"Dutci Sittin da Arba'in ɗai babu,
Su ag ga zuriyam Mujaddadi,
Da su suka jihwam munahuki,
Sai bobawa ya barkace"
Inji Makaɗa Abubakar Amadu (Kassu Zurmi) a cikin Waƙarsa ta Ɗan Tauri, Bala Ƙonanne Gummi. Dama Kassu Zurmi Tasbaha/Casbaha ya ke nufi domin akasari tana da ɗa/ƙwara 99 ne, idan aka tara /haɗa 60 da 39(Arba'in a cire ɗaya) za a samu 99. Askr/Askar da Musulmi ke yi ta hanyar amfani da Tasbaha/Casbaha shi ne Kassu Zurmi ke nufi da "Jifar Munafuki" domin kariya ce da kuma barkata ko kwance wani shiri ko makircin mak'iyi /abokin adawa. Ya ɗora zancensa akan Major Chukwuma Nzeogu Kaduna ne da ya jagoranci kisan gillar da suka yiwa Firimiyan Jihar Arewa, Sir Ahmadu Bello GCON KBE, Sardaunan Sakkwato ranar 15 ga watan Janairu na shekarar 1966. Sai dai duk da wannan aika - aikar basu cimma cikar gurinsu ba domin sun "barkace" sanadiyar Alƙunutin da suka sha daga al'ummar musulmi da Ƙassu Zurmi ya kira da Zuriyar Mujaddadi (Watau Sheikh Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi) su Chukwuma Bobayi kenan.
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.