Ticker

6/recent/ticker-posts

Salo Asirin Waƙa na Farfesa Abdullahi Bayero Yahya [03 - Babi Na Biyu]

 Salo Asirin Waƙa

Salo Asirin Waƙa

Salo Asirin Waƙa
 

BABI NA BIYU

Ma’anar Salo Da Muhimman Tubalansa

Salo

Kalmar salo ba baƙuwa ba ce ga kowane Bahaushe. To amma inda gizo ke saƙarsa shi ne a nemi mutum ya kawo bayani mai gamsarwa kan abin da ya fahimta game da wannan abu da ake kira salo. A maimakon ya kawo jumla ko jumlolin da ke ayyana mana ko mene ne salo, sai ka tarar ya ƙare da ba mu misalan na salon. Idan ma ba a ankara ba sai ya laɓe ga ɓangare guda na rayuwa wanda tunaninsa ya kawo masa a matsayin gonar salo (kamar maganganun mata), ya yi ta kawo misalai ya kuma ce mana su ne ma’anar salo.

Wannan irin dibilwa da salo yake da idan mutum ya ƙuduri bayyana ma’arsa al’ada ce ta harshe, sannan kuma a gefe guda ɗabi’a ce ta ɗan Adam. Bisa ga ɗabi’a mutum ya fi jin sauƙin ya kawo abu a maimakon a nemi ya faɗi ko mene ne abin. Saboda haka ya fi jin sauƙin ya faɗi misalin abu da a ce ya faɗi ma’anarsa. Ya fi jin sauƙin ya nuna Ahmad ya ce shi ne Ahmad, maimakon a nemi ya faɗI ko wane ne Ahmad ta yadda ko a cikin dubun dubata aka ga Ahmad ana iya a gane shi ne Ahmad ɗin, ba wani Ahmad daban ba.

To amma fa duk wannan ba zai kawar da tambayarmu mai yi mana ƙaiƙayi ba. Mene ne salo?

Amsarmu tana nan cikin zamanin ƙuruciya. Mun sha jin mahaifiyar yaro tana ce wa ɗanta, ‘Kai raba ni da salo”, musamman idan yaron ya zo yana neman ta yarda ta yi masa wani abu da yake ganin idan da a kai tsaye ne ya ce ta yi masa shi, ba za ta yi ba.

Tambaya a nan ita ce: Me mahaifiyar wannan yaro take nufi da cewa ɗan yana da a yayin da ta yi furucinta? Ba tare da zurfafawa ba, ashe ba tana nufin cewa yaron yana da dabara ba? Wato yana son ya yi mata dabara. Yana son ya yi mata wayo. A taƙaice, yaron yana son ya bi wata hanya ya sa uwarsa ta yi wani abu. Saboda haka ashe a wannan hali, salo yana nufin dabara ko hanya ko wayo.

Ga alama ba a yi kuskure ba idan aka ce wannan ma’ana ta salo ita ce dahir a duk inda aka kaɗe aka raye ta kowace fuskar kalmar salo. Dubi ƙaulin Hausawa da suka yi na ‘salon magana’. Ai abin da wannan ke nufi bai wuce ‘wata magana daban da wadda aka saba yi ko ji’ ba. Magana ce da aka yi ta wata hanya ko dabara daban da yadda aka saba. Haka kuma ‘sabon salo’ yana nufin sabuwar hanya, hanyar da take daban da wadda aka saba da ita. ‘Wani salon rawa’ kuwa yana nufin wata dabara ko hanya ta yin rawa, ba wadda aka riga aka gani ba. Kazalika akwai sabulu akwai kuma ‘sabulun salo’, wato sabulu amma ba wanda ake saurin kawowa a zuciya ba. Sabulu ne na daban, wanda aka bi wata hanya ta musamman wajen yinsa.

