Ticker

6/recent/ticker-posts

Hanyoyin Rage Tsananin Sha'awa

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assslamu alaikum, Malm ko akwai wata magani da zan sha don daina sha'awa ko rageta, wllh ina da matsaninciyar sha'awa wanda ko da yaushe inna ciikinta shi ne nake tsoron faɗawa halaka, don Allah a taimaka ni budurwa ce.

𝐀𝐌𝐒𝐀👇

Wa'alaikumussalamu. Toh da farko dai lallai ki Kamewa daka gane-gane domin kallace-kallacen wasu abubuwa da hotunan tsiraici masu motsi sha'awa yana kai mutum zuwa haram. Idan kina chating da samari mai motsa sha'awa ki ji tsoron Allah ki daina. Ki yawaita yin azumi Ki daina hirar batsa da maza ko mata yan'uwanki.

Hanyoyin rage tsananin shaawa ga maza ko mata

Hanyar da za a rage tsananin sha'awa ga wadanda ALLAH madaukakin sarki yajarabce shi da Ita.

1. Shan ruwa mai sanyi makwalwa dai-dai.

2. Za a samo kuzbara busassa wanda aka yi garinta kwatankwacin karamin cokali sai azuba aruwan mai sanyi da yamma har zuwa asuba sai asanya sukari a sha, Insha ALLAH yana saukaka tsananin sha'awa ga namiji ko mace. Amma idan akwai hali yin Aure yafi, idan kuma mace ɗaya gareka ka kara su zama biyu, idan biyu ne kanada hali kara ta uku, idan ukune kanada hali to kakara ta huɗu, domin karika samun cikakkiyar gamsuwa, Ubangiji Allah ya sa mu dace Ameen.

.

3. Za a samo wani haki da'ake cemasa Arrajla sai arika tafasawa ana shan sa shi ma yana saukaka tsananin sha'awa ga maza ko mata, za ki iya samun sa amma sai dai a Kano.

4. Ko kuma ka samo zait Kafuur sai arika diga ɗan kaɗan a cikin kofin shayi suka ce idan ana shan wannan yana kashe tsananin wutar sha'awa...... Amma lallai idan da hali yin aure yafi... Ko kuma yin Kari ga maza!!!

5. Ko kuma a samo Yansun da kako sai arika tafasawa ana sha, shi ma yana saukaka tsananin sha'awa.

6. Ko a samo kwayoyin Salak Irin wanda masu lambu suke shukawa yafito sannan su dasa shi yagirma ya zama Salak, to wannan kwayoyin da'ake yafawa su za ki samo sai kirika tafasawa kina sha suka ce wannan hanya yana yanke tsananin sha'awa gaba ɗaya, sannan wanda yake fama da yawan mafalakai ko da yaushe amma da wannan hanyar za a iya samun waraka.

Ubangiji Allah yabamu dacewa, masu yawan yimana tambaya a kan yadda za su rage tsananin sha'awa ga hanya...... Lallai ga wanda yake da tsananin sha'awa ko bashida da mata.. ko ba ta da miji, kuma babu halin yin Aure to amaimakon yin Istiminai (musterbution) to kwara bin ɗaya daga cikin waɗannan hanyoyin domin asami sauki!!!

Allah ta'ala ya sa mu dace

Ku Kasance Da mu Cikin Wannan Group Domin Ilimantarwa Tare Da Faɗakarwa a Sunnah.

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/DTrJJCF04ƘpACEtA7hyu4R

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments