Idan
ka gama sanin komai, ya za a yi wani mutum ya zo maka daga waje
ya mallake ka? Ba zai yuwu ba! Na ga wata makaranta
da wani ya...
Hanyoyin Cin Nasara a
Rayuwa 31: Duk Abu Naka Naka Ne
Baban Manar Alƙasim
Zauren Markazus Sunnah
Sakaci da rashin kulawa ko
rashin sani su ne manyan abubuwan dake sanyawa mu rasa damar dake hannunmu ko
mu bar ta wani ya ƙwace
mana, da farko fara gina kanka tukun, yi ƙoƙari ka sami ginshiƙi mai ƙarfin
gaske, kar ka yarda ka yi abu a kan jahilci, in kamfanin gyaran mashin za ka
gina binciki kanka tukun, shin kana da kuÉ—in
da zai ba ka damar aiwatar da wannan aikin? In ba ka da shi to ya za a yi ka
samu? Ilimin aikin dai yana kanka kuÉ—in
aiwatarwan ne ba bu.
.
Da farko tsaya ka karanci
sana'ar da za ka fara, shiga ciki a matsayinka na mai koyo, yi ƙoƙari
ka san komai nata, kayan aiki, abubuwan da ake buƙata,
masu kyau da jabu, kudadensu, dadewarsu, bambance-bambancen dake tsakanin
kamfanoni, lokutan da suka fi dacewa da inda ya kamata a yi saboda yawan mabuƙata, ya zamanto dai a matsayinka na mai
koyon aiki ba abin da ba ka sani ba, albashi in ka zo daukar ma'aikata da za su
yi maka bayani kan kayan aiki da sauransu ba abin da ba ka sani ba, kuma ba
wanda zai yi ƙoƙarin cutarka ko bata maka aiki.
.
Na koyar a wata makaranta ta
Misho, inda na ga hedimastan koyaushe yana zagawa azuzuwa yana ganin darussan
da ake koyarwa, da lokutan da ake koyarwan, wata rana ya amshi wani aji ya
koyar ko ya yi musu tambayoyi don ganin shin abin da suke buƙata malaman suke ba su kokuwa? Na yi
mamakin ƙwaƙwalwar
mutumin yadda ya san komai kai har da sunan daliban, ba abin da malami zai fada
wanda bai sani ba, sai na tambaya, ya aka yi ya san duk waÉ—annan
abubuwan? Sai aka ce ya koyar na tsawon shekaru da dama kafin ya kai ga riƙe makarantar a hannunsa, ashe asali ma
ba ɗan ƙasa ba ne, amma yana tsari mai ƙarfin gaske, koyarwar ta taimake shi sanin
komai.
.
Idan ka gama sanin komai, ya za a yi wani mutum ya zo maka daga waje
ya mallake ka? Ba zai yuwu ba! Na ga
wata makaranta da wani ya so gudanar da ita. Ya tanaji komai amma bai da kudi, sai suka
hada hannu da wani mai abin hannunsa, a ƙarshe
aka fara rigimar shin wa ma yake da makarantar tukun? Wanda ya fi ƙarfinka sai ya dauki hannunka ya mare ka
da shi, kusan abin da aka yi kenan, mutumin farko da a ce yana da kuÉ—insa
sai ya ci gaba da gudanar da lamuransa shi kaÉ—ai
ba zai jawo kowa ba.
.
Duk abin da za ka yi in dai
kai da ƙarfinka za ka yi aiki wani da dukiyarsa
kar ka yarda a ce komai shi zai yi, wani zai ce kar ka damu, ko nawa kake so ni
zan dauki nauyi, in ka yarda da wannan to ko shakka babu ka sayi wuƙar yanka kanka, sanya taka dukiyar kuma
ka yi aiki da ƙarfinka, ba yadda zai
dawo wata rana ya yi farfagandar cewa komai nasa ne don shi ya yi, kai ma ka
sanya kuÉ—inka,
ka yi aiki da ƙwaƙwalwarka sannan ka ba da lokacinka
daidai gwargwado, abubuwan dake faruwa a duniya yanzu yadda ka san ba lahira a
gaban mutane.
.
Akwai wata makaranta da wani
ya so gudanarwa, shi ya ke da wuri a hannunsa, sai ya jawo wani babban malami
wanda ya yarda da shi sosai, ya danƙa
komai a hannunsa, sai mutumin ya yi aiki da wannan damar ya maida mai wurin
yaronsa ya yi ta yi masa bauta na tsawon shekaru, sai dai ya É—an gutsuro
a wata ya miƙa masa, ba wanda ya
san abin da ake ciki, a ƙarshe
da yake mai wurin shi ma ba nasa ne na kansa ba sai mutumin ya kori shi wai bai
gamsu da irin gudummuwar da yake badawa ba, idan kana da rai ba abin da ba za
ka ji ba, waÉ—annan su ne abubuwan da ni na gani da
idona Allah ne kaÉ—ai ya san abubuwan dake
faruwa a wasu wuraren.
.
Da a ce mutuminnan ya koyo
aikin, ya fara da kansa bai janyo kowa ba, shi yake gudanar da komai ba wanda
zai zo rana tsaka ya mamaye masa wuri, balle ya tuhume shi da rashin gaskiya
har a ƙarshe ya ce zai kore shi, duk sana'ar da
za ka shiga yi ƙoƙari ka san gabanta da bayanta yadda ba
wani abin da zai boyu maka, kana da cikakken 'yanci, kana da duk wata dama da
za ka dauki matakin da kake so, ba tare da wani ya yi aiki da ƙwaƙwalwarka
ya cuce ka ba, in kana gaya wa kanka cewa ba za ka iya kaza ba ina tabbatar
maka daga lojacin da wani ya karbe maka wannan damar sai yadda ya yi da kai.
.
Za a kai yadda ba za ka iya
zartar da komai ba sai abin da ya so, shi kuma abin da ya ce ka yi ba ka da
makawa, ko kafin ka farga ya yi maka babbar illa, don duk abin da zai amfane ka
ba zai yarda da shi ba, duk kuma wata hanya da za ka bi wace za ta nuna maka
hanyar daidai ba zai yarda ka san ta ba, taka ta ƙare
kenan, ka bude idanunka, ma'ana duk lokacin da ka gano cewa nasararka tana kan
dakinka ne to ka gina matakalanka da kanka, ka hau da kanka ka ciro, ka sani in
ka tura wani ya ciro maka to shi ma fa yana so.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.