Ticker

6/recent/ticker-posts

Kwazazzabo A Hanyar Ƙauna



An ce ‘garin so ba ya nisa,’ ba don rashin nisa ko ƙalubale da ke tattare da tafiyar ba, sai don shi so ‘mai hana ganin laifi ne.’ Duk da kasancewarsa ‘makahon aiki,’ akan samu lokutan da maɗaci ke tarfuwa cikin maɗinsa. Ɗaya daga cikin mafarin irin waɗannan tangarɗa shi ne yarda da da’ifan hadisan sheɗan game da zamantakewa, musamman irin ta soyayya. Bahaushe na da samfuran ire-iren waɗannan kalaman da suka shahara wurin raba kan masoya cikin maganganunsa na yau da kullum. Waɗannan baitoci sun dubi kalaman da ke ƙasa a matsayin ‘Kwazazzabo A Hanyar Ƙauna’:
 “Idan mace ta nuna so, za ta sha wahala a hannun namiji!”
“Idan namiji ya nuna so, zai sha wahala a hannun mace!”

Na yi tofin Allah-tsine a waɗannan zantuka inda a ƙarshe na rufe da cewa: “A so shi ne nau ra’ayi!”
----------------------------------


08133529736


----------------------------------


1.      Kunne suka ɗau zance,
Sautin ga ya zan mance?

2.      Sautin ya ratsa sifika,
Nan wayar da na ɗauka.

3.      Ya doki fatar kunne,
Ciki ya yi kan aune.

4.      Ya ƙwanƙwasa wa dodo,
Gidansa can na na gado.

5.      A nan ya san babu zama,
Ya ɗauki saƙo shi ma.

6.      Ya doshi fadar kayi, (head)
Can ya je yak kayi. (took to)

7.      Sarki wato ƙwaƙwala,
A nan ya ba da sanarwa.

8.      Jini shi ne ɗan saƙo,
Ya kai shi saƙo-saƙo.

9.      Sai zuciya ta yi nauyi,
Sai duk jiki ya yi sanyi.

10.  Tunani sai ya yi zarya,
Ya rinƙa yin gewanya.

11.  Dukan jiki ya yi lakwas,
Ya mai gudu sa’i takwas.

12.  Kogin tunani ya kafe,
Kamar ƙanƙarar safe.

13.  Miyon baki yai yauƙi,
Ɗacinsa ko ba sauƙi.

14.  Idanduna sun yi ruwa,
Suna batun lumshewa.

15.  Lakar jiki ta yi lakas,
Dukan jiki yai mankas.

16.  Na ji ni duk nai lakus,
Ya mai wuni kan kuskus.

17.  “Idan mace tai zurfi-
Kogi na so ta yi laifi.

18.  Za tai kwanan ƙunci,
Domin ta yo ganganci.”

19.  Wannan batu yai muni,
Baƙi wulik a kamanni.

20.  Tushensa ko sheɗan ne,
Salon ɓata zumunta ne.

21.  Hanyar saɓa abota ne,
Tushen raba masoya ne.

22.  Mafarin tarzoma ne,
Silan kai ga rabewa ne.

23.  Salon kau da tunani ne,
Gwarin kai na mutane ne.

24.  Ko su mazan mene ne?
Batun suke mui aune.

25.  “Bayyana so garaje ne,
Nema wa kai wahala ne.”

26.  Me ya hana mu lura ne?
Wanne za mu kama ne?

27.  Ni kam na san ƙarya ne,
So silan zama lau ne.

28.  Hanyar sada zumunta ne,
Mafarin riƙon ƙauna ne.

29.  Ina a ce dai mu gane?
Mene ne son asali ne?

30.  Ina mu san yarda ne?
Riƙon hanun juna ne?

31.  Ina mu san marari ne?
Tarairayar juna ne?

32.  Ina mu san shauƙi na?
Da tai makon juna ne?

33.  Ina musan sa wa ne-
A rai an zamto ɗai ne?

34.  Ina mu san jigo ne?
Sinadarin rayuwa ne?

35.  Ina mu san duk mai so-
Ba ya cutar da abin so?

36.  Ina mu san mace mai so-
Ba ta cutar da mijin so?

37.  Ina a san miji mai so-
Bai cucin matar mai so?

38.  Ina a san in ga so-
An zam ɗai dalilin so?

39.  Na so a so a sanya so,
Ya zam ana son mai so.

40.  Idan da so a san da so,
A gane so da silan so.

41.  A samu sirrin riƙe so,
A ware so da rashin so.

42.  Kai zuciya akwai batu,
Wasunsu ba su ambatu.

43.  Na sakaya na dunƙula,
Na cure na ko mumula.

44.  Na sallama wa nazari,
Ya binciko shi sarari.

45.  Af! Na fara sambatu,
Ba basmala farin batu.

46.  Ubangiji daɗo tsira,
Ga manzo baban Zara.

47.  Alaye duk saka da su,
Sahabu jimlatan da su.

48.  Hamda Ilahu Rahimi,
Kai ne ka tarfan illimi.

49.  Abu-Ubaida ne ya yi,
A so shi ne nau ra’ayi.

Juma’a, 04/01/2019
2:20am

Post a Comment

0 Comments