𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum malam, ya ƙoƙari? To, Allah ya taimaka. Malam, tambayata ita ce: Wai mene ne hukuncin namijin da idan zai fita ba ya wa matarsa sallama ko gaya mata ya fita, amma yana so ta yi masa addu'ar Allah ya tsare? Haka kuma idan ya dawo, ba ya yi mata sallama, amma yana so ta yi masa sannu da zuwa. Sai ita kuma tace haramun ne, ba za ta yi ba; idan bai gaya mata ya fita ba, ba za ta ce masa Allah ya tsare ba, idan kuma ya dawo bai yi mata sallama ba, ita ma ba za ta yi masa sannu da zuwa ba. To malam, yaya wannan abin yake? Ya halatta a gare ta ta ƙwale shi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam
warahmatullahi wabarakatuh.
A shari'ar Musulunci, wajibi
ne miji ya yi wa matarsa sallama idan ya shiga gida, kuma yana da kyau ya sanar
da ita idan zai fita. Amma rashin yin hakan ba ya halasta wa matar ta ki yi
masa addu'a "Allah ya tsare" ko ta ki tarbar sa da sannu da zuwa ba,
domin biyayya da mutunta miji suna da nata matsayi.
Ba wajibi ba ne a shari'ar
Musulunci miji ya fada wa matarsa duk lokacin da zai fita daga gida, amma hakan
yana da kyau domin kwanciyar hankali da kuma sanin halin da ake ciki. Kuma yana
kawo wa matarsa nutsuwa kuma yana hana fargaba, yana kara nuna girmamawa da
kuma kyautata zama a tsakaninsu.
Allah ya wajabta yin sallama
lokacin shiga kowane gida, har da gidan mutum na kansa. A cikin Suratus-Nur aya
ta 61:
... ؕ فَاِذَا
دَخَلۡتُمۡ بُيُوۡتًا فَسَلِّمُوۡا عَلٰٓى اَنۡفُسِكُمۡ تَحِيَّةً مِّنۡ عِنۡدِ
اللّٰهِ مُبٰرَكَةً طَيِّبَةً ؕ كَذٰلِكَ يُبَيِّنُ اللّٰهُ لَـكُمُ الۡاٰيٰتِ
لَعَلَّكُمۡ تَعۡقِلُوۡنَ
...To, idan kun shiga wasu
gidaje, ku yi sallama a kan kawunanku, gaisuwa ta daga wurin Allah mai albarka,
mai daɗi.
Kamar wancan ne Allah Yake bayyana muku ayoyinSa, tsammaninku ku yi hankali.
(Surah: An-Noor, Ayat: 61).
Manzon Allah (Sallallahu
Alaihi Wasallam) ya ce wa Anas ɗan Malik: "Ya kai ɗana!
Idan za ka shiga gurin iyalinka ka yi sallama, zai zama albarka a gare ka da
kuma mutanen gidanka." (Tirmidhi).
Idan kina fuskantar wannan
matsalar, yana da kyau ki zaunar da mijinki cikin lallashi da nuna ƙauna, ki tunatar da shi wannan sunnah ta
Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) domin gidanku ya ci gaba da samun
albarka da zaman lafiya.
A cikin hadisin da ke cikin
Sahih Muslim, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya bayyana cewa idan
mutum ya shiga gidansa bai ambaci sunan Allah ba (wato bai yi sallama ba),
Shaidan yana cewa da sauran shaidanu: “Kun sami wurin kwana a daren nan.” Wannan
yana janyo yawan fada, rashin fahimta, da ɓacin
rai a tsakanin miji da mata. Idan mutum ya shiga gida ya ambaci sunan Allah (ya
yi sallama), shaiɗan yakan ce wa sauran shaiɗanu:
"Ba ku da masauki a wannan gidan yau." Idan miji ya shiga gida da
sallama da ambaton Allah, shaidan yana fita daga gidan, kuma zaman lafiya da
albarka suna tabbata tsakaninsa da matarsa.
Mijin da yake shiga gida ba
tare da ya yi wa matarsa ko iyalinsa sallama ba ya bar babban alheri, ya kuma
saɓa wa
koyarwar Alƙur'ani da Sunnah,
domin yin sallama lokacin shiga gida Sunna ce mai ƙarfi (wasu malamai sun ce wajibi ne) da
ke kawo albarka da kariya ga gida. Shiga gida babu sallama dabi'a ce ta rashin
kulawa da rashin kyautata wa iyali. Ya kamata miji ya lazimci yin sallama domin
samun rahamar Allah a gidansa.
Yin sallama yana sanar da
mace cewa mijinta ne ya shigo, hakan yana hana ta tsorata ko firgita. Amma tana
iya firgita idan ta ji mutum ya bayyana a kanta farat ɗaya
ba tare da ta ji motsi ko sallama ba. Idan miji ya shigo bai yi sallama ba,
mace za ta iya riga shi yin sallamar domin tunatar da shi cikin ruwan sanyi da
hikima.
Malaman Musulunci sun
bayyana cewa, koda mutum ya shiga gidan da babu kowa a ciki, Sunna ne ya yi
sallama ta hanyar cewa: "ASSALAMU ALAINA WA 'ALA
'IBADILLAHIS-SALIHIN." Ko kuma Ya ce: ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI
WABARAKATUH. Ko da babu kowa a gidan, shari'a ta nuna mutum ya yi sallama domin
akwai mala'iku da aljanu musulmai masu zama a wurin.
Saboda haka wajibi ne miji
ya yi wa matarsa sallama idan ya shiga gida, kuma yana da kyau ya sanar da ita
idan zai fita. Amma rashin yin hakan ba ya halasta wa matar ta ki yi masa
addu'a "Allah ya tsare" ko ta ki tarbar sa da sannu da zuwa ba, Rashin
yi masa addu'a "Allah ya tsare" ko "sannu da zuwa" saboda
zafin rai ko ramuwar gayya kuskure ne kuma rashin biyayya ne. Idan ta ki saboda
ta ce sai ya gyara nashi laifin, tana kara rura wutar saɓani
tsakaninsu ne. Ya kamata ta yi hakuri ta yi masa addu'a da maraba, sannan ta yi
masa sallama domin tunatar da shi cikin ruwan sanyi da hikima.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.