Ticker

6/recent/ticker-posts

Bayanin Kabli Da Ba'adi [02]

• Wanda ya ɓoye a gurin bayyanawa ya yi sujjadar ƙabali, wanda kuma ya bayyana a gurin da ake ɓoyewa ya yi sujjadar ba’adi.

SHARHI:

Idan mutum ya ɓoye karatu agurin da ake bayyana karatu acikin sallah, kamar mutum ya ya ɓoye karatu a raka'a biyun farko na sallar magriba ko raka'o'i biyun farko na isha'i ko asubah, to zai yi sujjadah ƙabli,

Wato bayan ya yi tahiya tareda yiwa Annabi {s.a.w} salati, to kafin ya yi sallama, sai kuma ya ƙulla niyyar sujjada guda biyu na ƙabli, sai ya yi su, sannan ya yi sallama, basai ya sake wata tahiya a bayansu ba.

Wanda kuma ya bayyana karatu a inda ake ɓoyewa, kamar misali wanda ya bayyana karatu cikin sallah a gurin da ba'a bayyana karatu a fili, to sujjada ba'adi ta kamashi,

Wato bayan ya yi tahiyar ƙarshe yayiwa Annabi {s.a.w} da sauran addu'o'i na bayan salati, to sai ya yi sallama, sai kuma ya ƙulla niyya ta yin sujjada ba'adi sai yayisu nan take, yana gamawa sai ya yi sallama basai ya sake yin wata tahiya a bayansu ba.

• Wanda ya yi magana yana mai mantuwa a cikin sallah ya yi sujjada ba’adi, Wanda ya yi sallama daga raka’o’i biyu yana mai mantuwa ya yi sujjadar ba’adi.

SHARHI:

Wanda ya yi magana da mantuwa acikin sallah, to sujjada ba'adi ta kamashi, wato sujjada biyu bayan sallama.

Wanda kuma ya yi sallama daga raka'a biyu, misali a sallah mai raka'a uku ko huɗu, sai ya manta ya yi sallama bayan ya sallaci raka'a biyu, to shima bayan ya tashi ya cika ragowar raka'o'in, to daga ƙarshe sai ya yi sujjada ba'adi.

• Wanda ya ƙara rakaa ɗaya ko raka’a biyu a cikin sallah ya yi sujjada ba’adi, Wanda ya yi ƙari a cikin sallah misalinta ta ɓaci.

SHARHI:

Wanda ya manta ya ƙara raka'a ɗaya ko raka'a biyu a cikin sallah, to sai ya yi sujjada ba'adi, bayan ya yi sallama.

 Wanda kuwa ya yi ƙari acikin sallah misalinta, kamar sallah mai raka'a huɗu ce, sai kuma ya yi takwas huɗu sau biyu kenan, to sallarsa ta ɓaci, dole sai ya sake sallah, kuma babu wata sujjada ta ƙabli ko ba'adi akansa.

 

• Wanda ya yi kokonton cikar sallarsa yazo da abinda ya yi kokonton a cikinsa, kokonto a cikin tauyewa kamar haƙiƙancewar sane.

SHARHI:

Wanda ya yi kokonto acikin sallah, kamar mutum yana sallar azahar, sai yake tunanin raka'a uku ya yi ko huɗu, to sai ya tashi ya ciko ɗayar kawai.

Domin kokonto acikin ragi a sallah, kamar mai sallah bai cika wannan raka'ar da yake kokonta akanta bane, samun nutsuwarsa shi ne ya cikata, saboda ya kuɓuta daga kokonton.

• Wanda ya yi kokonto a cikin tauye raka’a ɗaya ko sujjada yazo da ita ya yi sujjadar ba’adi.

SHARHI:

 Wanda yake tunanin cewa ya rage raka'a ɗaya ko biyu, to ya cikata nan take, sannan kuma sai ya yi sujjada ba'adi, wato bayan ya yi sallama sai ya yi sujjudu guda biyu.

• Idan ya yi kokonto a cikin sallama, to ya yi sallama idan ya kasance a kusa babu sujjada a gare shi, idan kuma ya tsawaita sallarsa ta ɓaci.

SHARHI:

 Idan mai sallah yana tunanin ya yi sallama ko baiyi ba, to yayita nan take idan bai tashi daga gurinba, idan kuwa baya gurin ya yi nisa, to sallarsa ta ɓaci, sai ya sake sallah.

• Mai yawan wasi-wasi yabar wasi-wasin zuciyarsa kada yazo da abinda ya yi kokonton a cikinsa, sai dai yana yin sujjada ba’adi idan ya yi kokonto a cikin ƙari ko tauyewa.

SHARHI:

 Wanda yake fama da yawan tunani acikin sallarsa, misali, mutum yana yawan tunanin cewa ya cika sallarsa ko kuma ya rage ko kuma ya ƙara, to kada yazo da abinda yake tunanin ya rage ɗin, sai dai kawai bayan ya yi sallama, zai yi sujjada ba'adi.

• Wanda ya bayyana karatun Alƙunut babu sujjada a gareshi, sai dai cewa an karhanta yinsa da gangan.

SHARHI:

 Idan mutum ya bayyana karatun Alƙunut acikin sallah, to babu komai akansa, amma dai anso a ɓoye karatunta,

 Sai dai zance mafi ƙarfi ana bayyana karatunta, domin a lokacin da Manzon ALLAH {s.a.w} yake karatun ta, sahabbai suna amsawa suna cewa Amiin.

ALLAH shi ne mafi sani.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

Duk mai neman ƙarin bayani ya yi mana magana ta private.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments