ME YA SA AKA BAMBANTA NAMIJI DA MACE A WAJAN RABON GADO ?

     𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum mallam me ne ne hukuncin wanda ke kokarin ganin an baiwa mace kason da aka bawa namiji wajen rabon gado?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa’alaikum assalam. Ya saɓawa Allah, Hakan kuma zai iya fitar da Shi daga musulunci in har ya yi gangancin haka, saboda kokari ne na warware hukuncin da Allah ya zartar. Allah da kansa ya raba gado bai wakilta wani don ya raba ba, ya bawa kowa hakkinsa gwargwadon kusancinsa da mamaci da kuma masalahar da Allah ya duba, wacce ya fi kowa saninta.

    Daga cikin hikimomin da suka sanya shariar Musulunci ta bambanta tsakanin mace da namiji a rabon gado shi ne: kasancewar hidimar namiji ta fi ta mace, yawancin mace idan tana karama tana karkashin kulawar mahaifinta, idan kuma ta yi aure tana komawa cikin kulawar mijinta. Allah ya yi alkawarin wuta mai kuna ga duk Wanda ya Saɓawa ayoyin rabon gado a cikin suratun Nisa’i aya:14, kamar yadda ya yi alkawarin Aljanna mai koramu ga wanda ya bi rabon da ya yi a cikin aya ta:13 a waccar Surat.

    Duk Wanda ya kiyaye dokokin Allah tabbas zai kiyaye shi, Wanda ya Saɓawa Allah, to yana nan a madakata, kuma mabuwayi ne mai tsananin karfi kamar yadda ayoyin Alƙur’ani masu yawa suka tabbatar.

    Allah ne mafi sani.

    Dr. Jamilu Zarewa

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

     

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.