Daga taskar Farfesa Abdullahi Bayero Yahya.
Abdullahi Bayero Yahya
Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
Email: bagidadenlema2@gmail.com
Phone: 07031961302
Shimfiɗa
Amfani da waƙa wajen ilmantarwa daɗaɗɗiyar hanya ce a tarihi.
Mawuyacin abu ne mutum ya binciki tarihin kowace al’ummar Musulmi ya zan ya
tarar da cewa ba su yin amfani da waƙa wajen ilmantar da
‘ya’yansu ba. Misali duk wanda ya tashi a ƙasar Sakkwato ba zai
kasa tunawa ba da cewa a lokacin ƙuruciyarsa a yayin
karatun sanin da ya yi akwai littafin Ƙurɗaba. Littafin nan da ke farawa da Yaƙulu Yahyal ƙurɗabiyyud dari/ Almurtaji masubatil Gaffari. Wannan littafi kuwa
ba a ƙasar Sakkwato ko ƙasar Hausa kurum ake
sa shi a karatun sanin Musulunci ba. Hasali wanda ya wallafa shi mutumin ƙasar Andalus (Spain)
ne kuma ɗan garin Ƙurɗaba (Cordova a yau).
To kuma idan muka leƙa tarihi muna iya
cewa duk Musulmin ƙasar nan yana sane da irin rawar da waƙa ta taka a lokacin
jihadin da Shehu Usmanu ɗan Fodiyo ya jagoranta
cikin ƙarni na 18 da na 19. Wane Bahaushe ko Bafulatani ne zai
ce bai ji waƙar Ma’ama’are ba? A duk tsawon jihadin da Shehu ya yi da
shi da ɗalibansa da ‘ya’yansa da sauran
malamai sun kasance masu mayar da wa’azin da suka yi wa al’umma zuwa waƙoƙin da ɗalibansu kan hardace su kuma baza su cikin ƙasar Hausa da kewaye.
Wannan hanya ta ci gaba ko bayan kafa daular Musulunci a ƙasar Hausa. Hasali, mutum
na iya cewa waɗannan waƙoƙi sun taimaka ainun
wajen tabbatar da samar da ilmi ga mutanen wannan ƙasa, abin da ya
tilasta ma Turawa ‘yan mulkin mallaka suka riƙa sara suna duban
bakin gatari a zamanin da suka mulke mu, saɓanin yadda suka yi wa
wasu al’ummomin da ba su da irin wannan tarihi.
Rubuta waƙoƙi a matsayin tattara
gundarin ilmin da ke cikin wani littafi shi ake kira nazmi. Wannan kuwa malamai
kan yi shi ne domin sauƙaƙar da neman ilmi musamman ga waɗanda ba su iya karatu da rubutu ba, saboda kuwa idan aka
rera waƙoƙin za su ji abin da ake faɗa.
Malamai kan zaɓi waƙa ne domin ta fi zube
iya jan hankali da kuma saurin isar da saƙo. Ko ba kome zumunta
tsakaninta da zuciya ta fi ta tsakanin zube ko wasan kwaikwayo da zuciyar.
A kan wannan hanya ce
Waƙar
Nijeriya ta samu. Wannan waƙa nazmi ne na darussan da Alhaji Shehu
Shagari ya koyar da ɗalibansa fiye da
shekaru sittin da suka wuce. Sharhi a kan wannan waƙa shi ne maƙasudin wannan maƙala.
2.0 Tsarabar Bayan Darussa
Bayanin da zai zo nan
ƙasa
nazari ne ko sharhin Waƙar Nijeriya wadda Alhaji Shehu Shagari ya rubuta. A
wannan maƙala an kira wannan waƙa da sunan Tsarabar
Bayan Darasi domin tunatarwa ga asalin samuwarta. Ɗalibai da yawa a yau
suna kallon waƙar a matsayin waƙar da aka zauna cikin
dare guda aka rubuta, sannan aka miƙa ta ga wata maɗaba’a ta buga. Suna kallon ta a matsayin waƙar da tushenta a ƙwaƙwalwa yake kurum, bai
da wata alaƙa da wani matashin malamin makaranta mai kuzarin aiki da
zimmar ganin ɗalibansa sun fahimci
darussansa ba. Da yawa daga cikin ɗaliban wannan ƙarni na ishirin da ɗaya, kai watakila har ɗaliban Kwalejin Shehu
Shagari a yau da ke sauraren wannan maƙala, ba sukan kalli
wannan waƙa a matsayin jingar da wani haziƙin malami, ɗan shekara ishirin da ‘yan kai, ya yi ba ɗalibansa bayan ya kammala gabatar da darussansa. To amma
a haka aka rubuta Waƙar Nijeriya. Kima-kima marubucinta ya riƙa rera wa ɗalibansa ita. Wato yakan rera musu baitocin da suka jiɓinci darasi ko darussan da ya koyar da su, ko dai bayan
kowane darasi ko kuwa bayan kowane rukunin darussa. Ya rera musu baitocin
daidai abin da ƙwaƙwalwarsu ke iya ɗauka.
2.1Tarihin Marubucin Waƙar Nijeriya
Marubucin Waƙar Nijeriya dai
sanannen mutum ne ga duk ɗan Nijeriya. Shi ne
Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari, zaɓaɓɓen Shugaban ƙasa mai ɗinbin iko na farko a wannan ƙasa tamu. Ya kuwa yi
wannan shugabanci ne tsakanin watan Oktoba na 1979 zuwa watan Disamba na 1983.
Jam’iyyar N.P.N. (National Party of Nigeria) ce ta tsayar da shi har sau biyu a
wannan muƙami kuma ya lashe zaɓen har sau biyu. Soja
ne suka kawar da gwamnatinsa a watan Disamba na 1983 kuma yin haka ne ya hana
gwamnatin kai ƙarshen zubi na biyu a shekarar 1987.
An haifi Shehu
Shagari, (da wannan suna aka fi sanin sa) ranar Larba 25 ga watan Fabrairu na
1925 a garin Shagari cikin lardin Sakkwato. Ya yi makarantar allo kamar yadda
kowane yaro da yarinya kan yi a wannan yanki na ƙasar Hausa, wato da
ita ya buɗe ido wajen neman ilmi kafin
makarantar boko. Ya yi karatun boko a Yabo da Sakkwato da Katsina.
Shehu Shagari ya fara
aiki a matsayin malami a Makarantar Midil (Middle School, Sokoto). Ya karantar
da fannonin kimiyya da tarihi da labarin ƙasa. Haka nan kuma ya
karantar a garin Argungu. Alhaji Shehu Shagari ya shiga siyasa tun a gomiyar
1950. Ya riƙa muƙamai da dama ciki har da na minister
da kwamishina da kuma Shugaba mai ɗinbin iko na farko na
Nijeriya. Shi ne ya jagoranci gina kasuwar Sakkwato ta yanzu. Alhaji Shehu
Shagari shi ne Turakin Sakkwato a Majalisar Sarkin Musulmi. Yana da mafi
darajar lambar girmamawa ta Nijeriya, wato G.C.F.R.
Alhaji Shehu Shagari
jigo ne a fagen rubuta waƙoƙin Hausa. Shi ne Uban Ƙungiyar Marubuta Da
Manazarta Waƙoƙin Hausa ta Nijeriya. Waƙoƙinsa suna da yawa, sai
dai kamar yadda ɗinbin rubutattun waƙoƙin Hausa suka sha ɓacewa saboda dalilai masu yawa (ciki kuwa har da kawaicin
marubutansu na ƙin fitowa da su a sarari). Waƙoƙin wannan bawan Allah
har yanzu ba a san yawansu ba kuma wasu ma ba a san su ba. Ya taɓa faɗa wa marubucin wannan
maƙala
cewa babban sanadin salwantar mafi yawan waƙoƙinsa shi ne kiran da
aka yi masa a Kaduna lokacin da yake zaune a Sakkwato. Daga ofishin Sardaunan
Sakkwato ne aka kira shi. A zaton Shehu Shagari kiran ba zai wuce kwana biyu ko
uku ba. Saboda haka sai ya kama hanya ba tare da kimtsa littattafansa da ke
cikin barayarsa ba. To amma da isarsa Kaduna ya yi gaisuwa inda Sardauna sai shi
Sardaunan ya ce masa, ka iso? Sai ka yi niyya zuwa tashar jirgi ana jiran ka ku
wuce zuwa Ikko. Matafiyinmu ya garzaya zuwa tashar jirgin ƙasa, ya shiga suka
runtuma sai Ikko. Suna isa aka nunnuna musu masauki. Daga bisani aka tafi da su
gidan gwamnati aka rantsar da su a matsayin ministocin ƙasa. Shi ke nan zama
ya kama Alhaji Shehu Shagari a Ikko, matafiyin da ya baro gida da sunan yin
kwana biyu ko uku. In gajarce muku labari, Shehu Shagari bai dawo Sakkwato ba
sai bayan wata shidda! Kuma ko da ya dawo ya tarar da yara sun yi abin da suka
saba da takardu, ciki kuwa har da Waƙar Nijeriya da sauran
waƙoƙinsa waɗanda ke rubuce cikin kundin da ya yi musu. Waƙoƙin sun salwanta ke
nan sai waɗanda aka iya samowa daga ɗaiɗaikun mutane musamman
ɗalibansa da abokansa.
Wannan shi ne taƙaitaccen tarihin
marubucin Waƙar Nijeriya, amma fa taƙaitawar taƙaitaccen bayani ke
nan.
2.2
Tarihin Waƙar
Nijeriya
Alhaji Shehu Shagari
ya rubuta Waƙar Nijeriya a shekarar 1948 lokacin da yake karantarwa a
Makarantar Midil ta Sakkwato. Wato ke nan yana ɗan
shekara 23 ya rubuta ta.Ya faɗa cewa rubuta wannan
waƙa
koyi ne ya yi da malaminsa Malam Adamu Koko.[1]
An rubuta wannan waƙa da kaɗan-kaɗan har ta yi tsawo, ba
don gazawa ba, a’a sai dai saboda yanayin da ya haifar da ita. Marubucinta ya
faɗa min cewa dalilai biyu suka haifar waƙar Nijeriya. Dalili
na farko shi ne zamansa malamin Tarihi da Labarin Ƙasa. Da shi yana
karantar da Ilmin Kimiyya ne. Haka kwatsam Turawan Mulkin Mallaka suka fito da
umurnin daina koyar da Ilmin Kimiyya a makarantu wai don baturen da ke karantar
da shi ya mutu, kuma musamman wai ba a iya karantar da ɗalibai wannan ilmi cikin harshen Hausa saboda ba a iya
fassara kalmomin fannu na kimiyya zuwa Hausa! Saboda wannan dalili ne malaman
da ke akwai a lokacin, irin su Shehu Shagari aka ce a mayar da su malaman wasu
fannoni daban. To shi kuwa Shehu Shagari ya karanta Ilmin Kimiyya ne domin a
lokacin ana neman a horar da malaman kimiyya. Da aka soke sai ya koma yana
karantar da Tarihi da Labarin Ƙasa waɗanda
yake da sha’awa da su tun azal. Ke nan zamowarsa mai koyar da waɗannan fannoni ta haifar da rubuta Waƙar Nijeriya. Sannan
dalili na biyu kan rubuta waƙar da kaɗan
da kaɗan shi ne marubucinta ya sheda min cewa ya
lura da cewa ɗalibansa sun kasance
masu sha’awar waƙa ne, rubutacciya da ta baka. Shi kuma ga shi ko bayan
zamansa malami shi marubucin waƙoƙi ne. Saboda haka sai
ya yi tunanin amfani da waƙa wajen karantar da ɗalibansa. A kan haka ne bayan kowane darasi ko rukunin
darussa sai ya rubuta baitoci masu bayyana darasi ko darussan a taƙaice a kan allo ya
rera wa ɗaliban, su kuma su rera. Waɗannan baitoci da yakan zo da su ya juya kan allo su ne ɗaliban kan rera idan suka koma ɗakunan kwana na makaranta. Ta haka ne ɗalibai da dama har da waɗanda
ba na ajinsa ba suka hardace baitocin suna kuma rerawa. Haka kuma akan turo
malamai daga garuwa zuwa Sakkwato domin halartar gajeren kwas na ƙarin sani dangane da
hanyar karantarwa. Alhaji Shehu Shagari yana daga cikin malaman da akan zaɓa su koyar da waɗannan malamai a waɗannan kwasa-kwasai. A nan ma yakan basu waɗannan baitoci bayan ya yi musu darasi. Su kuma idan suka
koma ƙauyukan da suke karantarwa sai su yi kamar yadda Shagari
yake yi a Sakkwato. Ta haka ne baitocin suka bazu a duk faɗin lardin Sakkwato.
Ta haka ne waɗannan baitoci sannu a hankali suka taru har suka zama waƙa mai tsawo, suka
zama Waƙar Nijeriya. To amma fa ba a matsayin littafi kamar yadda
muka san ta a yau ba. Wannan ya ɗauki lokaci mai
tsawo.
A 1951 lokacin da
Alhaji Shehu Shagari yake karantarwa a Argungu wani baturen makaranta ya neme
shi da ya ba da wannan waƙa domin a buga ta a matsayin littafi. Marubucin ya amince
da wannan bukatar. Shi kuma baturen ya kai wa Kamfanin Gaskiya don su buga. To
amma sai Kamfanin Gaskiya ya sharɗanta cewa sai
marubucin ya mayar da Hausar cikin waƙar zuwa abin da suka
kira Daidaitacciyar Hausa. Da bature ya mayar wa Shagari da wannan martini sai
ya tambaye shi mece ce Daidaitacciyar Hausa. Bature ya faɗa masa Hausar Kano ake nufi. Shi kuwa Shagari ya mayar
masa da cewa ai babu marubucin da ke iya rubuta waƙar Hausa ba tare da
ya surka da Sakkwatanci ba. Saboda haka Sakkwatanci ne Hausar waƙa kuma shi ba ya jin
yana iya biya wa Kamfanin Gaskiya da bukatar, wato ba zai yar da kwari ya ɗauki lefe ba.
A gomiyar 1970 ne
wata baturiya mai suna Mrs Jean Boyd ta gabatar wa Shehu Shagari da shawara
cewa ya kamata a buga Waƙar Nijeriya zuwa littafi wanda ‘yan makaranta za su riƙa amfani da shi, ta
kuma dage da lalle sai an buga waƙar.[2]
Alhaji Shehu Shagari ya sheda mata cewa shi fa a lokacin bai da wannan waƙa a hannunsa sai fa
watakila idan aka ci sa’a aka same ta a hannun abokai ko ɗalibai. Boyd kuwa ta ce ba matsala. Ka san bature da ɗaukar ma rai. Nan take ta sa cigiya a jaridu cewa ana kamɓen wannan waƙa kuma duk wanda ya
biya bukatar za a ba shi goro. Ba da jimawa ba bukata ta biya. Ciroman Sakkwato
Alhaji Muhammadu Bello Mai Wurno ne ya kawo Waƙar Nijeriya daga
cikin adane-adanensa![3]
Jean Boyd ta tuntuɓi marubucin waƙar da ya sabunta ta
domin ta dace da zamani. Misali a lokacin da ya rubuta waƙar ana cikin mulkin
mallaka, Nijeriya ba ta sami ‘yancin kai ba. Saboda haka baitoci kamar na 66
zuwa na 85 sababbi ne domin maganar jihohi da suka ƙunsa. A ƙarshe dai an buga Waƙar Nijeriya a 1973.
Tun daga 1973 har zuwa yau an sake buga wannan waƙa har sau huɗu, 1978 da 2006 da 2007 da kuma 2009.
Ka ambaci Shehu
Shagari cikin taron ɗalibai ko malamai ko
marubuta waƙoƙin Hausa ko manazartansu, haƙiƙa ko tababa babu Waƙar Nijeriya ce za ta
faɗo musu a rai. Kai ko a sha’anin siyasa hakan
takan auku. A zamanin da yake Shugaban Ƙasa ya kai ziyarar
aiki a Amerika a zamanin da Jimmy Carter yake shugaban ƙasar Amerika. A yayin
da suke cin abincin rana a fadar ƙasar Amerika sai ga
wata baturiya ‘yar ƙasar ta fito tana rera Waƙar Nijeriya da Hausa.
To bayan da suka ƙare cin abinci, an tashi ana gaisawa, sai Bahaushenka na
Allah ya nufi wadda ba Bahaushiya ba amma ta ji Hausa raƙwai har ma da rera waƙar Hausa! Abin jin daɗi ne ga kowane Bahaushe mai kishin harshensa. To amma me
ya auku a wannan ganawar da Bahausar Baturiya? Kallon sa kurum ta riƙa yi. Ita kome ba ta
fahimta ba don ko ‘ha’ na Bahaushe ba ta sani ba! Ashe, ashe ilmin harshe da
rera waƙa kurum ta ƙware a kai![4]
Nasara hasarar ƙasa. An tsara haka ne domin Shugaban Ƙasar Nijeriya ya saki
jikinsa ya ji a gida yake, ya kuma ɗebe baƙunci! Ko mene ne suke
nufi? Oho o o, ya dai gane!
Janar Mamman Vatsa ya
fassara Waƙar Nijeriya zuwa harshen Ingilishi kuma an buga ta a
haka. Allah ne kurum ya san ko malamin makaranta nawa ne suka yi amfani da Waƙar Nijeriya a wurin
karantarwarsu. Marubucin wannan maƙala na iya tuna cewa
ya yi amfani da ita a karantarwar da ya yi a makarantar Sakandare ta garin
Anka. A lokacin ne ya yi ƙoƙarin zaƙulo baiwar rubuta waƙa da ke kwance cikin ɗalibansa yayin da yake rera Waƙar Nijeriya tare da
su. A duk lokacin da suka rera wasu baitoci tare da maimaitawa da kuma rawa sai
ya ce wa ɗaliban a sake rera baitoci sannan a yi
ƙoƙarin ƙirƙiro baiti cikin karin
Waƙar
Nijeriya.[5]
A yau kuma bayan
shekara sittin da ɗaya (61) da Shehu
Shagari ya rubuta Waƙar Nijeriya ga mu mun taru a Kwalejin Ilmi ta Shehu
Shagari muna nazarin Waƙar Nijeriya ta Shehu Shagari, Wannan kwalej a yau
shekarunta talatin da tara (39) da kafawa. Wato dai da Kwalejin Ilmi ta Shehu
Shagari da ilahirin ɗaliban da ke cikin
Kwalejin Ilmi ta Shehu Shagari da kuma wasu malaman Kwalejin, duk Waƙar Nijeriya ta Shehu
Shagari ta girme su!
2.0
Taƙaitaccen
Sharhi Kan Waƙar Nijeriya
3.1Zubi Da Tsari
Waƙar Nijeriya waƙa ce ‘yar tagwai ko
‘yar ƙwar biyu. Wato kowane baitinta yana da sheɗara (ɗango) biyu. A yadda
ta fito cikin littafi waƙar tana da baiti ɗari biyar (500). Tana
da amsa-amon (ƙafiya) ciki da na waje, wato ƙarami da babban
amsa-amo. Babban shi ne /ya/ a yayin da ƙaramin mai iya
sauyawa ne daga wannan baiti zuwa wancan kamar yadda ya gada. Ga misalin da ke
nuna abubuwan da aka faɗa:
1.
‘Yan
yara ku zo a faɗa muku
Ku ji labarin Nijeriya
2.
In
an tambai ku ku ce musu
‘Mu tamu ƙasa Nijeriya’
3.
Don
kam da yawa aka tambaya
Shin wai mi an Nijeriya
4.
To
wagga ƙasa ce ba wata
Ita anka sani Nijeriya
5.
Turawa
su ka raɗa mata
Wanga suna wai Nijeriya
6.
Sun
kira wani kogi Niger
Mu Kwara muke cewa, jiya
7.
Daga
sunan kogin nan ɗaya
Suka sa na ƙasa suka rataya
A baiti na 3 da na 7
ne kurum ƙarami da babban amsa-amo suka kasance iri ɗaya, wato duka ya ne.
Idan aka yi nazari za
a iya lura da cewa baitocin sun kasu zuwa rukuni-rukuni dangane da ƙananan jigoginta.
Abin nufi a nan shi ne za a sami jerin baitoci a kan wani saƙo sannan wani jerin
ya biyo baya yana magana a kan wani saƙo. Misali, baiti na 1
zuwa na 7 sun ƙunshi saƙo kan yadda aka yi aka ƙirƙiri kalmar Nijeriya
aka ce sunan ƙasa ne; baiti na 8 zuwa na 9 bayani ne kan dangantakar
kogin Niger da Nijeriya; baiti na 10 zuwa na 11akwai bayanmi kan tekun da kogin
ya faɗa cikinsa da kuma maƙwabtan Nijeriya a
arewa inda Hamada take; tarihin waɗannan maƙwabtan ƙasashe na arewacin
Nijeriya shi ne saƙon da baiti na 12 zuwa na 19 suka ƙunsa, cewa can da a ƙarƙashin mulkin Faransa
suke. Sai kuma baiti na 20 zuwa na 65 waɗanda ke ɗauke da bayanin yadda Nijeriya ta kasance yanki-yanki, lardi-lardi
a ƙarƙashin mulkin mallakar
Turawan Ingila. A rukuni-rukuni kamar waɗannan za a tarar da
baitocin nan ɗari biyar na Waƙar Nijeriya. Wannan
shi ya tabbatar da cewa Shehu Shagari ya rubuta wannan waƙa zubi-zubi dangane
da darussan da ya karantar wa ɗalibansa.
Ɗangogin wannan waƙa gajejjeru ne kuma
mafi yawansu kammalallun jimloli ne. Suna da sauƙin fahimta ga yara.
Kalmomin cikinta daidai fahimtar yara suke. Manyan kalmominta suna da sauƙin bayyanawa ga babba,
wato malamin yaran. Misali, kalmar ‘hatsaniya’ a baiti na 86 ana iya fassara ta
da ‘yawan faɗan baki’, Kalmar
‘amalta’ kuwa a baiti na 497 ana iya fassara ta da ‘abu ya girma ƙwarai kamar raƙumi, don raƙumin da ya girma haka
shi ake kira amali’.
Marubucin yakan yi
hattara ga kawo Kalmomi masu tsauri sosai, inda yakan yi saurin fassara su da
misali. Alal misali, ɗalibi zai so sanin
ma’ana ‘tozartacciya’ a baiti na 254 inda Marubucin ke cewa:
254.
Dag
arewa a kai bayi kudu
A yi musanya tozartacciya.
Nan take a baiti na
gaba sai ya kawo misalin manufar kalmar:
255.
Don
mutum ake bai a sayo giya
Ko bindiga lalatacciya
3.2
Salo
Salon cikin wannan waƙa mai sauƙi ne. Haka kuwa ya
dace da yanayin fahimta da rayuwar yara. Da salon ya kasance mai tsauri ne to
da kuwa sha’awarsu ga waƙar ta taƙaita. Da kuma ba su ƙallafa wa kansu
hardace ba balle su yaƙa ta ga junansu. Mai karatu zai fahimce abin nufi a nan
idan ya kalli waɗannan baitoci:
1. ‘Yan yara ku zo a
faɗa muku
Ku ji labarin Nijeriya
…
243.
Ɗan yaro in ka so sanin
Kurmi da tsiri Nijeriya
244.
Taso
a Arewa ka yo kudu
Ka ga yadda suke sassakiya
Kai da jin waɗannan baitoci ka san da cewa an yi la’akari da tunanin
yara. Baiti na ɗaya ya fara da kwaɗaitarwar ba da labari, kamar dai malamin ya hangi cewa
hankulan ɗalibansa suna wani wuri. Shi kuwa yaro
da ka ce masa zo ka ji in faɗa maka wani abu ka
san da cewa zai tara hankalinsa duk a gare ka. Haka nan kuma an kwaɗaitar da yara ga yin tafiye-tafiye don neman sani a baiti
na 243 da na 244. Haƙiƙa waɗannan baitoci guda
biyu sun fito fili a zuciyar marubucin wannan maƙala lokacin tafiyarsa
ta farko daga Sakkwato zuwa Ikko cikin mota. Tsirrai da yanayin gidaje
sassakiya suke yayin da mutum ya tashi daga arewacin Nijeriya ya yi kudu.
Marubucin Waƙar Nijeriya ya tsara
ta ta yin la’akari da al’adu da addinin ɗalibansa. A kai a kai
yana tunatar da su hikima da baiwar Mahaliccin Sarki Allah. Dubi yadda ya
gabatar da wani ɓangare na Labarin Ƙasa:
124.
‘Yan
Adam mu ji tsoron Rabbana
Shi ya yi ƙasa da samaniya
125.
Ya
yi taurari da farin wata
Yai abin da ka haskaka duniya
126.
Ita
rana amfaninta biyu
Haskenta yakan game duniya
127.
Sannan
ga zafi nata ne
Kullum take zafafa duniya
…
Wannan gabatarwa tana
koya wa yara sanin iko da jinƙayin Mahaliccinsu zuwa ga mu bayinsa.
Daga nan kuma sai marubucin ya shiga bayanin ilmin kimiyyar da ke cikin wannan
jinƙayi
da Allah ya yi wa bayinsa, wato yadda ɗalibansa ke iya gane
cewa wani yanayi ya shigo (baiti na 131-2, da na 136-7) da kuma yadda rowan
sama kan samu (baiti na 140-4) da dai sauransu. Haka kuma akwai irin wannan
salon gabatarwa ta yin la’akari da addini a baiti na 161 a yayin da marubucin
yake son yin bayani kan albarkatun ƙasa, dabbobi da itace
da amfaninsu ga ‘yan Adam.
Jaweabin Kammalawa
Ba nufina ba ne in feɗe biri har wutsiya dangane da hikimomin da ke cikin Waƙar Nijeriya. Babu
fili kuma babu lokaci sannan uwa uba ilmi ya ƙaranta. Abin da na yi
bai wuce nuni ga ɗaliban nazarin waƙa, musamman na
Kwalejin Ilmi ta Shehu Shagari, domin su sami ƙaimin nazarin wannan
waƙa
sosai da sosai. Ina da ra’ayin cewa ɗalibi na iya saka ta
a matsayin abin Nazarin ƙwaƙƙwafi don samun digirin dokta, wato Ph.D. “Ƙwarewa a Aikin
Karantarwa: Nazarin Dubarun Koyarwa Cikin Waƙar Nijeriya ta Shehu
Shagari” take ne da ɗalibi mai neman Ph.D.
kan iya jinjinawa.
MANAZRTA
Dunfawa, A.A. (2002),
“Waƙa
A Tunanin Yara”, kundin neman
digiri na uku, Sokoto: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Ɗangambo, A (2007), Ɗaurayar
Gadon Feɗe Waƙa, Zariya: Amana
Publishers
Shagari, S. (2007), Waƙar Nijeriya, Zariya: Northern Nigerian
Publishing Company (NNPC).
Shagari, S. (2009), Waƙar Nijeriya da Waƙar Hanƙuri, Kaduna: Sonia
Computer
Yahya, A.B. (1997), Jigon Nazarin Waƙa, Kaduna: Fisbas
Media Services
Yahya, A.B. (2001), “Dangantakar Waƙa Da Tarbiyyar ‘Ya’yan Hausawa” cikin HARSUNAN
NIJERIYA XIX, Centre for The Study of Nigerian Languages, Kano: Bayero
University, sh. 94-109
Yahya, A.B. (2001), SALO ASIRIN WAƘA, Kaduna: FISBAS,
[1] Duba littafin Waƙar Nijeriya da Waƙar Hanƙuri na
Alhaji Shehu Shagari (2009), shafi na 5.
[2] Duba kamar sama.
[3] Bayani daga marubucin waƙar
a cikin hirar da mai wannan maƙala ya yi da shi ranar Lahadi 07/06/2009. Ciroma
kuma ɗaya daga ɗaliban marubucin waƙar ne.
[4] Hira da Marubucin waƙar
ranar Lahadi 07/06/2009.
[5] Watakila yanzu wani ko wasu
daga waɗannan ɗalibaina sun nare da rubuta waƙoƙin Hausa. Allah ne Masani
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.