Abstract
This chapter dwelt on some of the security measures used by government to ensure and maintain security with a particular reference to Nigeria. It revealed that the Federal Government is the sole repository of security in Nigeria. The Constitution of the Federal Republic of Nigeria 1999, as amended, has placed the burden and duty of security, the maintenance of law and order and protection of lives and property within the federation squarely upon the shoulders of the federal government. This means that the Federal Government solely owns and controls the security without sharing it with any of the 36 states and the FCT. Paragraphs 17 and 45 of Part 1, Second Schedule, of the Excusive Legislative List of the 1999 Constitution (as amended) has exclusively given the Federal Government control of the security agencies. Hence, the State Governments do not have direct control and significant roles to play in the maintenance of security, except complimenting the Federal Government via provision of logistics for the security agencies in their respective domains. Furthermore, the chapter explored the place of security in the Constitution of the Federal Republic of Nigeria as well as identified security agencies having the stake of ensuring security in Nigeria. It also enumerated and discussed some of the security measures being taken to provide, ensure security of lives and property in Nigeria as well as how Zamfara State Government has been making efforts and complementing Federal Government to contain the security threat the state grapples with. However, some of the security measures identified in the chapter are just overt ones with several covert ones not said here. This is because, no nation, world over, does reveal all of its security measures to avoid countering them by criminals, domestic collaborators and hostile nations.
Sabi’u Alhaji Garba (PhD)
Inkiya da gida mai lamba 47, Titin Tafida,
Bukkuyum, Ƙaramar Hukumar Bukkuyum, Jihar Zamfara
1.0 Gabatarwa
Wannan babi ya mayar da hankali ne a kan matakan da
gwamnati ke bi ko ɗauka wajen
tabbatar da tsaro. An ɗauki gwamnatin
Tarayyar Nijeriya a matsayin misali inda aka yi bayani dalla-dalla a kan
hanyoyin da ake bi wajen tabbatar da tsaron ƙasa a Nijeriya. Sha’anin
tsaro a Nijeriya ya ta’allaƙa kacokam a kan gwamnati. A matakan gwamnatin ma, gwamnatin Tarayya ce
ke da ruwa da tsaki a kansa, ba gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi ba.
A dalilin haka ne, gwamnatin shugaba Obasanjo, a shekarar 2000 ta fito da
tsarin tabbatar da tsaron ƙasa, wanda Bala da Ouédraogo (2018:3) suka
tabbatar na ɗaya daga cikin
manyan tsare-tsare da tanade-tanaden tsaron ƙasa da aka taɓa samarwa a Nijeriya. Duk da haka, sai a shekarar
2014 ce ofishin mashawarcin shugaban ƙasa kan harkokin tsaro ya sake inganta da ɗab’in kundin (Bala da Ouédraogo, 2018:3). A cikin
wannan kundi, an tsara cewa, babban buri da babbar manufar Nijeriya ita ce
tabbatar da ƙasa mai cike da zaman lafiya da lumana da ƙarfin arziki da
yalwar arziki ga kowa (Bala da Ouédraogo, 2018:3). Abin da
wannan bayani ke nuna mana shi ne cewa, tsaro babban lamari ne da wannan ƙasa ta bai wa
muhimmanci. Wannan ne ya sa aka ayyanan a cikin kundin ‘Babban muradin Nijeriya
shi ne tsaro da walwala da jin daɗin ‘yan ƙasa da ‘yanci da
kare mutuncin ƙasa da zaman lafiya da dimokaraɗiya da haɓakar arziki da kuma adalci ga kowa (Bala da Ouédraogo, 2018:3).
Kodayake, su ma waɗannan matakai biyu: gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi na
da hannu a tsaron, amma rawar da suke takawa ba ta wuce irin ta ‘yan kallo ba
waɗanda ka iya bayar
da gudunmuwa idan an buƙaci su bayar ko idan sun ga lamari na neman ƙwacewa! A bisa wannan
ne aka gwama wasu daga cikin gudunmawa da rawar da gwamnatin jihar Zamfara ta
bayar kasancewar jihar na fuskantar matsalolin tsaro domin ganin an shawo kan
matsalar a jihar ta Zamfara. Binciken da Garba (2020) ya gudanar ya tabbatar da
haka inda ma ya gano wasu wurare ko yankuna a ƙaramar hukumar
mulki ta Bukkuyum da hukumomi ba su da cikakken ƙarfin iko ko faɗa-a-ji. Domin fahimtar ma’anar yankunan da hukumomi
ba su da cikakken ƙarfin iko ko faɗa-a-ji, dubi aikin
da Rabasa da wasu (2007) suka gabatar.
An mayar da
hankali a kan tanade-tanaden doka musamman Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na
shekarar 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima domin tsamo muhallin tsaron ƙasa Nijeriya tare
da karkata akalar aikin domin zaƙulo dokokin da suka tabbatar da kafuwar hukomomin tsaro a Nijeriya. An
nuna irin matakan da gwamnatin Tarayya ke bi wajen tabbatar da tsaro da ma
yadda gwamnatin jihar Zamfara ke bayar da gudunmuwarta wajen shawo kan matsalar
tsaro a jihar.
2.0 Ma’anar Tsaro
Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero (2006:453) ya
bayar da ma’anar tsaro, amma a kaikaice. A cikin Ƙamusun, an umurci mai dubawa ya koma ya dubi
kalmar ‘tsara’ inda a shafi na 452 na Ƙamusun aka
bayar da ma’anar tsara (tsara, fi’ili)
ko a ce (aikatau) da ‘kare’ tare da
bayar da misali: Allah Ya tsare shi. Ita kuma kalmar ‘kare’ (karee, fi’ili) ko a ce aikatau), an bayar da ma’anarta a shafi
na 234 na ƙamusun a
matsayin (i) yin katanga don asirta wani abu, (ii) tsare wani abu, (iii) tokare
ko datse. Ita kuma Kalmar ‘kariya’ (kaariyaa,
suna, mace) na nufin yin amfani da wani abu don kange wani abu (2006:235). Daga
wannan bayani, ana iya fahimtar cewa, tsaro na nufin ɗaukar matakin kariya daga faruwar wani abu,
musamman maras kyau ko daɗi.
