Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Saka Al-Kur’ani A Waya 📲

 Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Yaya hukuncin saka Ƙur’ani a waya a musulunci? a kan kalli batsa a wayar, a kan turo batsa baka sani ba ma, sannan kuma a kan shiga bayi dashi. Ina neman Bayani game da Saka kur’ani a waya.

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Hakika wannan zamani ne na kimiyya da fasaha (technology), kimiyya ta mamaye komai, da alkhairinta ko sharrinta.

Daga cikin alkhairints akwai sanya Al-Kur’ani a cikin na’ura kamar wayar hannu. Yawaitar kimiyya ya sa mutane na ta tambayoyi domin sanin Halal

da Haram a cikin addinin mu. Ina rokon Allah da yakarama mai tambaya Ilimi, fahimta da dacewa a kan kyakkyawan aiki.

Babu laifi a sanya Al-Kur’ani a na’ura mai kwakwalwa ( kamar waya, cassetes, CD/DVD plates, flash, computers etc).

Amma wajibi ne a tsare alfarmansa da darajarsa a kan hakan.

Hukuncin mu’amala da batsa nanan a kan Haramci, saidai baishafi Al-Kur’anin da ke cikin waya ba. Duk da cewa suna cikin waya ɗaya, to amma ko wanne yana mazauninsa.

Sai dai idan hakan yana taɓa darajar Al-Kur’anin da ke cikin wayar, to a yi gaggawan tsare martabar Al-Kur’ani, tahanyar kawar da batsar a cikin wayar. An tsinewa duk mai kallon tsiracin wani.

 

Makaruhi ne a shiga da wayar ko na’urar da ke ɗauke da Al-Kur’ani idan gilashin na’urar/wayar na buɗe da Al-Kur’anin kuma ana ganinsa a gilashin (screen). idan gilashin wayar baya nuna (displaying the text of Ƙur’an) ayoyin Al-Kur’ani a fili. Ko kuma wayar na kashe (swich off), ko ta yi lumm da duhu ba a ganin komai na Al-Kur’ani a gilashinta. To, idan gilashin wayar bai nuna Al-Kur’ani ba, babu komai.

WALLAHU A'ALAM

Ku Kasance Damu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/EPG7wVPlgxRFR4R9CdR8xY

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

Post a Comment

0 Comments