuta. Abin nufi shi ne waƙar baka ta riga rubutatta samuwa a ƙasar Hausa domin ita ce wadda ta fi rubutattar zama ta gargajiya.

Kafin Musulunci ya bayyana a wannan ƙasa waƙoƙin baka ne kurum Hausawa suke da. To amma wannan tangarɗa ba ta zama dalilin a ce mawaƙi bai kasance ɗaya daga cikin mallaman Hausawa ba. Wannan magana a fili take idan aka tuna da cewa mawaƙi maƙerin maganganun hikima ne ta fuskokin harshe da hanyar rayuwa?

Rashin ingantacciyar hanyar taskace waƙoƙin baka ya kasance babban dalilin da ya hana waƙoƙin Hausa na zamani mai tsawo kawowa gare mu a yau. To amma wannan ba zai raunana hasashen ba kan cewa waƙoƙin da muke da su waɗanda aka yi su a wannan zamani, musamman na ƙarni na 20, madubi ne na waƙoƙin ƙarnukan da suka shuɗe.

A kan wannan hujja ce muke iya kawo misalan da ke gabatar da mawaƙi a matsayin mallamin al’ummarsa ta ƙasar Hausa. Ibrahim Narambaɗa ya ce a wata waƙarsa:

Ai sarauta ban da nufin Allah ta

Da ɗibat ta akan yi da ƙarfi

 

Waɗanga da nag gaza ganewa

Da sun ga

 

Ana haka nan da sun yi

 

Gogarman Tudu jikan Sanda

Maza su ji tsoron ɗan Mai Hausa

 

Ku dangana tun ga uwaye

Ba duka ɗan sarki ba ka samun sarki

Wane ku dangana tun ga uwaye

Ba duka ɗan sarki ba ka samun sarki

 

Ɗan sarki duka yag ga sarauta

Ga ta kamak kusa tai mashi nisa

In dai bai yi sarautan nan ba

Sai ya kwana da mikin zucci

 

Ɗan sarki duka ab ba kowa

Ɗan sarki duka ab ba komi

Sannan yat tcira yawon ƙarya

Ya san ba ya sarauta

Sai fa shi kwan nan

Gobe shi kwan nan jibi

Dangi nai mashi Allah-waddai

Baƙam magana ba ɓaci ta ba

Amma ta ɗara ɓaci zahi

(Ibrahim Narambaɗa: Gogarman Tudu jikan Sanda/Maza su ji tsoron ɗan Mai Husa)

 

Waɗannan ɗiyan waƙa cike suke da ilmantarwa ga ‘ya’yan sarauta na ƙasar Hausa. Haka nan kuma suna ɗauke da karantarwa ga al’umma gaba ɗaya ta fuskar harshe da kuma rayuwa. A wannan ɓangare Narambaɗa ya taskace wa al’ummarsa kalmomin ‘‘Mai Hausa’’, waɗanda ke nufin Sarkin Musulmi. Haka kuma a ɓangaren Gobir da Kabi da Zamfara na ƙasar Hausa idan aka ce ‘Hausa’ abin da ake nufi shi ne Sakkwato saboda ita ce cibiyar ƙasar Hausa kafin zuwan Turawan mulkin mallaka.

A sashi ɗaya kuma Narambaɗa ya bayyana wa Hausawa cewa su lura cewa a cikin ma’amala, baƙar magana duk da yake ba zagi ce ba, amma fa a lokacin da aka yi wa mutum ita zai ji ta da zafi fiye da zagi. A Musulunce mutum yana iya jure zagi ya ƙyale domin ramawa daidai take da zagin kai da kai. To amma baƙar magana fa?

A inda Narambaɗa ya ɓarje guminsa shi ne wurin ‘ya’yan sarauta. Nan ne ya fara da yin tsokaci kan wani mugun halinsu da suke arewa su yafa wai sai sun gaji gidansu. Hakan ko yana faruwa ne ko da ɗan sarki ya san bai cancanta ba. Shi dai tun da ɗan sarki ne kamar ‘yan’uwansa to ya cancanta. Hasili da ya san ana yin sarauta da ƙarfin tuwo da kuwa ya hau gadon sarautar nan! To saboda wannan rashin aiki da hankali na ‘ya’yan sarauta ne Narambaɗa ya yi musu nasiha yana cewa shin wai me ya sa ba su lura da cewa ai ba dukkan iyaye da kakanninsu ne suka yi wannan sarauta ba. Ya kamata su sa idon basira su fahimci cewa fa a kowane lokaci mutum ɗaya ne tak ake naɗawa a matsayin sarki. Saboda haka, inji Narambaɗa, su bar wa Allah zaɓi.

Daga nan kuma sai Narambaɗa ya ilmantar da jama’a game da irin rayuwar ‘ya’yan sarauta ta fuskar tsananin gurin da suke da na zamowa magadan iyayensu. Ya faɗa mana cewa shi fa duk ɗan sarkin da ya ga sarautar gidansu ta faɗi kuma yake ganin shi ne mafi cancanta (kuma mafi yawan ‘ya’yan sarauta haka suke), amma kuma sai Allah ya ƙaddara ba shi aka naɗa ba, to lalle ko shakka babu wannan ɗan sarki zai kasance cikin mummunan baƙin ciki.[8]

Narambaɗa ya ƙara ilmantar da mu cewa duk ɗan sarkin da ya kasance bai da wani girma a idon jama’a, sannan kuma ya yadda girman ta hanyar zama ɗan raraka, to shi kam da shi da zama sarki haihata-haihata. Matsayinsa cikin ‘yan’uwansa shi ne abin takaici, abin Allah wadan naka ya lalace kuma abin yi wa tir!

4.6 Mai Gyaran Al’umma ne

Mawaƙi mutum ne wanda ke amfani da baiwar da Allah ya yi masa ya tsawaci al’ummarsa dangane da taɓarɓarewar halaye da al’adu na gari, kuma ya yi kashedi kan munanan abubuwan da ke ƙoƙarin zama jiki ga al’ummarsa. Haliru Wurno ya yi irin haka a waƙarsa mai suna ‘‘Yaƙi Da Rashin Tarbiyya’’. Ga misalin baitocinta:

8. Ji takaici ni kam ya isan

Sarkin sata mai son shi zan

Shi riƙe samu gona ta zan

Mulkinai mu ko duk mu zan

 Banzar banza Najeriya

 

 9. Mis sa haka wai ba a lura ba

 Amsar rashwa ba a bar shi ba

 Yau mallammai su ag gaba

 Su ci hanci had da bugun gaba

 Imani ya fita zucciya

 

 10. Wa’azin da sukai na a ba su na

 Suka suka yi ga sarakuna

 A rufe bakinsu da riguna

 Ko tafsirin dodoru na

 Ƙudurinsu su mallaki duniya

 

 11. Shafin kwalli ko karuwa

 Ga biɗar mata ‘yan ga-ruwa

 Da gida daji ko anguwa

 An san haka balle karuwa

 Wannan ita ak kan angaya

 …

17. Wac ce a yi mulki langadam

A ci irlin babba shina sudum

Riƙa garwashi hauninka dum

Tsare girma yanzu ka zam Sadam

 Shi ɗai ka riƙon Najeriya

...

 34. Ikon banza na shi akai

 A ci rashwa hanci ci akai

 Manyan nan su nay yad da kai

 Fadar kowa yau shi akai

 Yi da gaske ɗumi bari dariya

 …

 36. Cewa mulkin ga ka san na kai

 Ba mulki na ba da za shi kai

 Ga bukata kowa ba shi kai

 In babu biyayya sariƙai

 Ka zama manya Najeriya

 (Alƙali Haliru Wurno: Yaƙi Da Rashin Tarbiyya)

 

Alhaji Mamman Shata shi kuwa ya soki al’adar Hausawa ta yi wa ‘ya’yansu auren dole. Ya yi kira da cewa su daina wannan domin hanya ce ta lalacewar yara maza da mata. Ga yadda ya yi gyaran:

Amma na tambayi ‘ya’yan birni

Na tambayi ‘ya’yan ƙauye

Kowanne ya bi zancen Shata

Ka ji ‘yan matanku zuwa ga mazanku

Kowanne ya bi zancen Shata

Baba idan za ai man aure

Goggo idan za ai man aure

Inna idan za ai man aure

A bar ni in zaɓi fari kyakkyawa

Kadda a ba ni baƙi mummuna

Auren tilas ba aure ne ba

Shi ke sa wasu yawon banza

Don salla da Salatil Fati

Kai don Allah mata ku yi aure

(Alhaji Mamman Shata: Mata Ku Yi Aure)

 

 Mawaƙi Ne Tun Asali

Mawaƙi mutum ne amma yana da wasu ɗabi’un da ya keɓanta da su waɗanda kuma sakamakon kasancewarsa mawaƙi yake da su. Shi mutum ne wanda Allah ya yi wa baiwar tsara waƙa. Baiwa kuwa a nan tana nufin kyautar Allah Maɗaukaki ga bawansa, ba don wani ƙarfi ko dabara ko sani ko ƙoƙari nasa ba. Ba kuɗi ya sa ya sayo wannan iyawa ba. Ba koyo ya yi ya iya wannan iyawa ba, ba kuma gado ne wanda malami ko alƙali ya raba ba. Kai tsaye ne sai iyawar ta faɗo masa. Mai ba da kyauta, Allah Mai iyawa kuma Ma’ishi, shi ne wanda ya yi masa wannan iyawa. Wannan shi ne dalilin da ya sa Haliru Wurno ya ce:

Waƙe fasaha ne da yac cuɗe ka

Kuma ba karatu na ba in an ba ka

Ilmi dubu sai ka biɗo wani nasa

(Alƙali Haliru Wurno: Ma’anar Waƙa)

 

Abin da Haliru ke nuni da shi a nan shi ne, waƙa dai ba za ka je ka zauna a koya ma tsara ta ba domin fasaha ce, wato wai don mallam ya fahimtar da kai cewa abu kaza da kaza da kaza su ne suka haɗu suka yi waƙa kuma duk wanda ya tashi tsara waƙa sai ya bi su, wannan ba zai sa ka tsara ta ba. Mawaƙi idan yana tsara waƙa bai ma san da cewa yana bin ƙa’idojin ba. Ganin cewa ɗalibi ya tsara waƙa to da ma Allah ya yi shi cikin waɗanda ya yi wa baiwar tsara waƙa. Abin da Mallam ke iya yi kurum shi ne ya zaƙulo wannan baiwa, amma ba ya cusa ta ba[9].

Idan mun fahimta da cewa mawaƙi mutum ne wanda aka yi wa baiwar tsara waƙa sai kuma mu duba mu gani ta yaya ne wannan baiwa ke tasiri a kansa? Waɗanne ɗabi’u ne ke bayyana ga mawaƙi ya kasance mawaƙi?

 Mawaƙi Mulkin Harshe Yake Yi

Mawaƙi yana da wata ɗabi’i wadda ke sanya ya kasance mutum mai mulkin harshen da yake waƙarsa da shi. Shi ba bawan harshe ne kamar mu ba. Mawaƙi mutum ne mai jan harshe kamar mai jan alewa[10]. Mutum ne wanda a wajen sarrafa harshe ya kai har a kan ƙereriyar bangonsa, wato maƙurar harshe. Abin nufi a nan shi ne idan harshe wata duniya ce tamkar daro ko kamar duniyar wata da muke kallo, sannan kuma duniya ce wadda mutum zai iya tattaki har ya kai ga gaɓarta, to duk ƙoƙarin da sauran mutane za su yi na yin tattaki cikin duniyar nan ta harshe, maƙurarsu inda suke walawa ita ce cikin da’irar duniyar, ba za su iya kai a kan gaɓa ba. Mawaƙi ne kurum zai iya hawan gaɓar, ya wakita, ya yi tsalle har ma ya iya shatawa da gudu ba tare da ya tuntsure ba! Togensa guda ne tak: idan ya bugu da giyar ‘yancin sarrafa harshen![11] Wato dai shi mawaƙi, ko bayan tarayyar da ya yi da sauran mutane na walawa a tsakiyar duniyar harshe, yana da ƙarfin yin tattaki zuwa bangon duniyar, ya yi yadda yake so. Ga dai taswirar wannan duniyar harshe don ƙarin bayani ga wannan manufa:

 DUNIYAR HARSHE

Duniyar Harshe

JA = Filin rawar mawaƙi SHUƊI = Filin rawar sauran mutane da kuma mawaƙi

Jan fili shi ne wanda mawaƙi yake iya shiga, shi kuwa shuɗin fili shi ne na sauran mutane da kuma shi kansa mawaƙi.

Waƙa

Waƙa ita ce maƙerar mawaƙi. A nan ne yake narka kalmomi ya fito da saƙonsa zuwa ga al’umma. A nan ne kuma yake narka su ya yi maganganun hikima, hikima ta harshe ko ta hanyar rayuwa.

A nazarin waƙa ana iya bayyana ma’anar waƙa da cewa:

Waƙa tsararriyar maganar hikima ce da ta ƙunshi saƙo

cikin zaɓaɓɓun kalmomin da aka auna domin maganar

ta reru ba faɗuwa kurum ba.[12]

 

Waƙa magana ce ta tsakanin zukata ko bayan cewa tunani ma yana naƙaltar ta. Abin nufi a nan shi ne ita waƙa takan yi tasiri ne kai tsaye kan zuciya fiye da sauran nau’o’in magana.[13]

A fayyace ana iya cewa waƙa magana ce da aka zayyana, ba wadda aka sako kara-zube ba. Magana ce wadda aka aza bisa sanannun ko ayyanannun ƙa’idoji waɗanda ke daidaita furuci da sauti, su kuma tilasta zaɓar kalmomi domin dacewar ma’ana da furuci. Ta haka ne maganar take zuwa babu kaura da juna ta furuci ko kalmomi ta fuskar daidaiton tsawon gaɓoɓi, saɓanin magana ta yau-da-kullum.

Post a Comment

0 Comments