Tsaro (security) na nufin kariya daga duk
wata tsangwama da barazana ga walwalar al’umma tare da bai wa al’umma damar
gudanar da hulɗa da zamantakewa cikin lumana. Tsaron cikin
gida (internal security) na nufin kariya ko rashin ababen da ka iya yin zagon ƙasa ga fahimtar juna tsakanin mabambantan al’ummomi da ɗorewar
kyakkyawar zamantakewar ‘yan ƙasa. Haka kuma, yana nufin matakan da ƙasa ke ɗauka wajen kare muhimman hukumomi daga maƙiya da ‘yan kanzaginsu da ke cikin ƙasar domin ta tabbatar da buƙatunta na kiyaye ɗiyaucinta,
al’adunta, tattalin arzikinta da samar da ababen more rayuwa domin biyan buƙatun ‘yan-ƙasa (DSS, 2012).
Tsaro, a wannan babi, na magana ne a kan
tsaron ƙasa (national security). Shi tsaron ƙasa na nufin dukkan matakan kariya da ƙasa ke ɗauka domin kare ta da ‘yan-ƙasarta daga barazanar cikin gida da ta waje
tare da tabbatar da kyakkyawan yanayi da ‘yan-ƙasa za su gudanar da ingantacciyar hulɗa
da zamantakewa. Daga cikin hanyoyin tabbatar da wannan yanayi akwai: kiyaye rayukan
‘yan-ƙasa da dukiyoyinsu da ingantaccen tattalin
arziki da addininsu da mutuncinsu da kuma kiyaye iyakokin ƙasa (DSS, 2012).
2.1 Gwamnatin da ke da Haƙƙin Tsaro a Nijeriya
Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na shekarar
1999 da aka yi wa kwaskwarima (Constitution of the Federal Republic of Nigeria
(daga yanzu KTMN 1999) ya tanadi matakan gwamnati guda uku a Nijeriya. Ga su kanar haka: gwamnatin
tarayya da ta jihohi da kuma ta ƙananan
hukumomi. Daga cikin waɗannan matakan gwamnati, ta tarayya ce ke da alhakin samar
da tsaro. Wannan ya faru ne saboda rabon ayukkan da aka yi tsakanin gwamnatin
tarayya da sauran gwamnatoci. Wannan rabo ya haɗa
da keɓaɓɓun ayukkan majalisar ƙasa (Exclusive Legislative List) da kuma ayukkan
da gwamnatoci suka yi tarayya (Concurrent Legislative List). Rataye na biyu,
kashi na ɗaya na keɓaɓɓun
ayukan majalisar ƙasa
(second schedule of the legislative powers, part one of the exclusive
Legislative List) na KTMN 1999 ya lissafa tsaro a cikin jerin kaɓaɓɓun
ayukkan majalisar ƙasa wato
gwamnatin Tarayya. Bugu da ƙari, sassan
KTMN 1999 na 214 da na 217 sun dangata haƙƙin tsaro
da gwamnatin Tarayya. Sashe na 11 a ƙarƙashin kashi na biyu na babi na ɗaya
na KTMN 1999 ya ta’allaƙa alhakin
tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin jama’a a kan gwamnatin tarayya. Rataye
na uku kashi na ɗaya na KTMN 1999 ya ƙunshi batutuwa da suka ta’allaƙa tsaro a kan gwamnatin Tarayya. Misali,
batutuwan wannan rataye sun haɗa da: lambobi na 16 da na 25 da kuma na 27.
Duk da haka, sashe na ɗaya,
kashi na ɗaya lamba ta 4 (7) ya bai wa majalisar dokoki
ta jiha damar samar da dokoki da za su taimaka wajen samar zaman lafiya da
lumana da ingantaccen mulki a jihar ko wani yanki nata idan aka yi la’akari da:
(a) duk wani lamari da ba a lissafa shi a keɓaɓɓun
ayukkan majalisar ƙasa ba,
(b) duk wani lamari da aka lissafa a ayukkan da gwamnatoci suka yi tarayya da
kuma (c) duk wani lamari da KTMN 1999 ya bai wa majalisar dokokin jiha damar
yin doka a kan sa. Wannan bayani bai bai wa jihohi haƙƙin tsaro kai-tsaye ba, sai dai ya nuna cewa,
jihohi na da damar samar da dokokin da za su ƙara wanzar da zaman lafiya. Wannan ne ya bai
wa jihohi damar samar da
hukumomi da ke taimakawa wajen gudanar da tsaro ta fannonin zamantakewa, bisa karantarwar addini kamar hukumomin
Hisba da fannonin zirga-zirgar ababen hawa kamar KAROTA a Kano da
LASTMA a Legas da sauransu. Har
yanzu ba wata jiha a Nijeriya da ke da jami’an tsaro masu damar ɗaukar
makamai na kanta. Ko da hukumar tsaro ta AMETOKUN da jihohin Yarabawa suka
samar ba ta zauna daram ba. Tana-ƙasa-tana-dabo.
Wannan ya tabbatar da cewa, haƙƙin tsaro da
ya haɗa da kare rayuwa da dukiyar jama’a da kiyaye
doka da tsari a Nijeriya ya ta’allaƙa kacokan
a kan gwamnatin tarayya. Gwamnatin jiha ba ta da wata rawa a kan tsaro Nijeriya
bayan tallafa wa hukumomin tsaro da ke aiki a jihar.
2.2 Gurbin
Tsaro a cikin Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na Shekarar 1999
KTMN na 1999 na cike
da ayoyin doka da suka shafi kare haƙƙi da rayuwa da dukiyar
‘yan ƙasa. KTMN na 1999 ya ɗora wa gwamnati nauyin kula da rayuwar
al’umma. Sashe na 14 (2) (b) na KTMN na 1999 ya ce: ‘zaman lafiya da jin daɗin jama’a su ne ginshiƙai a aikace-aikacen gwamnati’. Wani muhimmin
abu shi ne, irin yadda taken
tarayya Nijeriya ya ƙunshi wasu
ginshiƙan tsaro. Sashe na 15 (1) ya ce: Taken
Nijeriya shi ne “haɗin
kai da aminci da lumana da ci gaba”. (The motto of
the Federal Republic of Nigeria shall be Unity and Faith, Peace and Progress). Bugu
da ƙari, sashe na 15 (2) na KTMN 1999 ya ce:
“Saboda haka, za a ja hankalin jama’a su ɗinke ƙarƙashin inuwa guda, sannan kuma za a haramta
duk wani nuna bambanci bisa dalilin mahaifa da
halitta da addini da muƙami da ƙabila da yare ko harshe”. Sashe na 15 (3) ya
ce: “Don a ɗinke
duk wata ɓaraka
tsakanin jama’a, hakkin ne a kan gwamnati ta: (a) samar da wadatattun hanyoyin
kaiwa da komowa, jigilar kayayyaki, da ayukkan kyautata rayuwar al’umma a faɗin Tarayyar Nijeriya; (b) bai wa kowane ɗan ƙasa
cikakken ikon zama a kowane ɓangare
na Nijeriya, ba lalle sai mahaifarsa ba”. Sashe na 16 na KTMN 1999 ya yi magana
a kan burin gwamnati na haɓaka
arziki, na 17 kuma ya yi tsokaci a kan burin gwamnati na kyautata rayuwa, na 18
kuma manufar ilmi, na 20 ko ya mayar da hankali a kan burin gwamnati na kare
muhalli na 21 kuma kiyaye al’adu na 23 ko karkata ya yi a kan ɗa’a ga ƙasa.
Daga cikin haƙƙoƙi na
wajibi da aka zayyana a babi na huɗu
na KTMN 1999 akwai sashe na 33 (1) da ya ƙunshi
cewa: “Kowane mutum yana da ‘yancin ya rayu, kuma babu
wanda za a raba shi da ransa da gangan, sai dai in an zartar masa da hukuncin
kisa a sakamakon gurfanar da shi da aka yi gaban kotu bisa wani laifi a Nijerya;
(2) ba za ɗauka an
raba mutum da ransa da gangan kamar yadda wannan Sashe ya hana ba, in ya mutu a
sakamakon amfani da ƙarfi
daidai gwargwado kuma ta hanyar da shari’a ta yarda, don: (a) a kare wani mutum
da ƙarfi a
sakamakon ta’adda, ko don a tsare dukiya; (b) a kama wani mai laifi ko yunƙurin hana wani tserewa yayin da shari’a ta
tsare shi; ko (c) daƙile zanga-zanga,
tarzoma ko tawaye”. Sashe na 34 (1) ya ce: “Kowane mutum yana da ‘yancin a mutunta
shi a matsayinsa na ɗan Adam,
saboda haka: (a) babu mutumin da za a gana masa azaba, ko a wulaƙanta shi ko a tozarta shi; (b) babu mutumin
da za a tsare cikin bauta ko aikin bauta; (c) babu mutumin da za a sa ya yi
aiki dole, ala-tilas”. Sashe na 35 na KTMN 1999 ya tabbatar da ‘yancin walwala
ga ‘yan ƙasa, na 36
ya mayar da hankali a kan ‘yancin mutum na a saurare shi a kuma yi masa adalci,
na 37 kuma haƙƙin kiyaye
sirrun ɗan ƙasa da iyalinsa, na 38 ko ya bai wa ɗan ƙasa ‘yancin tuani da ra’ayi da addini. Shi
kuma sashe na 42 ya karkata a kan haramci kan danniya, na 44 kuma ya yi kariya
daga karɓar dukiya
da ƙarfa-ƙarfa.
Babu shakka, KTMN 1999 ya cika ya tumbatsa da matakan
kariya domin tabbatar da tsaro ga ‘yan ƙasa domin ya ƙunshi kusan duk wani ɓangare da
ya shafi tsaron jama’a. Sai dai, inda gizon ke saƙa shi ne, ko ‘yan ƙasa suna ganin dukkan waɗannan
tanade-tanade da KTMN 1999 ya samar domin tabbatar da tsaron jama’a? Samar da amsar wannan tambaya ba ya daga cikin alƙiblar wannan babi. Yana da kyau a gabatar da
cikakken bincike a kan wannan batu domin a samu ƙwaƙƙwarar amsa da tabbaci a kan wancan tambayar.
2.3 Hukumomin
Gwamnati da suka Jiɓinci Tsaro a Nijeriya
Domin tabbatar da tsaron al’umma, gwamnatin tarayya
ta tanadi hukumomi iri-iri da suka jiɓinci
tsaron ‘yan ƙasa ciki
da waje. An tsara waɗannan
hukumomi tun daga waɗanda za su
hango ko shaƙo harkoki
ko abubuwan da za su iya tayar da fitina a ƙasa daga cikin ƙasar da ma wajenta tare da bayar da bayanan
yadda za a shawo kan su zuwa waɗanda za su kare wanzuwar matsalar da waɗanda za su
murƙushe
matsalar idan ta kai ga faruwa da waɗanda za su
yi kame da bincike da gurfanarwa gaban mashar’anta da kuma waɗanda za su
garƙame waɗanda aka
zartar wa hukunci. Haka kuma, akwai waɗanda ke
kula da shige da fice na al’umma da kayansu da na lafiyar kayan gona da dabbobi
da ma masu kula da ruwa da sarararin samaniya da na kare haɗurran titi
da na jirgin sama. Duk waɗannan
hukumomi an tanade su ne domin su tabbatar da tsaron rayuka da dukiya da lafiya
da mutuncin ‘yan ƙasa.
Waɗannan hukumomi sun haɗa hukumar
leƙen asirin
cikin gida SSS da leƙen asirin waje NIA da ta Soji da ‘Yansanda da mashar’anta da gidan yari. Akwai
hukumomin shige da fice Immigration
da na fasa-ƙwabri
Kwastan da Agricultural Quarantine da
Port Health da Sojin ruwa da sama da ta
kare haɗurran titi
ta FRSC da kuma ma’aikatan tsaro na
filayen jirgin sama (Aviation Security)
da na kashe gobara. Har wa yau, akwai hukumar hana sha da fataucin kwayoyi NDLEA da ta hana fataucin ɗan Adam NAPTIP da hana cin hanci da rashawa na ICPC da EFCC.
Idan ana maganar tsaron ƙasa, dukkan waɗannan
hukumomi na da rawar takawa kuma suna ɗamfare da
juna tare da taimakekeniya wa juna. Misali, baya ga samar da dabaru da bayanan
kare faruwar haɗurra,
hukumar FRSC na taimakawa manyan hukumin
tsaro da bayanan da suka shafi ababen hawan da aka aikata wasu laifuka da su. Wannan
na faruwa ne domin hukumar FRSC na da
rumbun bayanan dukkan ababen hawan da aka yi wa rijista da lamba tare da
mamallakarsu a faɗin
Nijeriya.
Dukkan waɗannan
hukumomi na da gindin zama a dokokin ƙasa. Misali, an kafa hukumomin tsaron ƙasa na sirri na SSS da NIA da kuma DIA masu kula harkokin tsaron sirri na
farin kaya da ƙasashen
waje da kuma harkokin soji, kamar yadda suka zo a jere, a babi na 278 na
dokokin tarayyar Nijeriya na shekarar 1986 (the National Security Agencies Act
of 1986 (CAP 278 LFN) bayan da aka rusa hukumar tsaro ta NSO. An yi wa wannan
doka kwaskwarima a babi 74 na
shekarar 2004 (National
Security Agencies Act, Cap N74. The Laws of the Federation of Nigeria, 2004). Za
a sami cikakken bayani a kan waɗannan hukummin tsaron sirri na Nijeriya a auakkan
Peters (1987) da Karim (2015). Sashe na 214 na KTMN 1999 ya bayar da damar kafa
hukumar ‘Yansandan Nijeriya; na 217 kuma ya sahale kafa rundunar mayaƙan
tarayyar Nijeriya da ta ƙunshi mayaƙan
ƙasa da na ruwa da kuma na sama.
Haka
kuma, gwamnati ta ƙara wa waɗannan hukumomi ƙarfi
da tallafi wajen ƙirƙirar
majalisar ƙoli ta harkokin tsaro iri-iri. Akwai: Majalisar
Kiyaye Sirrin Ƙasa da Majalisar Tsaro ta Ƙasa
da kuma Majalisar ‘Yansanda ta Ƙasa.
Rataye na uku kashi na ɗaya
G (16) na KTMN 1999 ya tabbatar da kafuwar majalisar tsaro ta ƙasa;
shi kuma na K (25) ya kafa majalisar kiyaye asirin ƙasa
a yayin da na L (27) ya kafa majalisar ‘Yansanda ta Nijeriya.
3.0 Tsarin Gudanarwar Wasu Hukumomin Tsaron Nijeriya
Mafi
yawan hukumomin tsaro na da mabambancin tsarin gudanarwa, sai dai inda suka yi tarayya da juna shi ne, dukkansu suna da babbar hedikwata a Abuja tare da hedikwatoci a
dukkan jihohin Nijeriya tare da birnin tarayya, Abuja. Misali, hukumar Soji na
da rundunoni da ake kira Divisions a
sassan Nijeriya da birged da garrison da bataliyoyi. Haka, a hukumar ‘Yansada na da ofisoshin shiya wato zones da ofisoshin yanki Area Commands ofisoshi a ƙananan
hukumomi Divisional Police Office da
ma ƙananan ofisoshi na ƙauyuka
wato Out Posts. Haka abin yake a hukumar kare al’umma ta Civil Defence. Ita
kuma hukumar leƙen asirin cikin gida SSS tana da irin nata tsarin:
tana da ofisoshin da aka sani a fili kamar ofisoshinta na ƙananan
hukumomi 774 a faɗin
Nijeriya, da kuma waɗanda ba a fili suke ba.
Ba
a banza aka tsara waɗannan
matakan tsarin gudanarwa na waɗannan hukumomi ba. Kowane mataki da irin aikinsa da kuma abin da ya sa
gaba. Akan tattara dukkan ayukkan a ɗauki matakin da ya kamata.
3.1. Wasu Hanyoyin Gudanar da Tsaro
Baya
ga bayanin da ya gabata a kan tsarin gudanarwar hukumomin tsaro, akwai wasu
hanyoyin da ake tabbatar da tsaron ƙasa.
Wasu daga cikin waɗannan
hanyoyi sun haɗa
da ma matakin soji ko ƙarfin gwamnati da kuma na lalama da na tallafa wa
al’umma. Ga su kamar haka:
3.1.1. Rundunar Haɗaka
Ɗaya daga cikin su ita ce hanyar samar da rundunar haɗaka wato joint
operation. Aikin Nte (2013) ya bayar da cikakken hasken a kan wannan hanya
ta samar da tsaron ƙasa. Shi kuma Jega
(2016) tarihin irin wannan rundunar haɗaka ya
bayar, musamman ta ɓangaren
soji.
Akan kafa irin wannan ruduna domin ta fuskanci wata matsalar tsaro kacokan
misali rundunar haɗaka
ta Lafiya Dole da ke kula da Boko Haram. Akan kafa irin wannan runduna domin ta
yi faɗa
da wasu matsaloli misa rundunar haɗaka ta Harbin Daji da ke ƙoƙarin
shawo kan matsalolin sace jama’a da satar shanu da sassanta rikicin manoma da
makiyaya.
Haka
kuma, kowace hukumar tsaro kan samar da irin wannan runduna ba tare da yin haɗaka da sauran hukumomi ba. Misali, hukumar ‘Yansanda
na da rundunar PuffAder, ta Soji na da rudunar Murmushin Kada, haka ma hukumar
SSS na da irin tata Special Incidence Response Team (SIRT).
A
yayin da rundunar haɗaka
ke gudanar da aikinta, su ma sauran jami’an tsaro da ba sa cikin rundunar na
can na gudanar da ayukkansu. Amfanin rundunar haɗaka shi ne tunkarar matsala ko matsaloli masu tasowa
domin a murƙushe su.
Bugu
da ƙari, Nijeriya kan yi haɗin guiwa da maƙwabtan
ƙasashe da ma ƙasashen
da ke nahiyar Afirka da ma duniya baki ɗaya domin shawo kan matsolin tsaron da ke addabar
Nijeriya da maƙwabtanta da nahiyar Afirka da ma duniya. Misali,
rundunar Soji mai kula da Tafkin Cadi da ta ƙunshi
sojoin Nijeriya da Niger da kuma Cadi; rundunar ‘Yansanda ta duniya International Police; Kwamitin hukumomin
leƙen asiri da tsaro na Afirka Committee of intelligence and Security Services in Africa. Waɗannan na taimakawa ƙwarai
wajen musayar bayanan sirri da tsaro da ake amfani da su wajen tabbatar da
tsaron ƙasa.
Karɓuwar da irin wannan hanya ce ta samu ta sa aka samar da
rundunonin haɗaka iri-iri a jihar Zamfara. A wani bincike da Suleiman (2019) ya
gudanar, ya lissafa irin waɗannan rundunoni da suka haɗa da: Harbin Kunama da Diran Mikiya da Puff Adder.
3.1.2 Rufe Iyakokin Ƙasa
Ɗaya daga cikin hanyoyin tsaro da ƙasa
ke ɗauka
domin kiyaye tsaronta ita ce ta rufe hanyoyi ko iyakokin shigowa ƙasar
daga wata ƙasar waje. Akan yi haka ta hanyar rufe iyaka ko
hanyar shigowa ƙasa ta ruwa ko ta sama ko ta hanyoyin mota wato
hanyar ƙasa. Mahukunta kan ɗauki irin wannan mataki idan sun samu bayanai da
suke ɗauke
da tabbaccin cewa wani abu ko wata barazanar tsaro da ake jin cewa za ta iya
shafuwar ƙasar ko ma ita ce ke haifar da matsalar. Za mu
tabbatar da haka, idan muka yi la’akari da yadda gwamnatin Nijeriya ta rufe iyakokinta
na ƙasa a watan Agusta na 2019, kuma har yanzu iyakokin na rufe. A cewar gwamnatin,
ta ɗauki
matakin ne domin hana shigowa da kayan abincin irn su shinkafa da sukari da mai
da ma makamai da ta ce ana safarar su zuwa Nijeriya wanda ke ƙara
ta’azzara tarzoma a ƙasa. Bugu da ƙari,
yayin da annobar cuta mai toshe hanyoyin numfashi wato kurona Coronavirus ta Ɓulla,
nan da nan gwamnatin Nijeriya ta rufe dukkan iyakokinta na sama inda aka hana
jiragen da suka taso daga wasu ƙasashe
sauka ko shigowa Nijeriya. Daga bisani ma, an dakatar da jiragen da ke
Jirga-jirga a cikin gida domin a kare yaɗuwar cutar.
3.1.3 Karɓar Makamai daga Hannu Mayaƙa
Ita ma wannan wata
hanya ce da gwamnatoci ke amfani da ita wajen magance matsalar tsaro. A irin
wannan hanya, akan umurci masu tayar da ƙayar
baya da su miƙa
wa gwamnati makaman da suke ɗauke
da su ba bisa ƙa’ida
ba. Nazarin da Ebiede da wasu (2020) suka yi ya nuna irin yadda karɓe
makamai daga hannun mayaƙa da masu tayar da
zaune tsaye a Nijeriya.
An yi amfani da wannan dabarar a jihar
Zamfara domin shawo kan matsalolin tsaro da take fuskanta. Jaridar Premium
Times (2018) ta ruwaito cewa, a ranar 15 ga watan Mayu na 2018, kwamitin zaman
lafiya da sulhu da kuma karɓar makamai
na jihar Zamfara da Malam Ibrahim Wakkala,
Mataimakin Gwamnan jiha, ke jagoranta, ya karɓo makamai
da suka adadin 5,870 daga hanun ɓata-gari, mahara. An miƙa makaman ga kwamitin da shugaban ƙasa ya kafa mai lura da karɓe ƙananan makaman da ke hannun mutane ba tare da
ƙa’ida ba,
inda aka lalata su.
Bugu da ƙari, Ƙaura (2019) ya
ruwaito cewa, a ranar 21 ga watan Satumba na 2019, maharani da suka ajiye
makamai a Zamfara sun miƙa wa
gwamnati tarin makamai masu yawa waɗanda suka haɗa da:
bindiga ƙirar AK-47
guda 39 da albarusai 10 da Labarbar guda 2 da bindiga mai sarrafa kanta GPMG
guda 1 da bindigar ƙirar LAR
guda 1 da kuma fistol 2. Har wa yau, a cikin rahoton, Kaura ya ƙara da cewa, Kwamishinan ‘Yansanda na jihar
Zamfara ya tabbatar da cewa, ’”yan-sa-kai ma sun miƙa makamai kimanin 200 ƙirar gida daban-daban”.
3.1.4 Samar da Kayan Aiki wa Jami’an Tsaro
Kamar
yadda aka nuna tun farko, haƙƙin tsaron ƙasa na a kan gwamnatin tarayya kacokam, gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi sai da su tallafa wa jami’an da ke
aiki a yankunansu. Bisa wannan, gwamnatin jihar Zamfara ta tallafa wa jami’an
tsaro da kuɗaɗe da motoci da sauran ababen buƙata domin gudanar da ayukkansu a jihar. Suleiman
(2019) ya ruwaito Mahmoud (2019) na cewa, ‘Gwamnatin Zamfara ta kashe maƙudan kuɗi kimanin Naira biliyan 17, domin tallafa wa jami’an tsaro su gudanar da aikinsu a jihar”. Tirƙashi! An daɗe ana ruwa, ƙasa na shanyewa. Ko ma dai mene ne, wannan ya nuna
irin yadda gwamnatin jihar ta kasha kuɗi wajen ganin ta samu zaman lafiya.
3.1.5 Kwamitocin Tsaro
A
matakan gwamnati daban-daban a Nijeriya da suka haɗa da: tarayya da jihohi da kuma ƙananan
hukumomi duk akwai wannan kwamiti na tsaro. Shugaban ƙasa
da manyan hafsoshin tsaro ne ke halartar kwamitin a matakin tarayya. Gwamnoni
da shugabannin
hukumomin tsaro ne ke halartar sa a matakin jiha, a yayin da shugabannin ƙananan
hukomomi da shagabannin hukumomin tsaro da sarakuna ne ke halartar kwamitin a
matakin ƙananan hukumomi. Akan yi wannan taro a ƙarshen
kowane wata ko kuma duk lokacin da wata buƙata
ko matsala ta bijiro. Akan tautana tare da yanke hukunci da ɗaukar matakin duk abin da ya jiɓinci tsaro a ƙaramar
hukuma. Haka abin yake a matakan jiha da tarayya.
3.1.6 Yaƙi da Safarar Kuɗi da Makamai da Rashawa da kuma Ta’addanci
Gwamnati tana ɗaukar matakai
ta fuskoki da dama domin yin kan-da-garki a kan wasu matsalolin tsaro da suka
haɗa da:
safarar kuɗi da
makamai da kuma rashawa. Safarar kuɗin haram na taka muhimmiyar rawa wajen
ta’azzara ta’addanci da sauran matsalolin tsaro. Garba (2013) ya ruwaito yadda
aka sake yi wa dokar hana safarar kuɗi ta
shekarar 2003 aka samar da dokar hana safarar kuɗI ta 2004 The Money Laundering (Prohibition) Act of
2003 was enacted, and re-enacted as the Money Laundering (Prohibition) Act of
2004. Daga bisani, an sake yi wa wannan doka kwaskwarima ta koma dokar hana
safarar kuɗi ta 2011 Money Laundering (Prohibition) ML(P) Act 0f 2004 ( Now 2011).
Abin
da wannan bayani ke nunawa shi ne, samar da dokoki na ɗaya daga cikin hanyaoyin da ake shawo kan matsalar tsaro a
duk lokacin da aka fahimci rashin doka ko rashin ingantattun dokoki na bayar da
dama ga wanzuwar wasu hanyoyi da ka iya haifar da matsalar tsaron ƙasa. Wannan manufa ta gwamnati ta
samu biyan buƙata a shekarar 2018, inda aka samar da hukumar kula da
harkokin kuɗi ta ƙasa Nigerian Financial Intelligence Unit (NFIU) wadda ta
fara aiki a shekar 2019. Kwalliyar wannan hukuma ta fara biyan kuɗin sabulu
domin tun yanzu ta kawo dabaibayi a kan yadda akan yi tu’ammali da kuɗaɗen
gwamnati.
Wannan ne ya sa a shekarar 2004, aka samar da
wata ayar doka, a karo na farko, da ta shafi ta’addanci a sashe na 15 na
dokokin hukumar yaƙi da rashawa da sauran laifukka ta EFCC. A shekarar 2011 kuma aka sake ƙarfafa dokar yaƙi da ta’addanci da kuma samar da kuɗin gudanar
da ta’addancin terrorism and terrorist
financing was enacted in 2011 as the Terrorism (Prevention) Act, 2011 (i.e.
TPA).
3.1.7 Yaƙi da Cin hanci da Rashawa
Yunƙuri da kyakkyawar niyyar da gwamnatin shugaba Buhari take nunawa
wajen yaƙi da
rashawa na daga cikin matakan tabbatar da tsaronNijeriya. Garba (2018) ya
lissafo wasu daga cikin hanyoyi da aka fito da su domin yaƙi da rashawa da gyaran hali da suka haɗa da:
shirin gyaran halin ‘yan ƙasa na change
begins with me da ƙulla
yarjejeniya da ƙasashen
duniya domin daƙile satar
kuɗin ƙasa da ajiye su a ƙasashen waje tare da dawowa da waɗanda aka
rigaya aka ɓoye a ƙasashen da tsarin kwarmato wato whistle blower policy da na tabbatar da
tilon asusu treasury single account da kuma tsarin
tattara ma’aikatan gwamnati wuri ɗaya wato IPPIS.
3.1.8 Samar da Abinci da Cimaka
Muhimmancin
abinci da dangogin cimaka a sha’anin tsaron ƙasa
ya fi gaban a nanata. Abinci wani muhimmin ɓangare ne a fannin tsaro ta yadda wasu manazarta da
masana suka sa shi wani kaso daga cikin kashe-kashen tsaro, wato food security. Wannan wani ginshiƙi
ne mai zaman kansa a fannin tsaro Nwokeabia (2003) da Metu et
al (2016) da Akinyetun (2018).
Shi kuma Akinyele (2009) nuna wajabcin samar da abinci
ya yi a ƙasa
musamman ta fuskar abincin mai gina jiki. Wannan ne ya sa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari
ta mayar da hakalinta wajen inganta noma domin ƙasa
ta zauna da ƙafafunta ta fannin abinci. Gwamnatin tarayya ta
samar da hanyoyin ƙarfafa wa manoma guiwa ta hanyar samar da iri da
taki da kayan aiki da bashin kuɗi domin inganta noma, musamman noman shinkafa.
Wannan
tsari ya haifar wa Nijeriya ɗa-mai-ido, idan aka yi la’akari da yadda cutar
kurona ta tunkaro ƙasashen duniya wadda ta tilasta rufe iyakokin ƙasashen
duniya tare
da dakatar da safara. Sarrafa shinkafar gida da Nijeriya ke yi ne ya agaji ƙasar
nan daga faɗawa
cikin rikicin ko matsanancin ƙarancin
abinci. Da ba don tsarin samar da abinci cikin gida, musamman shinkafa, ya fara
kankama ba, da Nijeriya ta gane Barno gabas take! Wanda bai fahimci yadda abin
yake ba, zai ce to ai yanzu ma hakan take, sai dai waɗanda suka san kwanan zancen, sun sani. Aikin da Zakaree da wasu (2018) suka yi ya tabbatar da
gudunmawar da tsarin noman shinkafa ya bayar a jihar Kebbi. Shi ma Hamagam (2020)
ya bayar da tabbacin yadda tsarin bayar da bashi ga manoma na anchor barrower
ya bunƙasa noman
shinkafa a jihar Kebbi.
3.1.9 Ilmantarwa
Wata
hanya da gwamnati ke tabbatar da tsaro ita ce ta ilmantar da al’umma. Hukumomin
tsaron Nijeriya daban-daban na bai wa irin wannan tsari muhimmanci. Akan yi wa
‘yan ƙasa bayani a kana bin da ya shafi tsaro ta fuskoki
daban-daban: a matakin ƙungiyoyi da matakin ƙauyuka
da garuruwa; a fadojin hakimai/uwayen ƙasa
da dagattai da sauran masu riƙe
da mulki. Bugu da ƙari, hukumomin wayar da kan al’umma irin su NOA da
kafafen sadarwa duk suna taka irin wannan rawa.
3.1.10 Sulhu
Wannan
na ɗaya
daga cikin hanyoyin da ake samar da tsaro, musamman bayan matsala ta faru
tsakanin ɓangarori
biyu ko fiye (2009).
Wannan daɗaɗɗiyar hanya ce da ake tsagaita matsala ko kawo ƙarshenta
gaba ɗaya.
Manya da ƙananan ƙasashen
duniya na amfani da wannan tsari. A halin yanzu, ƙasar
Amurka na can na tattaunawa a kan teburin sulhu da Taliban domin a kawo ƙarshen
yaƙin Afganistan na kusan tsawon shekara ashirin.
Gwamnatin
jihar Zamfara ma ta yi amfani da wannan salo inda aka haɗa tarurruka tsanin shugabannin al’ummomin Hausawa da
Fulani domin a samu bakin zaren matsalar da ta haifar da gagarumar matsalar
tsaro a faɗin
jihar. Duk da dai matsalar ba ta kau gaba ɗaya ba, amma an sami sauƙin
ta. Jami’an gwamnati da na hukumomin tsaro sun
ziyarci dukkan fadojin masarautun jiyar domin tabbatar da wannan sulhu.
3.1.11 Afuwa
Wannan
ma na ɗaya
daga cikin matakan da ake ɗauka
domin kawo ƙarshen matsalar tsaro a dukkan matakan gwamnati a faɗin duniya. Ayukkan Vanessa (2013) da Ajibola (2015) da
Tobor da Odubo (2017) sun tabbatar da gudunmawar yi wa ‘yan tayar da tarzoma
afuwa wajen samar da zaman lafiya a Nijeriya. Bisa wannan ne, gwamnatin jihar
Zamfara ta yi afuwa ga Buharin Daji da mabiyansa a lokacin mulkin Alhaji
Abdul’aziz Yari. Shi ma sabon gwamnan jiha, Muhammadu Bello Matawalle ya yi irin wannan afuwa ga mahara. Yana da kyau a gane
cewa, wannan babi ba ya da
hurumin bayanin ko wannan tsari na afuwa ya yi tasiri ko a’a a matsalar tsaron
Zamfara ba.
3.1.12 Samar da Aikin Yi
Wani
mataki da gwamnati kan ɗauka
wajen samar da tsaro shi ne samar wa ‘yan ƙasa
aikin yi. Idan an ce aikin yi, mafi yawa za su tunanin aikin gwamnati na ofis.
A nan, ana magana ne a kan yadda za a samar da hanyoyi da ‘yan ƙasa,
waɗanda
suka yi karatu da ma waɗanda
ba su yi ba, za su samu hanyar gudanar da rayuwa ba tare da yin zaman banza ba.
Wannan ne ya sa gwamnai ta fito da hukumar samar da aikin yi ta ƙasa
National Directorate of Employment da
ma wasu irin ta da suka biyo bayanta. Wannan gwamnati ta Muhammadu Buhari ma ba
ta ƙasa a guiwa ba wajen fito da hanyoyin samar da aikin
yi ga matasa. Misali, akwai: N-Power inda aka ɗauki matasa a sassa daban-daban na ƙasa
ake biyan kowannen su albashin Naira dubu talatin duk wata (N30,000).
3.1.13 Tallafi ga Masu Rauni
Domin
kare masu fama da matsanancin talauci a cikin al’umma daga faɗawa cikin ayukkan laifi da za su ƙara
taimakawa wajen ta’azzara matsalar tsaro, gwamnati ta fito da tsarin tallafa wa
masu ƙarami ƙarfi
da Naira dubu biyar N5000 duk ƙarshen
wata social security. Gwamnatin
tarayya da Shugaba Buhari ke jagoranta ce ke gudanar da wannan tsari, amma ya
shafi dukkan jihohi, ciki har da jihar Zamfara. Ana kiran wannan tsari a
Turance da Conditional Cash Transfer (CCC). Haka kuma, akwai tsari na trader money
da har wa yau,
gwamnatin tarayya ke gudanar da shi. A wannan tsarin da ake bai wa ƙananan
‘yan kasuwa, mafi yawa mata, tallafin Naira dubu goma (N10,000) domin su ƙara
jari. A wani bincike da Roseline da Charles (2019:20) suka yi, sun tabbatar da
wannan tsarin tallafi ga jama’a da gwamnatin Buhar ta samar a shekarar 2016 domin rage raɗaɗin talauci a tsakanin al’ umma.
3.1.14 Wasannin Gargajiya
Wasannin
gargajiya na daga cikin hanyoyin da ake amfani da su wajen magance matsalolin
tsaro. Wasu lokuta akan sanya gasa a tsakanin mabambantan al’ummu da ba sa
ga-maciji da juna domin ƙarfafa zaman lafiya. A jihar Zamfara, a ranar 14 ga watan Agusta na 2019, gwamnan jihar, Muhammadu Bello Matawalle, ya shirya
wasar sharu/shaɗi
wa Fulani a bikin sallah ƙarama ta shekarar 2019, a Gusau, babban birnin jihar
(Umar 2019). Wannan ya bai wa Fulanin damar sakin jiki su zagaya cikin garuruwa
da kasuwanni a faɗin
jihar, inda kafin hakan, ba su iya zagayawa.
4.0 Kammalawa
Wannan babi ya yi ƙoƙarin
fito da irin matakan tsaro da gwamnati ke ɗauka wajen tabbatar da tsaro a ƙasa
tare da shawo kan matsala ko matsalolin tsaro da suke addabar ƙasa
ko wani yankinta. Kodayake, matakan da aka yi bayanin su a nan na daga cikin
yanki ko kashin matakan da gwamnati ke ɗauka ko amfani da su wajen tsaron ƙasa.
Wato, akwai wasu matakan da ba za a iya faɗin su ƙarara
a nan ba. Domin kuwa, a harkokin tsaro, ba komai ake bayyanawa duniya ba! Dalilin
haka kuwa, shi ne, baya ga ‘yan tayar da zaune tsaye, mahara da ‘yan-barandan
da ke yi wa wasu ƙasashen waje aiki domin kitsa kutunguila a cikin ƙasa,
akwai magauta na waje da ke neman hanyoyin da za su yi amfani da su domin tayar
da zaune tsaye. Kowace ƙasa daga cikin ƙasashen
duniya na neman lagon ‘yar uwarta domin ta samu wata dama a kanta.
A
cikin babin, an yi nutso, an lalabo tare da tabbatar da gwamnatin da ke da haƙƙin
samar da tabbatar da tsaro a Nijeriya da gurbin tsaro a cikin KTMN 1999 da hukumomin
gwamnati da suka jiɓinci tsaro
a Nijeriya da kuma wasu hanyoyin gudanar da harkokin tsaro a Nijeriya. Bugu da ƙari, an gwama matsalolin tsaro da jihar
Zamfara da irin matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka ko
take ɗauka domin
shawo kan matsalar.
5.0 Manazarta
1. Ajibola, I. O. (2015). Nigeria’s Amnesty
Program: The Role of Empowerment in Achieving Peace and Development in
Post-Conflict Niger Delta’, SAGE OpenJuly-September
2015: 1 –11First Published July 6, 2015 Research Article https://doi.org/10.1177/2158244015589996
2. Akinyele, I. O.
(2009). ‘Ensuring
food and nutrition security in rural Nigeria: An assessment of the challenges, information needs, and analytical
capacity’, https://www.ifpri.org/publication/ensuring-food-and-nutrition-security-rural-nigeria-0
3. Akinyetun, Tope. (2018). ‘Towards Achieving
Food Security in Nigeria: The Economic Strains and Strategies for Way Forward’,
Global Journal of Economics and Finance Vol.
2, No.1; January, 2018 www.gjefnet.com
4. Bala, S. and Ouédraogo, E. (2018). ‘National Security Strategy Development: Nigeria Case Study’, Working Paper (Preliminary Draft)
Africa Centre, July 2018 https://africacenter.org/wp-content/uploads/2019/04/2019-04-NSSD-Case-Study-Nigeria-EN.pdf
5. Department
of State Services (2012). Manual. Abuja: National Headquarters State Services
6. Ebiede,
T.M., Langer, A. and Tosun, J., 2020. Disarmament, Demobilisation, and
Reintegration: Analysing the Outcomes of Nigeria’s Post-Amnesty Programme. Stability:
International Journal of Security and Development, 9(1), p.6. DOI: http://doi.org/10.5334/sta.752
7. Garba, S. A. (2013). ‘Money Laundering and Terrorist Financing:
Role of the State Security Service’, being a paper presented at the State
Director of Security’s (SDS) Conference, Kano State Command, for the month of
May, 2013 held at Kano State Command on 20th
May, 2013
8.
Garba, S. A. (2018). ‘Challenges/Impediments
to Anti-Corruoption War in Nigeria: The Way Forward’, being a paper presented at the Monthly Staff
Capacity Building Lecture and State Director of Security’s (SDS) Conference for
the month of March, 2018 held at Kano State Command on 20th March,
2018
9. Garba, S. A. (2020). ‘Insecurity
in Bukkuyum LGA of Zamfara State: The Case of Ungoverned Spaces’, a paper
presented at the 4th National Conference organized by Faculty of
Arts and Islamic Studies, Usmanu Danfodiyo University Sokoto themed ‘Zamfara
Kingdom: Social and Political Transformation from 14th Century to
Date’, held at the Usmanu Danfodiyo University Auditorium from 25th to
28th February, 2020
10. Hamagam, A. M. (2020). ‘How Anchor Borrower raised
Kebbi rice production’, Daily Trust Newpaper published on 23 February, 2020 https://www.dailytrust.com.ng/how-anchor-borrower-raised-kebbi-rice-production.html
11. (2009). ‘Conflict, Conflict Resolution
and Peace-Building: The Role of Religion in Mozambique, Nigeria and Cambodia’,
Commonwealth
& Comparative Politics, 47:1, 52-75, DOI: 10.1080/14662040802659033
12. Jega, M. (2016). ‘From Scorpion Sting to Snake Bite’, Monday Column,
Daily Trust Newspaper Published n Jul 18 2016 5:00AM http://www.dailytrust.com.ng/news/monday-column/from-scorpion-sting-to-snake-bite/155739.html
13. Karim, A.
A. (2015). ‘Major Intelligence Organization in Nigeria and Beyond’, in Ajayi
Kunle (ed.) Readings in Intelligence and
Security Studies. Ado-Ekiti: Intelligence and Security Studies Programme of
Department of Political Science and International Studies.
14. Kaura, A. (2019). ‘Zamfara Bandits surrender
weapons’, September 21, 2019, https://www.radionigeria.gov.ng/2019/09/21/zamfara-bandits-surrender-weapons/
15. Kundin
Tsarin Mulkin Nijeriya 1999
16.
Metu, A. G. et al
(2016). ‘Achieving Sustainable Food Security in Nigeria: Challenges and Way
Forward’, 3rd International Conference on African Development Issues (CU-ICADI
2016) ISSN: 2449-075X, http://eprints.covenantuniversity.edu.ng/6653/1/icadi16pp182-187.pdf
17.
Nte, N. D. (2013). ‘An Analysis of Intelligence Support to Security
Operations in Nigeria: A Review of Some Joint Task Force Operations’, Peace and Security
Review Vol.5, No.9, First Quarter, 2013,
pp.1-23
18. Nwokeabia, O. D. (2003). ‘Forestry
And Food Security In Nigeria’, paper presented at the xII World Forestry
Congress, 2003, Quebec City, Canada http://www.fao.org/3/XII/0038-A1.htm
19. Peters, J.
(1987). ‘Nigeria's Intelligence System: An Analysis’ Africa Spectrum, Vol. 22, No. 2 (1987), pp. 181-191. Sage
Publications, Ltd. https://www.jstor.org/stable/40174640 Accessed: 30-03-2020 21:08 UTC
20. Premium
Times (2018). ‘5,870 illegal arms destroyed in Zamfara’, May 15, 2018, https://www.premiumtimesng.com/regional/nwest/268481-5870-illegal-arms-destroyed-in-zamfara.html
21. Rabasa, Angel et al (2007). ‘Ungoverned Territories:
Understanding and Reducing Terrorism Risks’, USA: Arlington. The RAND
Corporation Prepared for the United States Air Force Library of Congress Cataloging-in-Publication Data available
from: http://www.rand.org/pubs/ monographs/ 2007/ RAND_MG561.pdf; Internet;
accessed 13/1/2020
22.
Roseline, O. C. da Charles, O. N. (2019).
‘National Social Investment Programme (NSIP) and Sustainable Poverty Reduction
in Nigeria: Challenges and Prospects’, IOSR
Journal Of Humanities And Social Science (IOSR-JHSS) Volume 24, Issue 10,
Series. 11 (October. 2019) 20-31 e-ISSN: 2279-0837, p-ISSN: 2279-0845. www.iosrjournals.org
23. Suleiman, Samaila. (2019). ‘Rural Banditry in Zamfara
State, Northwest Nigeria’, Social
Sciences Research Council June 13, 2019
https://kujenga-amani.ssrc.org/2019/06/13/rural-banditry-in-zamfara-state-northwest-nigeria/
24. Tobor, J. O. and Odubo, F. (2017). ‘Amnesty Program as a Peacebuilding
Initiative in Niger Delta, Nigeria’, Arts
Social Sci J 8: 272. doi:
10.4172/2151-6200.100027
25. Umar, Shehu. (2019).
‘Zamfara: Matawalle, deputy, hundreds attend Fulani sharo festival’, Jaridar
Daily Trust ta ranar 14 ga watan Agusta na 2019 https://www.dailytrust.com.ng/zamfara-matawalle-deputy-hundreds-attend-fulani-sharo-festival.html
26. Vanessa, U. (2013). ’Nigeria's Amnesty Programme as a
Peacebuilding Infrastructure: A Silver Bullet?, Journal of Peacebuilding & Development, 8:1, 30-44, DOI:10.1080/15423166.2013.789255
27.
Zakaree, S. S. et al (2018). ‘Anchor Borrower Programme on Agricultural
Commodity Price and Employment Generation in Kebbi State, Nigeria’, European Scientific Journal May 2018 edition
Vol.14, No.13 ISSN: 1857 – 7881
(Print) e - ISSN 1857- 7431
DOI: https://dx.doi.org/10.36349/tjllc.2022.v01i01.012
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.