Ticker

6/recent/ticker-posts

Zumuntar Fasaha: Kamancin Daidaito Tsakanin Waƙar ‘Mu Yaƙi Jahilci’ Ta Malam Mu’azu Haɗeja, Da Waƙar ‘Yaƙi Da Jahilci’ Ta Alhaji Ɗahiru Musa Jahun Bauchi.

Article Citation: Yankara, M. M. and Babba, N. (2021). Zumuntar Fasaha: Kamancin Daidaito Tsakanin Wakar ‘Mu Yaki Jahilci’ ta Malam Mu’azu Hadeja, da Wakar ‘Yaki da Jahilci’ ta Alhaji Dahiru Musa Jahun Bauchi. Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies, 2(4). Department of Nigerian Languages. Sokoto: Usmanu Ɗanfodiyo University. P 123-135.

Zumuntar Fasaha: Kamancin Daidaito Tsakanin Waƙar ‘Mu Yaqi Jahilci’ Ta Malam Mu’azu Haɗeja, Da Waƙar ‘Yaƙi Da Jahilci’ Ta Alhaji Ɗahiru Musa Jahun Bauchi.

Muhammad Musa Yankara
Sashen Hausa
Jami’ar Gwamnatin Tarayya Dutsin-ma,
Jihar Katsina.
+234 806 2367 496
esemwaiy12@gmail.com 

Da

 Nasiru Babba
Sashen Hausa
Jami’ar Gwamnatin Tarayya Dutsin-ma,
Jihar Katsina.
+234 803 7466 414
nasbab22@yahoo.com

 

Tsakure

Rubutattun waƙoƙin Hausa, ɓangare ne na adabin zamani mai matuƙar muhimmanci, wajen isar da saƙo ga al’umma, wanda ya shafi fannoni daban-daban na rayuwarsu. Marubuta da daman gaske sun yi amfani da wannan hanya wurin cimma manufofinsu da muradunsu, tun bayan bayyanar hasken ilimin karatu da rubutu. Tauraruwar rubutattun waƙoƙin Hausa ta fara haskawa ne, tun a wajajen ƙarni na 17 da 18; sai dai kuma ba su samu cikakkiyar ranar shanya garinsu tare da tumbatsa ba, sai a ƙarni na ashirin, bayan shigowar karatun boko, inda aka sami mawallafa ‘yan boko suka rinƙa rubuta waƙoƙin kan manufofi daban-daban na rayuwa. Malam Mu’azu Haɗeja[1] da Alhaji Ɗahiru Musa Jahun[2] suna cikin mashahuran marubuta waƙoƙin Hausa, da tauraruwarsu ta haska a wannan ƙarni. Manufar wannan takarda ita ce, lalubar wani abu na zumuntar fasaha tsakanin waƙoƙin Sha’iran biyu masu kamar zubi iri ɗaya, dangane da abin da ya shafi yaƙi da jahilci.

 

1.0 Gabatarwa

Ilimi makami ne na yaqar munanan abubuwan da jahilci kan kawo wa al’umma. Kowace al’umma da irin qalubalen da take fuskanta dangane da barazanar jahilci da durqushewar ilimi. Duk da yawaitar hanyoyin koyo da koyarwa da ake da su, amma har yanzu ana iya cewa jahilci ya yi kaka-gida musamman a wannan qarni na mu da muke ciki. Idan aka ce jahilci ana nufin rashin sani, shi kuwa ilimi yana da ma’anar sanin wani abu ke nan da ya shafi inganta rayuwa.

Tun tale-tale, malamai suke qoqarin faxakar da al’umma ta fuskoki daban-daban kan muhimmancin ilimi da nusasshe su illolin jahilci. A lokacin jihadin Shehu Usmanu Xanfodiyo (1804), da almajiransa, sun yi amfani da waqoqi wajen ilimantarwa da faxakarwa da wa’azantar da al’umma. Haka abin ya gangaro har qarni na ishirin, a inda aka sami malamai da marubuta waqoqi musamman a cikin rubutun boko, suka ci gaba da xabbaqa wannan aiki na faxakarwa da ilimantarwa.

Marubuta irin su Malam Mu’azu Haxeja da Alhaji Xahiru Musa Jahun suna daga cikin ire-iren malamai marubuta da aka samu a Q20 (1900) waxanda waqoqinsu suka yi tasiri ga al’umma, saboda hanqoronsu da fatansu shi ne al’umma ta samu ci gaba ta fuskar yaqar jahilcin da ke tattare da ita.

Muradin wannan takarda ita ce, fitar da zumuncin tunani tsakanin waqoqi biyu na marubuta biyu (Malam Mu’azu Haxeja da ya yi waqar ‘Mu Yaqi Jahilci’ da kuma Alhaji Xahiru Musa Jahun da ya yi waqar ‘Yaqi da Jahilci’). Manufar yin hakan kuwa shi ne nuna irin qawancen da mawallafan suka yi tsakaninsu dangane da manufa. Marubutan sun gina waqoqin nasu a kan tunani iri xaya game da jahilci da yadda yake addabar a’umma. Wataqila hasashen fasahar da suka zuba a waqoqinsu wancan lokacin ita ta zama hanyar da za ta vulle ga al’ummar wannan lokaci. Ko ba komai, Hausawa na cewa ‘Da tsohuwar zuma ake yin magani’. Ana cewa ‘Ido ba mudu ba ne, amma ya san qima’. Ta yiwu hakan yana da alaqa da zancensu na ‘Da muguwar rawa, gwamma qin tashi’.

2.0 Tarihin Mawallafa (Malam Mu’azu Haɗeja da Alhaji Ɗahiru Musa Jahun) a Taƙaice

An haifi Malam Mu’azu Haɗeja cikin unguwar Kilabakori, a shekarar 1918, a cikin garin Haɗejiya. Mahaifinsa shi ne Abdullahi ɗan Abdulmumini, mahaifiyarsa kuma ana kiranta da Zuga, amma sunanta na yanka shi ne Fatima[3]. Malam Mu’azu ya sami kyakkyawar tarbiyya daga iyayensa, da horo na zama yaron kirki da hazaƙa wurin aiki. Ya fara karatun allo (Muhammadiyya) tun yana da shekaru uku a duniya, a makarantar Malam Alhamdu cikin garin Haɗejiya. A nan ne ya fara koyon karatun babbaƙu kuma ya ci gaba da karatun Alƙur’ani har ya sauke.

Malam Mu’azu ya samu ilimin boko, inda ya fara tun daga elementare har zuwa kwalejin horar da malamai. Sannan ya yi aikace-aikacen gwamnati, kuma ya riƙe muƙamai da dama, a wurare daban-daban.

Ana kyautata tunanin Malam Mu’azu Haɗeja ya fara sha’awar waƙa ne tun yana karatu a Midil ta Kano, dalilin wani Basakkwace mai suna Maikaturu, wanda ya shahara wurin waƙa. Daga nan ne, Malam Mu’azu Haɗeja ya fara ‘yan wallafe-wallafensa, har dai Allah ya tarfa wa garinsa nono, likkafa ta ci gaba.

Shi kuwa Alhaji Ɗahiru Musa Jahun, hasashe na nuna an haife shi ne tsakanin shekarar 1941 zuwa 1942 a unguwar Jahun da ke cikin garin Bauchi. Alhaji Ɗahiru Musa Jahun ya fara karatun Muhammadiyya a wata makarantar Islamiyya ta Malam Ladan, a unguwar Kur da ke Bauchi. Ya yi karatu a makarantar malam Maigari da makarantar malam Baƙo, kafin daga baya ya koma hannun babban yayansa da karatu, inda cikin shekaru biyu ya sauke Alƙur’ani. Bayan ya zama matashi, sai ya tafi yawon buɗe ido a garin Gombe inda ya haɗu da wani malami mai suna malam Murshidi wanda a hannunsa ya ƙara faɗaɗa karatunsa na addini.

Ta ɓangaren ilimin boko kuwa, Alhaji Ɗahiru Musa Jahun an bar shi a baya, duk da sha’awar da yake da shi. Sai dai ya koyi haɗa haruffa a wajen abokansa wanda hakan ya sa, ya iya rubutu da karatun Hausa sosai.

Alhaji Ɗahiru Musa Jahun bai gaji waƙa ba domin, shi jinin sarauta ne, kuma iyayensa ba mawaƙa ba ne, malamai ne. Allah ne ya yi masa baiwa ta shirya waƙa da kuma sha’war da yake yi da ita, wanda hakan ya sa ya tsunduma cikin wannan aiki, ta hanyar tasirantuwa da waƙoƙin Malam Mu’azu Haɗeja. Hakan ya sa ya zaɓi waƙa fiye da sana’o’in da yake yi, saboda ya fi ba ta muhimmanci a cikin zuciyarsa.

2.1 Tsokaci Kan Waƙar Mu Yaƙi Jahilci da Kuma Waƙar Yaƙi da Jahilci

Waqar ‘Mu Yaqi Jahilci’ ta Malam Mu’azu Haxeja tana bisa karin Hajaz. Wato karin da qafa ta 2 MAFAA’IILUN (v - - -) ke maimaita kanta domin ta bayar da shi (karin Hajaz). Misali

2. Zaman jama’a/cikin duniya

Ba ya kyau in/da jahilci.

 

3. Zalunci gami/da lalaci,

Duka mai had/da sa su jahilci.

(Mu’azu Haxeja: Waqar Mu Yaqi Jahilci)

 

Ita ce waqar da aka fara yi. Abin nufi waqar da ta fara samuwa kafin waqar ‘Yaqi da Jahilci’ ta Alhaji Xahiru Musa Jahun. Mawallafin ya yi amfani da gargaxi mai tsoratarwa wajen tabbatar da manufarsa ta rubuta waqar inda ya zayyana aibobin jahilci da jahili. Dubi misalin hakan a wurin da yake cewa:

47. Jahilci abin gudu ne kadda,

A rave shi ko cikin barci.

 

48. Jahilci ka vata al’amura,

Jama’a mu guje wa jahilci.

(Mu’azu Haxeja: Waqar Mu Yaqi Jahilci)

 

Haka kuma, waqar tana da zubin baituka ‘yan tagwai (qwar biyu). Sannan an qawata qafiyar (amsa-amo) baitocin tsakanin babba (na ciki) da qarami (na waje). Babban amsa-amon waqar na gavar kalma ne mai qarewa da ‘ci’ yayin da qaramin kuma ya kasance mai sauyawa. Ga misalin yadda Sha’irin ya tsara zubin waqar kamar haka:

59. Rashin ilimi da jahilci,

Kan ja wa maza wulaqanci.

 

75. Cikin duniya Ta’ala kadda,

Ka jefa mu gun wulaqanci.

(Mu’azu Haxeja: Waqar Mu Yaqi Jahilci)

 

Alhaji Xahiru Musa Jahun, a cikin tarihinsa an nuna ya tasirantu da irin salo na waqoqin Malam Mu’azu Haxeja. Wataqila hakan ba ya rasa nasaba da dalilinsa na rubuta waqar Yaqi da Jahilci bisa tsari da salo irin na mawallafin da ya gabata. Waqar Yaqi da Jahilci an xora ta kan karin Basix wanda ake karva-karva tsakarin qafa ta 6 MUSTAF’ILUN (- - v -) da ƙafa ta 5 FAA’ILUN (- v -) domin a samar da shi (karin Basiɗ). Misali

10. Me zan faɗa/tunda ban/da abin da za/ni faɗa,

Sai dai in ce/Rabbana/ka tsare mu ja/hilci.

