Ticker

6/recent/ticker-posts

Dafa-Dukan Shinkafa Da Na Shinkafa Da Wake Da Dafa-Duka Mai Kayan Hadi Da Yawa

Abubuwan Da Ke Ciki

Dafa-Dukan Shinkafa

a. Albasa

b. Gishiri

c. Kayan Yaji

d. Magi

e. Mai

f. Ruwa

g. Shinkafa

h. Tarugu

i. Tattasai

j. Tumatur

An kawo bayanin dafa-dukan shinkafa a ƙ ar ƙ ashin 9.1.1 da ke babi na tara. Yana da kyau a lura cewa, dafa-dukan shinkafa a yau na da bambanci matu ƙ a da ta gargajiya. A zamanance akan sarrafa dafa-dukan shinkafa cikin nau’o’i da salailai daban-daban. Yayin samar da dafa-dukan shinkafa a yau, ana iya ha ɗ a shinkafar da ɗ aya ko fiye daga cikin wa ɗ annan:

a. Dankalin Hausa

b. Dankalin Turawa

c. Doya

d. Makaroni

e. Taliya

f. Wake

Dafa-Dukan Shinkafa  da Wake

a. Albasa

b. Gishiri

c. Kayan ciki

d. Kayan yaji

e. Magi

f. Mai

g. Ruwa

h. Shinkafa

i. Tarugu

j. Tattasai

k. Tumatur

l. Wake

Ita ma wannan  dafa-duka kamar wadda ta gabata ta ke. Za a dafa wake  daban a kuma tafasa kayan ciki da Albasa . Sannan za a jajjaga kayan miya  da kayan yaji a soya. Daga nan a tafasa shinkafa daban. Sai kuma a yi sanwa a saka magi da gishiri tare da kayan ciki. Idan ta tafasa sai a saka waken da aka dafa tare da shinkafa. Idan ta yi a sauke tukunya .

Dafa-Duka Mai  Kayan Haɗi da Yawa

i. Alayyafu

ii. Albasa

iii. Doya

iv. Kabbaji

v. Karas

vi. Kayan yaji

vii. Kori

viii. Magi

ix. Mai

x. Makaroni

xi. Naman kaza ko nama da kifi

xii. Ruwa

xiii. Shinkafa

xiv. Taliya

xv. Tarugu

xvi. Tattasai

xvii. Tumatur

xviii. Wake

Ita ma wannan  dafa-duka zamani ne ya zo da ita, Bahaushe  ya sami fasahar gudanar da ita ne a dalilin cu ɗ anyarsa da wasu al’ummomi dabn-daban. A duk lokacin da aka ƙ uduri aniyar gudanar da ita, da farko za a wanke  alayyafu da albasa  da kabeji da karas a yanka a aje a gefe. Sannan a jajjaga tarugu da tattasai da albasa da tumatur wuri ɗaya kar a niƙa shi sosai kamar na miyar tumatur, ana saka masa ’yar kanwa a ciki kaɗan don ta gusar da tsami . Za kuma a tafasa nama da gishiri da magi da kori a aje gefe, idan kuma kifi ne, a ɗanyensa za a tafasa shi, in kuma busasshe ne za a saka ruwan zafi  a wanke shi a cire masa ƙaya ajiye domin ya tsane.

Za a yanka doya ƙanana-ƙanana a wanke  wake  a tafasa sannan ajiye gefe guda. Za a dafa shinkafa tafasa guda a sauke. Daga nan sai a soya nama a cire shi, sai kuma a soya jajjage. Idan ya soyu a saka kayan yaji da tafarnuwa. Za a yi sanwa tare da ruwan nama, idan kifi ne ba za a saka shi ba, sai a saka magi da gishiri da kori. In ya tafasa za a saka shinkafa da doya da wake a bar su zuwa wani lokaci, sai a saka taliya da makaroni. Idan suka ɗan jima, sai a saka kabeji da alayyafu da karas sannan a yanka albasa . Yana da kyau a kula da adadin ruwan da za a sa yayin sanwa, domin yawaita ruwa na sanya abincin ya kwaɓe.


Citation (Manazartar Littafin):   Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

Get a copy:
To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
+2348133529736

You can also write an email to:

Post a Comment

0 Comments