Idan aka koma ga maganar uwa da ɗanta mai salo, a iya kawo wata tambaya kamar haka: Wane tasiri salon yaron zai yi a kan mahaifiyar? An dai lura cewa zai sa mahaifiyar ta yi masa abin da yake so. To ai kalmar ‘sa’ ita kanta tana bukatar a fayyace ta a irin wannan hali. Ana iya cewa, salon yaron zai burge mahaifiyarsa domin yana ganin salonsa zai ƙawata, ko kuma zai yi wa maganarsa kwalliya. Wato shi salo mai yin ƙawa ko kwalliya ne. A taƙaice, salo kwalliyar magana ce mai tasiri kan mai jin ta.

A nan ne kuma muke ganin ya kamata mu sake yin tambayarmu ta tun farin. Wato: Mene ne salo?

To amma kamin a ƙirƙiro jumla ko jumloli da za su tsaya a matsayin ma’anar salo, ya kamata a fito da wani abu a sarari wanda a cikin wannan tattaunawa aka mayar a bayan fage. Wannan abu kuwa shi ne, manufa ko saƙo ko jigo, wanda shi ne abin da salon yaronmu ke son isarwa ga mahaifiyarsa. A maganar yau da kullum akan ce ma’anar magana ko maƙasudinta. Duk dai abu guda ake nufi, saƙo ko jigo ko manufa. Ya danganta ga yanayin abin da ake magana a kai. Saboda haka kuma ana iya cewa salo, shi ke bayyana saƙo, shi ke kai saƙo inda aka nufa da shi.

Ta yin la’akari da gaba ɗayan tattaunawar da aka yi tun farko har zuwa sakin layin da ya gabaci wannan, ana iya kawo ma’anar salo da cewa, salo dabara ce ko hanya mai yin kwalliya ga abu domin abin ya kwarzanta ko ya bayyana. Idan kuwa za a yi wa wannan ma’ana gyara domin a bayyana salo a cikin nazarin waƙa. wanda shi ne fagen wannan littafin, ana iya a ce:

Salo yana nufin duk wata dabara ko hanya a cikin waƙa wadda mawaƙi ya bi domin ya isar da saƙon da yake son ya isar. Ita wannan dabara ko hanya tana yi wa waƙa kwalliya ta yadda saƙon waƙar zai isa ga mai saurare ko karatun waƙa[14]

 

Muhimman Tubalan Salo

Idan salo yana nufin duk wata dabara ko hanya da waƙa ta ƙunsa domin tabbatar da isar da saƙo ga mai ji ko karatu, to ashe kuwa abu ne mawuyaci mutum ya ƙididdige tubalansa. Abin nufi a nan shi ne, sai dai a kimanta faɗar abubuwan da salo ya ƙunsa masu tabbatar da ingancinsa, amma ba a kawo su duka ba. Tattare da wannan kuma shi ne, ba zai yiwu ba a iya ƙididdige ire-iren salo. Za a jinkirta kawo dalilin wannan magana ta ƙarshe a nan gaba. Yanzu tsokaci ne kan magana ta farko za mu yi, wato muhimman tubalan salo.

Ana iya kawo aƙalla muhimman tubalai takwas waɗanda kuma masana da dama suka lura da su[15]. Waɗannan tubalan gina salo kuwa su ne:

1. Mallakar kalmomi5. Rauji

2. Ƙirar jumla6. Tsarin tunani

3. Nau’o’in jumla7. Jadaddawa

4. Siffantawa8. Dangatakar tsari

1. Mallakar Kalmomi

Mawaƙi yana bukatar ya kasance fasihi ne ga zaɓen kalmomin da zai yi amfani da su a cikin waƙarsa domin salonta ya inganta har saƙon da ta ƙunsa ya isa ga waɗanda aka nufa da shi. A mallakar kalmomi fasahar mawaƙi ita ce ƙwarewarsa ga sanin kalmar da ta dace a wuri kaza, ta fuskar ma’anarta da kuma tasirin da za yi wajen fahimtar maganar (wato ɗango ko baiti ko ma waƙar ɗungurungum) da ta fito daga cikinta. Saboda haka ashe mawaƙi ko bayan kasancewarsa mai iya yin wannan irin zaɓin, tilas ne ya zamo shi kansa rumbu ne na kalmomi masu sigogin ma’ana da ƙari iri ɗaya, kuma yana iya kawo su ba da wahala ba. Misali ƙirin da tilin da wilik da siɗik da ɗiɗin, duk kalmomi ne masu bayyana yadda launin baƙi yake. Haka kuma ƙirar waɗannan kalmomi iri ɗaya ce. Wato gaɓar farko ta kowace kalma gajeruwa ce a yayin da gaɓa ta biyu ta kasance doguwa.

Wace kalma ce daga kalmomin nan guda biyar ta fi dacewa da ɗango ko baiti ko waƙar mawaƙi? Iya zaɓo kalmar shi ake nufi da mallakar kalmomi a fagen salon waƙa. Dubi waɗannan tagwayen baitoci waɗanda kowane rukunin tagwai a cikinsu ya yi amfani da wata kalma mai bayyana ma’anar za’ida daban da ta ɗan’uwansa:

a. 20 Dubi bayanta tun daƙ ƙafa har ka zo

 Gun wuya ya yi sanda sumul bai ɗaya

21. Na ji zancen barewa tana yo niya

 Na yi ƙari faɗin na fi kowa wuya

 

b. 20 Dubi bayanta tun daƙ ƙafa har ka zo

 Gun wuya ya yi sanda sumul bai ɗaya

 

21. Na ji zancen barewa tana yo niya,

 Na yi zwari faɗin na fi kowa wuya

 

c. 20 Dubi bayanta tun daƙ ƙafa har ka zo,

 Gun wuya ya yi sanda sumul bai ɗaya

 

21. Na ji zancen barewa tana yo niya,

 Na yi zuƙu faɗin na fi kowa wuya.

(Fardiya)

 

To a cikin rukunonin tagwayen baitocin nan uku, a ganinka wane rukuni ne ya fi bayyana saƙon da mawaƙin ke son isarwa, wato za’idar da ya ji barewa na faɗin cewa ta tafka game da kyawon wuyanta a ɓangaren ɗaya, da kuma kyawon wuyan matar da mawaƙin ke bayani a kai a ɗaya ɓangaren?.

Idan kana bukatar ka yi wa kowane rukuni adalci, to ya kamata ka yi la’akari da waɗannan abubuwa kamin ka yanke hukumcinka:

1. Kowane rukunin baitoci yana ƙoƙarin nuna cewa wuyan matar ya fi na kowa kyau, har da na barewa.

2. Kowane rukunin baitoci yana nuna cewa a lokacin da barewa ta ga wuyan wannan mata sai ta farga tare da yin da-na-sani kan bugun gaban da ta sha yi wai ta fi kowa kyawon wuya, ashe ba ta sani ba wuyan wannan mata ya fi nata, nesa ba kusa ba.

3. Muhimmancin kalmomi kamar zance da tana da yo niya da kuma faɗin, a cikin rukunonin baitocin.

Wannan shi ake kira mallakar kalmomi wanda yana daga cikin tubalan da ke inganta salon waƙa. Sanin kalmomi da iya zaɓo su don amfani da su a cikin waƙa mataki ne na kyautata salo da kuma isar da saƙo. Da yake ita waƙa ta fi sifantuwa da yin la’akari da amfani da gaɓa a maimakon kalma, ya zama wajibi ga mawaƙi ya yi la’akari da ƙirar gaɓoɓin kalma, ko bayan ya san ma’anar kalmar

2. Ƙirar Jumla

Ƙirar jumla a fagen salon waƙa tana nufin yadda tsarin kalmomi yake a cikin abin da ake kira jumlar waƙa. Ita kuwa jumlar waƙa tana iya kasancewa jumla kamar yadda aka san ta a fagen nahawun harshe. Amma kuma ba lalle ne ta kasance hakan a koyaushe ba. Salon waƙa yana kawo ƙunshiyar magana guda cikin tsarin da ya dace da bukatun isar da saƙon da yake nufin isarwa, da kuma bukatun da suka haɗa da na kari da rauji

Ta ɓangaren bukatun isar da saƙo, salo yakan gina jumlarsa ta amfani da kalmomin da suka kasance su ne muhimmai. Wato zai yi watsi da duk wata kalma wadda ba tilas ba, ko da kuwa a ganin nahawun harshe ba wadda ake iya yin watsi da ita ba ce. Alal misali a cikin waƙarsa mai suna Waƙar Habbi Alƙali Haliru Wurno ya nuna wannan ɗabi’a a waɗannan baitoci:

20. Kwad damƙi damtcen Habbi ba shi baƙin ciki,

Maganatta ta hi zuma ruwa ba su kai ba.

 

21. Tsaye zaune Habbi irinta kam ba a gan ta ba,

Na dubi mata ba kamar mahbuba.

 (Alƙali Alhaji Haliru Wurno: Waƙar Habbi)

 

A ɗango na biyu na baiti na 20 Haliru Wurno ya yi watsi da kalmomin zaƙi da balle da su. Wato da a wajen mai nahawu ne wannan ɗango zai kasance kamar haka:

Maganatta ta hi zuma zaƙi balle ruwa su ba su kai ba.

Shi kuwa ɗangon farko na baiti na 21, aƙalla kalmar ko ita ce za a iya cewa Haliru ya yi watsi da ita, amma idan aka matsa za a iya cewa ya yi watsi ne da ko a ……ko a…., a cikin ɗangon. Saboda haka wannan ɗango a wurin mai nahawu zai kasance kamar haka:

Ko a tsaye, ko a zaune Habbi irinta kam ba a gan ta ba

Bayan yin watsi da kalmomin da ba muhimmai ba a cikin ƙirar jumla, salo yakan gina jumlarsa da ƙirar da mai nahawu zai nace cewa an jirkice ta. Wato gaba ta koma baya, ko tsakiyar ta zo a farko, ko a ƙarshe. Dubi ɗango na biyar na wata waƙar Haliru Wurno da ya yabi Alhaji Bello Yahya inda yake cewa:

14. Babban bajini Bello ƙane ka zama wana,

 Haskenmu ɗiyan Baba ina son ka ga raina,

 Na Abbas bahagon Manuga walla maɗi na

 Ba don asuli wanga da yah hau bisa kaina

 Tabshi nika yo ma na kiɗi za ni kiɗawa.

 (Alƙali Haliru Wurno: Yabon Bello Yahya Sakatare)

 

A wajen malamin nahawu wannan ɗango a jirkice Haliru ya kawo shi. Idan aka ɗauki yanki ɗaya wanda ya faro daga kalmar /tabshi/ ya ƙare da kalmar /kiɗi/, shi malamin nahawu zai bukaci a sa ƙirar jumlar kamar haka:

Kiɗi na tabshi nika yo ma

 

Ko kuma:

Kiɗin tabshi nika yo ma

Haka kuma salo yakan gina jumla da kalmomin da nahawunsu bai daidaitu da na gaba ɗayan jumlar ba. Wato idan a maganar yau da kullum ne za a furta kalmar, to tilas ne a sake mata kama. A ɗango na uku da na huɗu Alhaji Shehu Alkanci ya sa kalmomin ‘sokewa’ da ‘duƙawa’ yin irin wannan zama na doya da man ja tsakaninsu da ɗangogin:

 Annabi dum yabonai kamas sabo na ba shi shuɗewa.

Tun farko yabo nai akai haƙ ƙarshe ba a ƙarewa,

Komi anka ce mai haƙiƙan na ba za a sokewa,

Girmanai hawa ɗai shikai kullum ba za shi duƙawa.

Don Allahu yaɗ ɗaukaka shi ga talikkai ga danginai

 (Alƙali A.Shehu Alkanci: Yabon Annabi Muhammadu).

 

Abin da za a lura da shi a nan shi ne cewa kalmar ‘sokewa’ a nahawunce, ‘soke’ za a sa ta a cikin ɗango na uku, sannan ita kuma kalmar ‘duƙawa’ a ɗango na huɗu a sa ta ‘duƙa’. To amma Shehu Alkanci ya san da cewa yin haka zai tilasta shi ya ƙara kalmar ‘ba’ a gaban kalmomin. Shi kuwa bai bukatar yin haka saboda ɗangogin za su fanɗare ta fuskar ƙafiya. A taƙaice ga yadda ɗangogin za su kasance a maganar mai nahawu:

ɗango na uku:

Komi anka ce mai haƙiƙan na ba za a soke ba ɗango na huɗu:

Girmanai hawa ɗai shikai kullum ba za shi duƙa ba.

Ya dace a nan a lura da wata ƙira ta jumla da salon waƙa kan iya haddasarwa. Ko bayan zaman bambaraƙƙwai da salo kan sa kalmomi yi cikin jumla, yakan kuma kawo jumlolin da ba cikakku (kamilallu) ba ta fuskar nahawu. Ɗango na uku da na huɗu na waƙar Shehu Alƙanci da aka kawo misali a sama, kyawawan misalai ne kuma na irin jumlolin da ba su cika ba. Sai dai abin fahimta a nan shi ne cewa rashin cikar jumlar da salo ya haifar ba abin da ke hana ko dagula isar da saƙon da jumla ko waƙa take ɗauke da shi ne ba. Wato dai salo bai karɓar jumlar da ba ta cika ba muddin ba za ta biya wannan bukata ta isar da saƙo ba.

3. Nau’o’in Jumla

Salon waƙa yakan kawo jumloli mabambanta waɗanda saƙonsu kan daidaita da haliyyar waƙa, wato susar zuciya da waƙa ta ƙunsa wadda kuma kan shiga cikin zuciyar mai saurare ko karatun waƙar[16]. Waɗannan mabambantan jumloli su ake nufi da nau’o’in jumlolin da salon waƙa yake da. Akan sami jumloli waɗanda ambato ne na abu a yayin da wasu suke tambayoyi ne. A wasu lokuta kuma sai ka sami jumloli ne da aka kawo su da bakin wani. Samuwar irin waɗannan jumloli ita kan sa a ce waƙar ta ƙunshi kalaman fiye da mutum ɗaya. To kuma salon da ake kira salon hira shi ya fi ƙunsar irin waɗannan jumlolin aron baki. Haka kuma a cikin nau’o’in jumla akwai jumla mai umurni da kuma mai ɗauke da kalmomi masu nuni da cewa akwai alamar motsin rai.

Muhimmin abin la’akari a nan shi ne, cewa a cikin waƙa duk waɗannan jumloli ba su bukatar alamomin rubutu kamar yadda zube ko wasan kwaikwayo ke bukata. Salo ya riga ya tanadi zuwan jumlolin cikin waƙa ba tare da alamomin ba.

4. Siffantawa

Zai fi kyawo idan aka fahimci cewa siffantawa nau’i ne na salo mai babban muhimmanci a cikin waƙa. Matsayin siffantawa kuwa tamkar baza ce da akan ce da ita ake rawa. Wato rashin salon siffantawa a cikin waƙa abu ne da ba a tunani tun da shi ne kan gaba wajen kawo wa mai saurare ko karatu saƙon waƙa yadda mawaƙi yake son a ji ko a kalle shi.

Da yake za a faɗaɗa sosai kan salon siffantawa a can gaba cikin wannan littafi, a yanzu zai wadatar da mai karatu idan aka kawo ma’anar salon kurum. Ga kuma ma’anar:

Salon siffantawa shi ne faffaɗan salon da ya tara surori ko sifofin da mawaƙi ya bayyana abu; salo ne da ke kawo hoton abu yadda mawaƙi ke bukatar mai karatu ko sauraren waƙarsa ya kalle shi da ido zuciyarsa ko tunaninsa; salon siffantawa hoto ne da kalmomi suka kawo.

 

5. Rauji

 Rauji yana nufin,

…zubin sauti a tsare a kan kari, ba kara-zube ba,…. Maimai na sauti a tsari takamaimai.[17]

Rashin rauji shi ne muhimmin dalili na farko da ke sa a ce maganar da aka karanta ba waƙa ce ba. Rauji shi ne asasin reruwar waƙa. Shi yake daidaita tafiyar waƙa tare da bugawar zuciya. Haka kuma rauji bai rasa danganta ta ƙuƙut da haliyyar waƙa. ko bayan sauran abubuwan da za a iya hangowa, raujin waɗannan baitoci kan yi ishara cewa zuciya mawaƙinsu ɗauke take da saƙo cikin fara’a:

Murna nikai sheawa nikai duk ko’ina

Koyaushe na sam ban bari ba togiya

 

Ga zuciya a cikin jiki ta bungulo

Sabon jini na zarce doki gomiya

 

Yau dug gari ya haskake ba mishkila

Ƙamshin furanni ko’ina kake ya gaya

 

Dangi na tsuntsu kafatan waƙa sukai

Haka na itace ba tsayi sai rausaya

 

Sanyi da zafi babu su duka sun gusa

Luɗufi salama ga aminci ya tsaya

 (Mun Yi Zance Kan Waya)

 

A taƙaice rauji ya ƙunshi maimai a tsare na sauti, ko aukuwa da daidaita ƙima (yawa) da kuma yawan gaɓoɓi, wato kari.

6. Tsarin tunani

Salon waƙa shi ke fitar da yadda zaren tunanin waƙa yake a cikinta. Wato salo shi ne kan ja zaren tunanin waƙa ta yadda saƙo zai fito a cikin saƙar da ta dace da shi har mai saurare ko karatu ya fahimce shi. Manufa a nan ita ce saƙo kan zo cikin waƙa mataki-mataki, zango na bin zango. Da waɗannan matakai ko zanguna ne za a iya fahimtar kasancewar salo mai sauƙi ko mai rikitarwa. Salo ne kan tsayar da wurin da wani tunani zai zauna. Wato ya ce tunani kaza ya zauna kamin wancan amma bayan wannan, sannan kuma har ila yau shi zai keɓe tsawon da saƙo kaza zai ɗauka a cikin waƙa. Duk waɗannan iyakoki tubalai ne da ake gina tsarin tunani a cikin waƙa.

7. Jaddadawa

Abin da ake nufi da jadaddawa shi ne yadda waɗansu kalmomi ko jumloli ko ɗangogi, ko ma baitoci da yanki-yanki na zaren tuani suka sami ƙarfafa fiye da waɗansu a cikin waƙa. Salo ne ke ɗauke da nauyin haifar da wannan jadaddawa. Wato shi ne yake da hanyoyin yin haka. Ɗaya daga cikin waɗannan hanyoyi kuwa ita ce maimaita kalma ko magana.

8. Dangantakar tsari

Mece ce alaƙar kalmomi da junansu a cikin waƙa? Mece ce alaƙar jumloli da junansu, ko baitoci ko zanguna da junansu a cikin waƙa? Mece ce alaƙar waɗannan da fahimtar saƙon waƙa? Amshoshin waɗannan tambayoyi su ne abin da ake kira dangantakar tsari a fagen salon waƙa. Salo shi ke ginuwa da wannan tubali. Yana daga cikin tubalan gina salon waƙa, ya kasance akwai irin wannan dangantaka da ke haifar da fahimtar saƙon waƙa.

Waɗannan tubalai guda takwas muhimmai ne wajen gina duk wani abu da za a kira salon waƙa. Su ne kuma waɗanda rashinsu cikin salo zai raunana shi. Raunanan salo kuwa shi ke daƙilar da fahimtar saƙo, ya kuma haifar da waƙar da Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo kan ce Hausawa na karɓar ta da furucin ‘ba laifi’ idan sun yi kara, idan kuwa ba su rufe ba, kai tsaye sai su ce, ‘ba tai min ba’[18].

Post a Comment

0 Comments