 

 

11. Du mai jiki/in da rau/ni shi yakan/ji jiki,

Shi ɗai ka jin/yadda ran/sa yakan ji ya/ɓaci.

 

12. Mai magani/zai yi zan/ce za a yar/da da shi,

Mai jin jiki/in ya am/sa ta fi in/ganci.

(Alhaji Ɗahiru Musa Jahun: Waƙar Yaƙi da Jahilci)

 

Kamar Kumbo kamar kayanta! Ita ma waqar an yi amfani da gargaxi mai tsoratarwa game da jahilci da illolinsa kamar yadda baitukan waqar da suka gabata suka zama madubin gane hakan.

Ta fuskar zubi da tsari na baitocin waqar, Alhaji Xahiru Musa Jahun bai tashi daga mazaunin da Mu’azu ya bar masa ya hau ba. Waqar ita ma an yi ta bisa zubin qwar biyu, tare da babban amsa-amo na gavar kalma mai qarewa da ‘ci’ kwatankwacin na waqar da ta gabata. Akwai kuma qaramin amsa-amo wanda yake canzawa irin na Malam Mu’azu. Don rarrabe qwaya da kwanso, za a iya duba zuwa ga misalai kamar haka:

4. Dukan buƙatunmu gun Allah muke ta biɗa,

Wasu bayyanannu waɗansu suna cikin zuci.

 

5. Da akwai buƙatu mutum mai rai irin ta daban,

Wasu mun haɗe kansu domin sun yi cancanci.

(Alhaji Ɗahiru Musa Jahun: Waƙar Yaƙi da Jahilci)

 

3.0  Kwatanci Tsakanin Waƙar Mu Yaƙi Jahilci da Kuma Waƙar Yaƙi da Jahilci

Mawallafa waxannan waqoqi, suna da tunani na manufa da ra’ayi da mahanga iri xaya cikin zubi da tsarin waqoqinsu na game da jahilci. Tunanin kowanne daga cikin mawallafan, ya bayyana cikin waqoqin, musamman da aka aza su saman gadon nazari aka yi fixarsu. Malam Mu’azu Haxeja yana ganin cewa, duk wata asara ta duniya tana tattare da jahilci; haka abin yake ga Alhaji Xahiru Musa Jahun. Idan a buxe zancen a fili, za a ga cewa tunanin mawallafan ya tafi a kan abubuwa kamar haka:

3.1 Abubuwan da ke kawo Jahilci

Malam Mu’azu Haɗeja ya yi bayanin abin da ke kawo jahilci cikin al’umma a waƙarsa ta Yaƙi da Jahilci, domin gargaɗi ga mutane da su guje masa. Wannan abin da Malam Mu’azu ya kawo kuwa ba komai ba ne face lalaci. Ga abin da yake cewa game da hakan a baiti na 57 da 58 kamar haka:

57. Ya Allah ka ba maza sa’a,

Mu yi ƙwazo mu kore jahilci.

 

58. Lalaci ya haifi jahilci

Jahilci ya haifi kafirci.

(Mu’azu Haxeja: Waqar Mu Yaqi Jahilci)

 

Zaren tunanin da malam Mu’azu ya ƙulla a nan shi ne, duk wani mummunan abu babban tushensa lalaci ne. Lalaci shi ya ke samar da jahilci, uwa uba har ya kai mutum ga kafircewa. Alhaji Ɗahiru ya ɗauki wannan zaren tunani na Mu’azu inda ya kwance shi daidai yadda ya ƙulla da cewa:

19. Farkon macucinmu dai sunansa lalaci,

Barden mayaƙin da shi ke yaɗa jahilci.

 

20. In mun kashe shi akwai ‘ya’yansa sai mu kula,

Don shi ya haifi munafunci da ha’inci.

(Alhaji Ɗahiru Musa Jahun: Waƙar Yaƙi da Jahilci)

 

Alhaji Ɗahiru Musa Jahun ya aminta cewa, sadaukin mayaƙin nan na jahilci wato lalaci, shi ne babban azzalumin da yake wargaza al’umma. Matuƙar ana son a samu yadda aka yi fata, to, dole sai an ga bayan lalaci tare da ‘ya’yansa sannan haƙa ta cimma ruwa.

A taƙaice tunanin waɗannan marubuta game da abin da ke haddasa jahilci duk ya tafi ne a kan lalaci, wanda ya zama shugaba kuma jagora, ga duk munanan abubuwan da jahilci kan haifar.

3.2 Abubuwan da Jahilci kan haddasa

Malam Mu’azu Haɗeja ya kawo bayanin abubuwan da jahilci ke haddasawa waɗanda mutum mai hankali, mai ilimi da tunani ba za ya so ya samu kansa a yanayi da hali irin na aikata ɗaya daga cikinsu ba. Misali:

4. Yawan rikici da cin bashi,

Duka mai haddasa su jahilci.

 

5. Sata da fashi da yin caca,

Duka mai haddasa su jahilci.

 

7. Rashin haɗa kai, yawan hargitsi,

Duka mai haddasa su jahilci.

(Mu’azu Haxeja: Waqar Mu Yaqi Jahilci)

 

Waɗannan abubuwa da makamantansu da Malam Mu’azu ya kawo, sun nuna yadda girman aibin jahilci yake a cikin al’umma. Dubi dai yadda yake haddasa rikici da hargitsi da yin sata da fashi da yin caca. Kalli yadda Malam Mu’azu ya nuna jahilci a matsayin abin da ke jawo talauci da tsiya da mayar da mutum mai munanan halaye irin su girman kai da kwaɗayi da ƙarya da ha’inci da yi da mutane da shiga zarafin da ba na mutum ba. Tunanin Mu’azu Haɗeja ya yi canjaras da na Alhaji Ɗahiru Musa Jahun inda yake cewa:

48. Jama’a su shirya su zauna lafiya a gari,

Da wuya ta tabbata sai an yaƙi jahilci.

 

64. Ga ‘yan fashi da makamai sai mu lura da su,

Duk galibansu suna cike ne da jahilci.

 

65. Son dukiya ta haramun babu imani,

Da mubazzaranci da shashanci da kafirci.

 

68. Son kai da son ‘yan uwa baka san shari’a ba,

Don jahili ba shi jin kunyar ƙabilanci.

(Alhaji Ɗahiru Musa Jahun: Waƙar Yaƙi da Jahilci)

 

In da akuyar gaba ta sa baki, masu bin ta nan sukan tsoma na su. Fasihan sun tafi a kan tunani iri ɗaya, dangane da aibin jahilci da abubuwan da yake haddasawa. In til, in ƙwal, rinin mahaukaciya! Aibin jahilci bai tsaya nan ba, domin Malam Mu’azu yana ganin:

10. Yawan rantsuwa ga Allah kan,

Ƙarya ya laɓe ga jahilci.

 

11. Yawan fankama da girman kai,

Duka caffarsu na ga jahilci.

(Mu’azu Haxeja: Waqar Mu Yaqi Jahilci)

 

Karen da ya yi cizo, Hausawa suka ce wai da kashinsa ake yin magani. Alhaji Ɗahiru Musa Jahun bai yi ƙasa a gwiwa ba wajen alaƙanta jahilci ta mahangar Malaminsa Mu’azu Haɗeja, in da yake cewa:

28. Ga rantse-rantse ta ƙarya ga rashin ladabi,

Mata maza babu kunya kaito jahilci.

 

29. Sai hura hanci gadara fariya da riya,

Allah tsare mu tsageranci na jahilci.

 

45. Domin sukan yanka ƙarya ba su jin kunya,

Kuma har su rantse da Allah ka ji dabbanci.

(Alhaji Ɗahiru Musa Jahun: Waƙar Yaƙi da Jahilci)

 

Daga lokacin da surutu ya yawaita, wuf! Sai a ji ƙarya ta fito. Ko an so a gyara, sai abin ya koma da kamar wuya, wai gurguwa da auren nesa. Idan ma ba a yi wasa ba, to sai allura ta tono garma. Don kuwa ana iya faɗawa kan kadarkon da Malam Mu’azu ya ce:

12. Shiga zarafin mutane, yi

Da mutane yana ga jahilci.

 

13. Yawan tsegumi da kinibibi,

Da yawan kwarmato da ha’inci.

 

14. Da gulma, yawan kisisina,

Duka ussunu na ga jahilci.

(Mu’azu Haxeja: Waqar Mu Yaqi Jahilci)

 

Wato dai, bayan jahilci ya mayar da mutum maƙaryaci, sai kuma ya yi haramar mayar da shi mashahurin magulmaci daga nan sai ya zama maha’inci. Ashe ke nan dabarar da Alhaji Ɗahiru Musa Jahun ya yi wajen gwama tunaninsa da na Malam Mu’azu daidai ne, domin kuwa yana ganin:

61. Shi yin surutu da ƙarya ga yawan musu,

Ke sa akan gane wane yana da jahilci.

 

69. Bai san mutunci ba bai kuma san amana ba,

Komi ake inda shi sai ya yi ha’inci.

(Alhaji Ɗahiru Musa Jahun: Waƙar Yaƙi da Jahilci)

 

3.3 Ɗamarar Yaƙi da Jahilci

Dillalin wada, shi ya san kuɗin jariri, in ji ‘yan hikimar magana. Idan tafiya, ta yi tafiya za a ga komai nisan gari, akwai wani a gabansa. Abin nufi da hakan kuwa shi ne, kowace cuta ba za ta rasa maganin da ke warkar da ita ba. Marubutan sun kawo wasu batutuwa da suke ganin hanyoyi ne da za su ɓulle wajen yaƙar jahilci a cikin al’umma. Malam Mu’azu zancen da ya ɗauko ga shi kamar haka:

46. Ya ce jama’a su ɗau himmar,

Yaƙi don a kori jahilci.

 

47. Su ɗau takuba su ɗau mashi,

Da wuƙaƙe a yanka jahilci.

 

48. Jahilci abin gudu ne kadda,

A raɓe shi ko cikin barci.

(Mu’azu Haxeja: Waqar Mu Yaqi Jahilci)

 

Malam Mu’azu Haɗeja ba shi da laifi wajen yin wannan ƙulli na hikima. Matuƙar ba tashi tsaye aka yi ba, to ci gaban da ake nema ba za shi samu ba kamar dai yadda Alhaji Ɗahiru Musa Jahun ya ɗora da cewa:

47. Komi ake so a yi shi na yanzu ko na gaba,

Kafin a fara ya zam an yaƙi jahilci.

 

49. Ko arziki ko sarauta ko dukan sha’ani,

Ka ga an ji daɗinta sai in babu jahilci.

 

50. Ko ɗaukakan duniya ka ji wane ya ci gaba,

Da wuya a same ta sai an yaƙe jahilci.

(Alhaji Ɗahiru Musa Jahun: Waƙar Yaƙi da Jahilci)

 

4.0 Kammalawa

Daga abin da ya gabata na wannan maƙala, za a yi katari da ganin yadda aka gwama ra’ayi biyu na fasihan mawallafa waƙoƙin Hausa, waɗanda taurarauwarsu ta haska tun cikin ƙarnin da ya gabata. Akwai bambancin ra’ayi da ake samu tsakanin mutane daban-daban, amma a wannan bincike za a taras da cewa, muhimmancin zantukan da ke ƙunshe cikin tunanin marubutan abu ne da ya zama iri ɗaya, sannan, mai matuƙar amfani ne ga jama’ar yau, da waɗanda za su zo gobe, bayan waɗanda suka wuce jiya sun tatsa.

Duk da irin tunanin da Hausawa suke da shi na cewa, “Idan dambu ya yi yawa ba ya jin mai”. Sun yi amanna cewa, da koyo akan iya. Ko ba komai, a wannan zamani akwai jan aiki gagarumi wajen iya kamo igiyar da waɗannan fasihai suka jeho, domin hawa tsaunin da za a yaƙi jahilci. Dole a yarda da cewa, “Duk mai hankali da tunani, ba ya nuna gidansu da hannun hagu”. Abin nufi, ‘guntun gatarinka, ya fi sari ka ba ni’. Takaici da haushin yadda jahilci ya dabaibaye al’ummarmu a yanzu, da yadda ya gurɓata tarbiyyar yaranmu, da irin koma bayan da ya kai ƙasarmu ya sa na jinjinawa kiran da Alhaji Ɗahiru Musa Jahun ya yi na cewa:

95. Yara ku je makaranta don biɗar ilimi,

Kar ku yi kasala ku himmatu ban da lalaci.

 

96. Yara ku bar talla don neman kwabo da ɗari,

Ƙarshen kwabon ku yi ta ƙobobo da jahilci.

(Alhaji Ɗahiru Musa Jahun: Waƙar Yaƙi da Jahilci)

 

Matuƙar ba a nusar da yara hanyar samun nagartaccen ilimi ba, lallai rayuwa za ta koma ga faɗin Hausawa na cewa, an yi zuwan zomo kasuwa. Wataƙila abin ya zarce hakan har ya kai ga tunanin Malam Mu’azu Haɗeja da ya yi wa mutanen Zulu na ƙasar Uganda:

73. Sun zo duniya haka nan,

Ba jin daɗi saboda jahilci.

(Mu’azu Haxeja: Waqar Mu Yaqi Jahilci)

A nan, ba abin faɗi wanda ya wuce a ce, dubara ta rage ga mai shiga rijiya. Idan ginar ta yi ruwa, sai a mayar da ita rijiya don amfanar al’umma. In kuma ta zama ƙandas, to kawai abin da ya fi cancanta da ita shi ne, shadda (masai).

Manazarta

Abubakar, A. Y. (1992). “Alhaji Ɗahiru Musa Jahun Bauchi: Nazarin Waƙoƙinsa Na Siyasa”. Kundin Neman Takardar Shedar Malanta. Bauchi: Bauchi State Polytechnic.

Abdulmumini, I. (1991). “Alhaji Ɗahiru Musa Jahun Bauchi: Rayuwarsa Da Ayyukansa”. Kundin Digirin Farko. Kano: Jami’ar Bayero.

Adamawa, A. (2007). Sirrin Kamalah. Bauchi: Adamawa Media Link.

Adamu, A. U. (2000). “Tarbiyyar Bahaushe, Mutumin Kirki and Hausa Prose Fiction: Towards an Analytical Framework”. A Seminar Paper Presented in the Department of English and European Languages. Kano: Bayero University.

Amfani, A. H. (2011). “Hausa da Hausawa: Jiya da Yau da Gobe”. One Day Symposium. Zaria: Ahmadu Bello University.

Aminu, Y.A. (1992). “Alhaji Ɗahiru Musa Jahun Bauchi: Nazarin Waƙoƙinsa Na Siyasa”. Takardar Samun Shedar Diploma. Bauchi State Polytechnic.

Birniwa, H.A. (2004). Siffantawa A Cikin Waqoqin Siyasa. In: Xunxaye Journal of Hausa Studies vol. 1 No1. Sokoto: Department of Nigerian Languages Usmanu Danfodiyo University.

Bugaje, H.M. (ND). Hankali da Lura: Matsayinsu da Muhimmancinsu a Rayuwar Hausawa. Muƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani. Zariya: Sashen Harsuna da Al’adun Afirka, Jami’ar Ahmadu Bello.

Bunza, A.M. (2002). Yaƙi Da Rashin Tarbiya, Lalaci, Cin Hanci Da Karɓar Rashawa Cikin Waƙoƙin Alhaji Muhammadu Sambo Wali Basakkwace. Lagos: Ibrash Islamic Publications Centre Ltd.

Bunza, A. M. (2009). Narambaɗa. Lagos: Ibrash Islamic Publication Centre Ltd.

Bunza, U. A. (2013). Tarbiya a Cikin Adabin Hausa: Tsokaci Daga Karin Magana. In: KADA Journal Of Liberal Arts Vol. 7 No. 1. Kaduna: Faculty Of Arts, Kaduna State University.

CNHN, (2006). Ƙamusun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

Xangambo, A. (2007). Xaurayar Gadon Fexe Waqa. Kaduna: Amana Publishers Limited.

Dunfawa, A. A. (2002). “Waƙa A Tunanin Yara”. PhD Dissertation. Sokoto: Department of Nigerian Languages, Usmanu Ɗanfodiyo University.

Dunfawa, A. A. (2003). Ma’aunin Waƙa. Sokoto: Garkuwa Publishers.

Gusau, S. M. (2014). ‘Waƙar Baka Bahaushiya (The Hausa Oral Songs)’. Being a Professorial Inaugural Lecture No14. Sashen Koyar da Harsunan Nigeriya. Kano: Jami’ar Bayero.

Gusau, S. M. (2015). Mazhabobin Ra’i Da Tarke A Adabi Da Al’adu Na Hausa. Kano: Century Research And Publishing Limited.

Jahun, Ɗ. M. (1985). Waƙoƙin Hausa Littafi na Ɗaya. Bauchi: Ramadan press limited.

Ibrahim, S. S. A. (2013). ‘Hani Da Horo a Matsayin Tubalan Ginin Waƙar ‘Baje Kolin Hajar Tunani’. Cikin: Zauren Waƙa Vol. 1, No. 1 p179, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Idris Y. (2013). Falsafar Zaman Duniya A Cikin Waƙar Duniya Ta Yusuf Kantu. Zauren Waƙa Vol 1 No 1 p189, Sokoto: Jam’iar Usmanu Xanfodiyo.

Omar, S. (2013). Fasahar Mazan Jiya: Nazarin A Kan Rayuwa da Waƙoƙin Malam Mu’azu Haɗeja. Kaduna: Garkuwa Media Services, Ltd.

Sarvi S.A. (2007). Nazarin Waqen Hausa. Kano: Samrib Publishers.

Yahaya, I.Y. da Wasu (1992). Darussan Hausa Don Manyan Makarantun Sakandare. Littafi Na Ɗaya. Ibadan: University Press Plc.

Yahya, A.B. (2007). Jigon Nazarin Waqa. Kaduna: Fisbas Media Services.

Yahya, A.B. (2016). Salo Asirin Waqa. Sokoto: Guaranty Printers.

Yankara, M. M. and Sifawa, H. S. (2018). Jigon Tarbiyya a Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Ɗahiru Musa Jahun Bauchi. Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies. Vol 2 No 1. Department of Nigerian Languages. Sokoto: Usmanu Ɗanfodiyo University. P 161-176.

Yankara, M. M. (2019). “Tarken Tarbiyya a Wasu Waƙoƙin Alhaji Ɗahiru Musa Jahun Bauchi” M.A Dissertation. Sokoto: Department of Nigerian Languages, Usmanu Ɗanfodiyo University.



[1] Domin samun cikakken tarihinsa, a duba aikin Sa’adiya Omar (2013). Fasahar Mazan Jiya: Nazari a kan rayuwa da wakokin Malam Mu’azu Hadeja.

[2] Ana iya duba aikin Yankara, M. M. (2018). Tarken Tarbiyya a wasu wakokin Alhaji Dahiru Musa Jahun.

[3] Sa’adiya Omar (2013). Fasahar Mazan Jiya

Post a Comment

0 Comments